← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 59

Sashe 17

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shukura tana tsaye ya kalleta fuskarsa dauke da Nishadi marar misaltuwa,Shi yasan bazai iya yiwa jinin Momee komai ba amma ga Shukura tana masa abinda ya dace ba tare da ta San komai kansa ba, kuma tana birgeshi wajen daraja dan Adam koya yake kuwa.
Kanta ta dago a hankali suka hada ido ta dauke kanta kana ta kara kallonsa suka hada ido again da sauri ta sadda kanta kasa ta kara dagowa nan ma idonsu ya sarke dana juna murmushi suka sakarwa juna sannan ya riko hannunta karo na farko, tun daga Palon yace yau fadi duk abinda kike so na baki shi,Shuru tayi ta nutsu sannan tace indai na fada zaka min ? Yace ae tace to daukeni ka shillani sama ka cafe dama na dade ina so na samu me karfin da zai min,Baffana ne ke yi min tun ina yarinya har na girma yanzu kuma ya rasu na dade ban samu anyi min ba...ba zato taji Ahleef yayi sama da ita kamar tsinke yayi mata yanda ake shilla yara ana cafewa kadan sannan ya direta a kasa,sai ga Shukura tana dariya tana hawaye wai ta tuna da Baffanta da Innanta da suka rasu,tun tanayi kamar wasa sai ta koma kuka gaba daya sosai take shesheka,ya danji tausayinta amma nata da sauki tunda taga gawarsu,shi kuwa bai san nasa ba ko daya.

kasa ce mata komai yayi har tayi kukanta ta gama sannan yace muje to,wani haushinsa taji wato shi bai iya lallashi ba,mota suka shiga suka dauki hanyar gida.
yau wani nishadi yake ji Shukura tayi masa abinda ya dace yayi Wanda bazai Iya Sabo da Momee da Abba,kida ya kunna me masifar dadi Shukura ta kama abin rigarta wani zare tasa a baki tana wasa dashi,Muryarsa taji yace me zaki ci yau ya fuskanci Bata wani iya girki ba kullum kayan zaki take ci,juyowa tayi ta kalleshi cike da murna, ba kara min kyau tayi ba, shi kanshi saida yayiwa Allah tasbihi,da sauri tace komai nake so na fada ? Yace yes, tace Allah ? Rantse kace Allah,ba zan rantse ba ni yaro ne ko dan Kauye ne cewar Ahleef, Shawarma da Pizza sai Madara me kwakwa,idan da chips and Egg ma zanci,yawwa na tuna fried rice da kaza itama kafin na kwanta zanci kaji ? Duk Wannan gurmin a cikinki zaki hada su yau ke kadai? To Bazan siya ba, shagwaba ta fara masa kaifa kace na fadi abinda nake so kuma na fada zaka ce a'a kawai ku dama yan boko haka kuke Alkawarinku ba cikawa sai dai ayi ta turanci,dariya ta bashi sosai Murmushi yayi yace Oho miki Bazan siya miki ba, kala daya zan siya ke ko lafiyarki bakya tunani,yana magana tana kallon lips dinsa tare da hakoransa,har ya gama ta tsura masa ido har sai da ya bigi sitiyari kadan sannan tace Allah kamar Saudatu ne kai, Harararta yayi kadan ke kuma me kama da Musa Driver na,Dariya tayi tace Allah ya kiyashe ni harda da yin maganar fulani hodi Jam wannan Driver naka me suffar yan ruwa,Murmushi yayi kadan shi zan aura miki ai nan gaba shine dai dai ke, glass dinsa ta dauka a wani waje cikin motar ta manna a fuska sai ya mata mugun kyau abinka da farar fata,ko da yazo inda zasu siya abinci haka ta fito da glass dinta sai kallonta akeyi yanda tayi kyau ka rantse yar wani Hamshaki ce,hannunsa ta rike Sabo da Bata taba ganin hadadden waje iri wannan ba sai taji tsoro ma, Mutane suna jinta tana wlh kamar a London,Sir kalli can naga irinsa a Makkah,ta daga kanta sama tace laaa ha ila kaga irin na film din nan wajen da akayi naushi aka Harbe yaran Boss irin saman wajen ne,wasu da yawa nan suka gane Shukura daga kauye aka zo amma a jikinta babu me ganewa,Ahleef ya take mata kafa da tasa tayi kara yace idan kika kara magana baza ki koma gidana ba a nan zan barki, Shuru tayi Bata kuma cewa komai ba har suka fito ta hango wani Building na Makeup cikin rada wai kar ta disgashi a mutane ta fara yafito shi da hannu wai ya sunkuyo zata yi maganar sirri,Ya dan duko kadan tare da mika mata kunne daya duk da haka saida ta dage kafafu sannan bakinta ya kai kusa da kunnen sa tace dan Allah can wajen ai gidan kwalliya ne ko ? Gashi nan Ansa Make up,Makeup kuma da hausa ai kwalliya kenan,ae kawai yace tare da mika ma plate din yace ta zabi abinda zata ci a zuba mata,ta dinga nunawa komai sai da ta nuna ana zubawa a gefe sannan yace tazo suje su zauna,Sama suka hau inda aka tanada na zama aci abinci,sai ta kalli plate dinta taga kalar abincin Ahleef daban da ya ebo babu shi a plate dinta,to ya akayi ita Bata ga wannan kalar ba gaskiya ita baza ta yarda ba kuma nasa zaifi nata dadi,Lemo ma kalar nata daban data zaba,kallon plate dinta tayi ta kalli na Ahleef,yana satar kallonta dama yana Sani yasa aka bashi special Wanda ba a wajen yake ba a kasa suke ajiyesu sai in ka karanta Menu nasu zaka San dasu,tana kalle kalle aka zuba masa Bata Sani ba.
sai kallon plate dinsa takeyi taki cin nata,yayi kamar bai ganta ba, ta fara cin nata sai ta tabe baki tana yatsina fuska,ta ja tsaki tana cakalkalashi a bakinta tace naka da dadi ? Yace kamar kunne zai cire,tace to ni nawa ba dadi dandana kaji,baki ya tabe ke kika zaba, to ni ya akayi banga irin wannan ba? Shuru ya mata yana jinjina kwadayinta,lemonta ta dauka ta kurba nan ma ta tabe baki tace baka ji ba kamar fitsarin jaka Allah basu iya komai ba, Shuru ya mata yana dariya a ransa,ta kalleshi ta kalli plate dinsa tace kaci a hankali ni ba ci maka naka zanyi ba, Murmushi yayi kawai yaci Gaba da cin nasa itama tana dan cakalar nata,taga da gaske cinye nasa zaiyi ba tare da ta dandanashi ba,Nata ta ebo kadan a Spoon tace dandana kaji to nawa,kai ya girgiza baya so,Ina Brush fa Allah kullum sau Uku kalli hakorana,na Sani ya furta,tace to San min naka naji kalarsa,plate din ya tura mata da ragowar kadan a ciki, ta cinye tas sannan ta kara jawo nata kalar ta cinye abinta,Lemo yake korawa tace sai ya San mata nasa taji irinsa,da kansa ya daura mata a saman lips wai tasha kadan.ta zuga da karfi zuuuuuuu har ta kusa zukeshi ya fisgo abinsa daga bakinta yaci gaba da sha.sai da suka gama sannan suka dauki hanyar gida abinsu.

Kwanaki kadan ba laifi tsakanin Shukura da Ahleef suna dan hira sama sama idan ta kama, yau ma 5pm Cikin kana nan kaya black jean da top Brown ya gaji da haduwa ya shigo a gajiye daga Office ya dawo,yana bude palo wani kamshi da sanyi ya dakeshi bai san sanda ya lumshe ido ba,Samansa ya Haura anan yaga gyara iya gyara yasan Shukura ce tayi,wanka yayi ya shirya Cikin 3qtr da riga Armless ya sakko kasa a gurguje nan ya iske Farhan har ya iso cikin shigarsa ta alfarma na Light blue Shadda,ya wani baje saman 3seater Remote a hannunsa yana chanja Channel na tv,Ahleef ya mika masa Hannu suka kashe sannan shi kuma ya dauki Remote na ac ya karo karfinta,Farhan ne yayi magana Cikin salonsu Guy kana hutawa fa wannan gida naka kamar me mata komai na daban,Murmushi kawai Ahleef yayi yana tunanin idan Shukura ta fito Farhan ya ganta taya zai wanke kansa duk da yasan Shukura yarinya ce me zaiyi da ita shi sai yar 25 zuwa sama kuma Farhan yasan da hakan.
kitchen Farhan ya shiga ya ebo kayan ci snacks da sha sannan ya dawo ya zauna suka fara hira irin ta zaratan abokai masu ji da kai, 15mnt tsakani sai ga Shukura ta bude kofa ta side dinta ta shigo Palon sanye da rigar Shaddar Ahleef ruwan toka Bata sa wandon ba sai rigar tazo mata har kasa tayi Rolling da bakin gyalenta na doguwar riga dan siriri,da gani wanka tayi ta shafa powder kawai da lipgloss,sallama tayi musu tare da gaisar da Farhan,cike da mamaki ya amsa,Ahleef kuwa tuni ya runtse ido yana tunanin amsar da zai bawa Farhan,saitin kafar Ahleef ta zauna a kasa zata yi magana sai taga Farhan yana ta faman kallonsu,sai ta fasa tace pls 2mnt zan ganka ta fada kasa kasa,Ahleef ya dan duko da kansa saitin nata yace fada min bazan iya tashi ba, Cikin rada tace 1k zaka ranta min,yau ma baice komai ba ya zaro ya bata,ta mike suna gani ta bude kofar tayi waje da Alama wani wajen zata je.
Chapter 17 · 0% Book details