Sashe 14
Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yau da safe da wuri sai ga Shukura da shishigi har kitchen din Ahleef anan ta soya doyarta da kwai Irin yanda Saudatu keyi,ta dafa tea yasha kayan kamshi ta ajiye a Dining ta wuce dakinta domin yin Wanka, Ahleef ya fito cikin Shirinsa na fita Office yaga an shirya abu a Dining,budewa yayi yaga doya ta soya yanka biyar ta cikin mutum daya,wato kanta kadai ta Sani, sai ya zauna yasha tea dinsa tare da cinye doyar tata tas bai bar ko kwallo ba
Ya Mike ya koma Bedroom dinsa yana amfani da System Kafin ya fita,Shukura Ansa jallabiyar Ahleef Milk ta fito zata kwashi girki ta bude plate wayam ba komai,tace to ko shine ya cinye min? Bari naje na tambayeshi naji aiko idan me gadi ne wlh sai ya gane kurensa kuji karfin hali,Saman Ahleef ta nufa sai taji tsoro tasan baya daukan raini,sai da ya fito cikin shirinsa tana palo lokaci da saura ta tsuguna har kasa jikinta na rawa tace ina kwana, baki kawai ya tabe,ta maza tayi tace uhm...Kawu na kaine ka matsar min da abincin dana dafa,wai wayo tayi masa ya matsar mata kar tace ya cinye mata, Shuru yayi mata tace Kawu dan Allah nace Ko kaine ka boye min wata doya a plate? Na sanka da kirki shi yasa nace ko kaine ka boye min ita, ya ganeta tsab, sai yace ban gane ba au har girki kikeyi dama? Au ba kai ka cinye ba ? harara ya zuba mata yayi gaba tare da cewa ni gidana tare da Aljanu nake rayuwa maybe sune.sai yaga ita ko a jikinta Bata wani Jin tsoron Aljanu Mamaki ya kamashi yar yarinya karama da ita Amma Bata Tsoro lallai girman kauye ce.
Sabon shiri ya sake kamar baza a mutu ba, ya fito ya iske Shukura sanye da Jallabiyarsa Milk sabuwa dal ta saka masa ta wani jera girkinta a gabanta harda Fruits cikin karin safenta hhh kuma abinda ya bashi dariya da yaga danwake a gefe da safe haka,ita Bata iya girke girke ba sai na gargajiya sai doyar da ta koya wajen Saudatu shike nan,suma na gargajiyar kadan ta iya,duk Bata San illar zama daga ita sai namiji a gida daya ba,sabo da iyayenta basu nuna mata komai ba kawai abinda taga dama shi takeyi. iyaye Irin wannan ke jawowa kaga yaran wasu kamar dabbobi haka suke a cikin alumma.
Tsawa ya mata kadan keee...tayi mugun tsorata ita Bata saba ba,ba a yi mata tsawa, sai tagigice kawai ta fashe da kuka, Kuka take kamar ana mata azaba,lallai zaki bar gidan nan kuwa dan iskanci daga miki magana,kayan maza kike sawa baki da ilmi babu kyau mace nasa kayan da Akayi su domin Maza haka ma maza,Allah ya tsinewa mace me kamanceceniya da da Namiji, haka Namiji ma,sai kina shigar min Bedroom baki da hankali kina ebo min kaya.
Shukura wacce tayi mukus taji ance zata bar gidan,Ta turo baki cike da shagwaba kamar zata narke tace to ai lalurace tasa,kayana suna Hotel na gudu kudina ya kare,kuma bani da kaya shine na ranci naka ka daina masifa pls kudi Sun kusa zauna min kwana nan zasu zo zan biyaka abinka, kuma sai na siye gidan nan idan nayi kudi ya zama nawa gaskiya yayi min.
Dariya ma ta bashi daga taimako shine zata siye masa gida idan tayi kudi,mazewa yayi yace to karki kara taba min kayan sawa ta ya isheki haka,in ba haka ba wlh bulala zan siyo a gidan nan,Dariya tayi ya kalleta suka hada ido ya bata rai Irin karfa a rainashi,wayarsa ce tayi kara ya dauka Hello Momee gani nan Airport din zan zo yanzu,da sauri ya dauki hanyar barin Palon yace ke taso muje na siya miki kaya karki kara taba min kaya,da Karfi tace Allah da gaske kake? Kace wallahi tallahi? taga bazai kulata ba kuma yayi Gaba abinsa,Da gudu ta kwashe kayan abincinta ta kai Kitchen ta figi dan gyalenta ta yafa a saman kanta sanye da jallabiyarsa ta fito da gudunta,Jallabiya ta tadeta ta fadi tasan jiranta yakeyi amma sai ta fara kuka a wajen yanda ta saba yi a gidansu gaban iyayenta,ko kulata baiyi ba da Alama ba driver zai tafi shine a mazaunin Driver,da sauri ta kara mikewa a rude ta bude Bayan mota ta zauna maimakon ta zauna yanda ake zaman mota duk ta rude sai ta zauna takalli bayan motar saitin Boot kamar biri,kafafunta ta lankwashesu ta zubawa bayan titi ido ba gabansa ba,Ahleef bai san sanda dariya ta kamashi ba kawai bai kulata ba dan mugunta yaja mota a haka,sai dariya akeyi Sabo da duk motar daya wuce to sai Sun kalli fuskar Shukura ana ta dariya,Yana Sani ya fisgi motar tayo luuu ji kake guf ta bige keyarta da bayan kujerar gaba me zaman banza tunda dama baya take kallo.
Har airport yaje yayi parking sannan ya fito ya Shiga bayan motar kusa da Shukura,wata Igiya doguwa ya dauko,yace oya kwanta,a tsorace ta kwanta tunaninta saceta zaiyi ko dan yankan kaine dama Bata Sani ba ta kawo kanta.
Hannayenta ya hada biyu ya daure tam,Kamshinsa duk ya cika mata hanci Har hanci take kara budewa,Kafafunta suma ya hade ya daure sannan ya fita ya kulle motar yayi gaba wajen su momee.
Suhail su zasu koma Us schl,sunyi shirin barin kasar,Momee kuwa Abba yayi fushi matarsa tayi jinya an boye masa shi yasa yace da ita zai tafi yanzu yafi kula da abarsa sai nan da 2mnths zasu dawo kasar, Latifa da Niima kawai za a bari,sai Ahleef dake can gidansa,Sallama sukayi da juna a gurguje an fara screening ma, Shukura tana mota da kyar ta Samu ta Mike Zaune tana hango Momee suna magana Ahleef Sun kebe,wayyo taso Ace Ahleef bai daureta ba da sai taje wajen Momee ta gaisheta Amma ba damar hakan, Niima tana Airport din can gefe tare da sabon saurayinta Yazo wai zai yiwa iyayenta a dawo lfy, kishi ya kama Ahleef yasan dan ta kona masa rai ne yasa ta kira saurayinta,kuma kishinsa ya motsa da kyar ya danne Har su Momee suka tashi sannan ya bar wajen a fusace,yana zuwa fuska ba Rahma ya kwance daurin da ya yiwa Shukura yace fito ki koma gaba, lokacin da Shukura ta fito har zata shiga gaban mota akan idon Niima,kamar kiftawar ido sai ga Niima taja rigar Shukura da karfi ta fisgota baya,Shukura ga saurin zuciya da daukan Hukunci Bata tsaya sanin wace ko waye ba yar karama da ita amma ji kake Tasss ta kwashe Niima da mari me mugun Zafi Wanda saida marin ya jawo hankalin kowa aka fara kallonsu,Ashar Niima ta dura kafin tayi wani motsi tuni Shukura ta shige mota ta rufe tare da sauke Glass tana cewa ki kiyayi ranar da zamu kara haduwa wlh sai na miki Illa ba irina akewa wannan a kwana lfy ba ba a takani duk inda muke da mutum, kaf Abuja birnin tarayya kinga Wanda ya Isa dani ta furta tana Nuna Ahleef,shi kadai ne zai iya Sani ya hanani,shine me fada aji shi kadai zan iya kyalewa sai wasu Dattijai mata su biyu,(momee da Saudatu) Amma bayan wannan to babu Wanda ya Isa ya min na kyaleshi bare ke banza a banza gaja,kazama,yar Kauye dake ana birni amma an kasa wayewa ban hakura ba duk ranar da muka kara Huduwa wlh sai kin fada,me kai kamar murhu.Niima ta Sandare a jikin motar tana mamakin wannan yar yarinyar da Bata fi mate din Latifa ba Amma take ci mata mutunci haka ta window cikin mota take aiko mata da zagi haka,Shukura ta tsinke mata tunani da cewa da Allah ki dinga sallah akan lokaci ko kyayi kwarjinin musulunci gashi Sabo da baki da kwarjini kamata na kare miki zagi da gani addininki bai cika ba, kinga kawu Ahleef shi ko kallon banza ban Isa na iya yi masa ba,ke kuwa har mari kika sha to ki kiyayeni yarinya dan ba sanda a kusa ne da wlh sai na sumar dake da ita,wani farin ciki ya lullube Ahleef yau Shukura ta gama masa komai a duniya bai san sanda ma ya fara dariya ba dama yana neman wanda zai goge Niima shi idan yayi mata girmansa ya zube kuma ko Sabo da Momee tare da Abba baici ace yayiwa jininsu wani abu ba.
Niima ta girgiza da ganin me mugun kyau haka,dama ana samun irin wannan a kasar nan, To a ina Ahleef ya samota kyau irin na Ahleef Amma yarinyar kamar ma ta Fishi ita bata taba ganin me kyawun Shukura ba a duniya sai ko Ahleef,nan take Haushin Shukura ya kamata taji ta tsaneta Sabo da ta fita komai da komai,ita Niima Allah ya zuba mata Hassada Bata kauna wani ya fita,a ranta tace sai na gano yarinyar nan yar uban wace,kuma tana bakin ciki Ahleef ya samu me kyau irin wannan tafi so taga ya auri mummuna dan kawai kar ya ji dadin duniya,bata so ta Ganshi yana farin ciki shi yasa ma Bata damu sosai ba akan cin mutuncin da Shukura tayi mata,.