← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 59

Sashe 53

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zamu ji ya Latifa za a Kare oho.😅😅😅😂😂😂🤣 Nafi yiwa Niima dariya wallah, magana ga yawu cike da baki hhhhh....
Up...up...Ni

AsmaBaffa.
[7/22, 1:14 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO

76-80

Official

By

AsmaBaffa

Farhan Yana Office hankali kwance Yana waya da Fatimansa wacce zai Aura sai zuba love suke yarinya Yar mutunci ga tarbiya ga wayewa gata itama kyakyawa da ita.
Latifa taci kwalliya ta Sha kyau itama, Office din Farhan tayi knocking,kafin ya Bata damar Shiga sai da ta gyara tare da kallon Fuskarta a mudubi, come in yace sannan yaci gaba da wayarsa ta soyayya, Yana ganin Latifa ce ya canja fuska Amma sai ya danne yace I will call u back later ya datse Kiran, sannan yace zauna, Latifa sai da ta wani karairaye sannan ta zauna tana fari da Ido tana juya kafada.

Farhan ya girgiza Kai wani haushi ma ta bashi yace fadi meke tafe dake Ina sauri akwai aiki a gaba na,Latifa tayi fari sannan tayi wani murmushin Jan hankali sannan tace zuwa nayi na maka Godiya Akan abubuwan da kayi mana, yace no Need ai ba damuwa,Murmushi tayi tace ok tare da Mikewa tsaye tana juyawa Dan ya gani,sai taci gaba da magana tana juya idanu baka da wani aiki da zanyi maka sabo da abinda kayi mana Ina so nima na saka maka da alkhairi kaima,Farhan ya zaro Ido yace Dan Allah nayi bana bukatar a saka min.

Latifa ta kalli Office din tana kashe Masa Ido tare da cewa Naga kamar yayi dirty ai da ko shara da mopping nayi maka,yace no na gode jeki kawai, Dan Allah Ina so na fada maka magana Amma tamin nauyin fada, biro ta dauka da paper a saman table dinsa kana ta Rubuta Masa I love u a jikin paper sannan ta Mika masa,ya karanta takaici ya kamashi ba aji ba komai direct, a fili yace Ina da matar da zan aura kiyi hakuri, Latifa takaici ya kamata dama Bata fiye kunya ba sai ta hayayyako Masa da masifa Kar ka Soni din sai me Dan nace Ina sonka ko Kai kadai ne Namiji mtswwww taja tsaki tare da bude Kofa ta fice a fusace.
Tsaki yaja ya Danna Kiran Fatimansa suka dora daga inda suka tsaya, Momee ta bawa labarin abinda ya faru tsakaninta da Farhan harda Hawaye,Momee tace Kinga kin nuna Masa Baki da tarbiya bazai taba sonki ba,Haka na koya Miki kiyi? Nan Momee tayi ta masifa.

Niima dai dai Lokacin data San Ahleef Yana dawowa daga Office lokacin taci kwalliya yau dai tayi kyau ba laifi,Compound ta fito tana jikin wata bishiya dake facing din inda ake parking cars yanda Dole Ahleef ya ganta, Bata Dade da Zama ba sai ga Motocin Ahleef sun shararo cikin gidan,ya fito da sauri sabo da Burinsa yayi sauri yaga Shukuransa,Bai kula ma akwai wata Niima a gefe ba tuni hankalinsa yayi wajen Matarsa,jikin kofar Kuma Shukura tana Nan ta kyafe cikin kwalliya da Shiga ta gaske Wanda kowa ya kalleta sai ya Kara,Niima sai gani tayi Shukura ta sakalkale mijinta cike da Shauki tayi ciki dashi tare da banko kofa.

Nan suka barta tayi tagumi tana sake saken duniya a ranta tana neman Mafita yanzu ta fara tunanin Ahleef ya Mata Nisa yafi karfinta, sai dai Shukura abin ba a cewa komai sai du'a'i kawai.
Hankalinta tashe tayi cikin gida bangaren Umma kwalla cike a idonta,Zazzabin son Ahleef ya lullubeta sai yanzu Allah ya jarabceta da matukar kaunar Ahleef,ji take kamar ranta zai fita sabo da sonsa, idan ta kalli cikin Mubaraq dake jikinta sai kuka ya Kara kwace Mata tare da Nadama, Umma ita kanta tausayin Niima ya fara kamata Kuma ta gane Ahleef take so.
Niima ta iske tayi tagumi Hawaye na zararo Mata masu dauke da sinadarin dafin son Ahleef a cikinsu🤣
Lallashi tare da Nasiha Umma ta Shiga yiwa Niima,Kuma Niima taji sanyi a ranta, na gode Umma Dan Allah Umma kisa Baki Ahleef ya aureni Nan gaba,Umma tayi Shuru sannan tace zan gwada rokarsa Amma idan yaki bazan Masa Dole ba,matar mutum kabarinsa Dole idan mijinki ne sai ya aureki,idan ba shi bane idan duniya zata taru a kansa wlh bazai aureki ba,kiyi Addua Allah Baki na gari me kaunarki.
Niima tace na gode Umma tana share hawayenta.

Da dare Ahleef yazo wurin Baba suna Hira Umma ta shigo itama ta zauna,sai da suka nutsu sannan ta kawo bukatarta na Ahleef ya taimaka ya auri Niima Nan gaba,Baba zaraf yace Saudatu ki fita daga idona,ke ko kunya bakya ji Zaki sa ayiwa Shukuran taki kishiya da kanki,Allah ne ya halatta,Amma Ana so mutum ya nemi yarinya ta gari ba irin Niima ba,mene Bata yiwa Ahleef ba,sai yanzu da bukatar ta ce sannan zata damu Mutane,lokacin da shi ya Shiga wani Hali a kanta ta tausaya Masa?to wlh ko ba Raina ban yarda ya aureta ba.

Umma a sanyaye tace Mene abin fada anan tunda kace Haka ai shike Nan Nima ba cewa nayi Dole ba,idan yaga zai iya nace,to bazai Aureta ba cewar Baba Kuma kika takura wlh da kaina zan koreta daga Nan gidan.

Ahleef ba karamin dadin Maganar Baba yaji ba,dama shi ko me za ayi bashi da Burin karawa Shukurnsa kishiya bare ya auri wata Niima.
Shukura ce ta shugo part din Umma kenan ta Dan tsinci Zancen kadan Amma Bata Gama Jin me ainihin Zancen ke nufi ba,share zancen tayi kawai tare da gaida su Umma ta nemi wuri ta zauna itama sannan ta ajiyewa Umma wani flask me kyau, me Kuma kika dafa na kwadayi yau? Umma ta furta, Murmushi Shukura tayi tare da cewa Baba Naga Yana son danwake shine nayi Masa,da Tsantsan Jin dadi Baba yace oh Yata na gode Allah ya muku albarka, Umma tace Ameen, kwalliyar da Shukura ta sheka itace ta tafi da hankalin Ahleef sai binta yake da kallo ya kasa dauke idonsa a kanta, Shukura tana kallonsa ta gefen Ido Kuma taji dadi tasan kwalliyarta tayi,Mikewa tayi ta wuce part dinsu Kar Ahleef ya kunyatata sabo da taga sai wani magana yake mata da idonsa daya tana tafiya yayiwa Su Umma sallama yabi bayan Shukuransa.

A kitchen ya isketa tana dube dube sai ji tayi ya rungumeta ta baya tare da Rada Mata sallama a kunne,Jikin Shukura har ya harba wani bukatar Mijin nata ya taso mata tana a jikinsa ta juyo suna Facing juna,hannayenta biyu tasa ta tallafi fuskarsa tana kallonsa a hankali in a sexy way tace kana da kyau Hero I love u,kissing din lips dinsa ta farayi a hankali,shima Yana yi har suka koma da zafi zafi kamar zasu cinye kansu Yana cewa I love u to the bone Bae.

Daukanta yayi cak suna kissing juna ta ko Ina haka suka fito zuwa Bedroom, tun kafin su Karasa sun cire kayan jikinsu, Nan suka Shiga baje harkoki Baji ba gani abin nasu sai Wanda ya gani, Ahleef ya susuce sai kalamai yake ratartakowa Shukura Mata itama Haka daga Nan ya Shiga zuba Mata adduoi Wanda bai ma San me yake cewa ba, sai Bayan sun nutsu tare da tsarkake jikinsu Yana zaune ya mike kafafu saman bed bayansa ya jingina da fuskar bed din.

Sanye take cikin wani mini skert da Yar Riga ko cibi Bata Kai ba me siririn hannu tayi kwalliya sosai tayi kyau,tsakiyar kafafunsa ta zauna itama Yana Danna system ta lafe a jikinsa,hannunta dauke da glass cup na fresh milk tana Sha tana bashi shima Yana Sha Yana aikinsa.
Ba tare da ya kalleta ba yace Honey gist me,Murmushin da tasan Yana tafiya da imanin sa ta saki, cike da Shagwaba tace Hero makaranta fa University ga result dinmu ya fito yaushe zaka sani, Zancen ya share, kukan Shagwaba ta fara masa, mene Kuma? ya tambaya, ba Kaine ba Ina ma maganar schl sai kana shareni baka son zancen ma, a hankali ya lankwaso da kansa tare da daura Mata kiss a lips dinta itama ta Kara turo Masa Dan lips nata tare da sakalo hannunta daya ta wuyansa ya Shiga kissing nata sai da ya gaji sannan yace ina sane da schl Dinki Baby,bana son kina barin gida kullum bazan jure ba Amma Dole inshallah Zaki je schl ki jirani.

Murna ta kama Shukura bata San sanda ta rungumeshi ba tana kissing dinsa ta ko ina zata yi University itama a daina Mata iyayi, dariya Ahleef yake sabo da yanda shukura take murna kamar zai sata Aljanna.

Niima ganin ba fuska wajen Ahleef kawai sai ta tattara nata ta dawo gida wurin Momee, ta waya Momee ta Kira Farhan da Ahleef suzo tana son ganinsa cikin gaggawa tare da Farhan, Babu komai a ransu suka yi parking compound na Momee kana suka Shiga bakinsu dauke da Sallama,Latifa ta labe jikin kofa tana leken Farhan,Niima Kuma Ana can ana cancada kwalliya.
Momee da farin ciki ta tarbesu tana murna suka gaisheta cike da ladabi,Ahleef yace Momee gamu da fatan dai lfy, Baki washe tace wlh lfy Lau,wata alfarma nake nema a wajenku,nasan nafi karfin komai a wajenku musamman Kai Ahleef Umarni ma idan na baka nasa zaka yarda, Ahleef yace Haka ne Momee ai har yau uwarmu ce har abada ma, Baki Momee ta Kara washewa sannan tace Ina so Ahleef Dan Allah ka rufa Mana asiri ka auri Niima idan ta haihu,Farhan Kuma ka rufa min asiri ka auri Latifa,kafin Momee ta Gama zancenta Gumi ya jike Ahleef duk da ac dake Palon,Farhan kuwa ko a gefen rigarsa yace Momee kiyi hakuri wlh Ina da wacce nake so na rigada na fitar da matar aure saura 3mnths biki ma,Allah ya Bata miji na gari Wanda ya fini,Kuma na gode sosai da Babban tayi da kika min,Dukul Momee taji a ranta,a fili tace ba damuwa Farhan na gode Allah bada zaman lfy yace Ameen.
Latifa Dake labe hawayen kauna ya kwararo mata tasan ta rasa Farhan shike Nan.
Chapter 53 · 0% Book details