← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 59

Sashe 13

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saudatu jiki na bari ta fara zubawa Su Abba,zata zubawa su Salman yace no na koshi ni,Suhail ma yace bazai ci ba ruwa zai sha kawai,Saudatu da fara'a ta kalli Ahleef tare da cewa kai fa Alhaji me za a zuba maka ? Ahleef ya kalleta aiko sai ya saki murmushi kamar ya santa yace Umma wanne kika dafa da hannunki ? Ta nuna masa kala uku harda Zobo Drink me dadi tace wannan nayi da kaina,yace zuba min su zan ci ni,Ita dai Saudatu sai tana ganin kamar ta San Ahleef amma ta kasa ganewa,Mama kuma da Su Hafsy sai kallon Ahleef sukeyi suna kallon Saudatu sai suka ga kamarsu daya har tayi yawa ma, komai nasu har hakoran kusan iri daya,Bayan ta zuba masa ya karba da kansa, har zata bar wajen Ahleef yace zauna mana Umma idan na gama sai mu tafi na jirasu a waje,Tsoro ya kama Saudatu tasan yau tata ta kare a gidan,tana zaune ya gama cin abincinta me shegen dadi sannan ya Mike Saudatu tabi bayansa suka fita har waje,yace Umma haka kuke rayuwa ke yar aiki ce ? Saudatu tace ae wlh rayuwa kenan,Ahleef yace ke da mijinki duk nan kuke aiki Saudatu tace ae a takaice ta bashi labarin irin zaman da suke a gidan,da wulakancin da suke fuskanta ita da mijinta,Ahleef ya tausaya musu yace watarana idan na samu time zan daukeki ki dinga dafa min abinci ina biyanki albashi Kin yarda? Murna ta kama Saudatu ta dinga godiya harda durkusawa har kasa,yace mijinki kuma sai na kaishi Office dina yana min goge goge ina biyansa,Zan baku wajen zama a gidana zan dawo na daukeki nan da 3wks.
Godiya kawai Saudatu keyi masa,yace haba Umma ki daina godiya haka ya zaro 10k ya Bata.

Abba ya fito tare da yan gidan suka rakasu suka tafi,Mama lokacin suka rufarwa Saudatu da balai da masifa iri iri suka ce gobe sai Sun bar musu gida,Asiri take wa bakinsu kowa yana sonta,tana mallake musu masu kudi,sai kace wata budurwa ita me zatayi da wasu maza masu kudi Saudatu ta furta a ranta, Babu hakurin da Bata basu ba har mijinta da suka sa masa dan dako Sam suka ce dole gobe su bar musu gida.

Tunda Shukura taga Ahleef ya bar gidan ta fito ta gyara gidan Neat har samansa yana ta kamshi ko ina ta canja tsarin gidan yayi Masifar kyau, tayi girkinta taci ta koshi ta dauki remote tana ta danne danne har Allah ya taimaketa ta kunna TV ta kamo tashar American film tana ta kallo har ta gaji ta mike ta shige bedroom din Ahleef toilet dinsa ta shiga tace dole na dana,ta fesa wankanta da kayan wankansa,ta fito ta shafa Body lotion dinsa,kayan gyara gashinsa da su ta gyara nata yana kamshi, Cikin sip dinsa ta bude ta duba cikin wankakkun shaddojinsa ta zabi wata ruwan toka ta dauki iya rigarsa wata yar fitted hannun links ne ta sa abarta shar tayi kyau kuwa,bata sa da wandon ba, turarensa iri iri ta fesa sannan ta kara gyara masa komai na dakin ta fito ta baje a palo tana kallon film tana shan lemo abinta,Ahleef har ya dawo Bata Sani ba, sai ji tayi ana kokarin bude kofa da gudu ta kashe TV ta arce inda ta saba buya,tun daga waje Ahleef ke Jin karar TV amma abin mamaki yana shugowa yaga TV a kashe,sai kwalin lemo,gashi shi yasan bai sa a gyara masa gida ba amma yaga gida sai kyalli yakeyi da sabon kamshi,tsoro ya kamashi ya haura sama yasha mamaki kalar gyaran dakin na musamman har Bedsheet an sake masa,Ya fito ya duba gidan kaf ko ina yasha gyara, ya tambayi security ko wani ya shigo ? Yace shi ba Wanda ya shigo,ya dawo ciki a fili yace wlh idan na kara ganin abin Tsoro guduwa zanyi na bar gidan.

Kwana uku tsakani kullum sai Shukura taje wajen da suke soya doya amma ba Saudatu ba labarinta,ta tambaya amma babu Wanda ya San inda Suke,har gidan Da Saudatu ke aiki taje amma akace an koresu daga aiki har kuka Shukura tayi sannan ta dawo gidan Ahleef taci Gaga da buyanta.
Yau Misalin 12 na dare Ahleef yana gida,Shukura ta sa rigar Shaddarsa wata Milk color Garin labe labenta ta daki wani karfen motsa jiki ta fadi Tim a kasa,kafarta ta dauje Jini yana fita,Kuka ta fashe dashi sosai ta manta Sam da za a kamata Bata kaunar ganin jini na fita sai ta fara kuka,kuka ta shiga rerawa,Ahleef Tsoro kamar ya sume,ya dauki katuwar kujerar Mirror yana lallabawa da niyyar duk Wanda ya gani ko aljanine fasa masa kai zaiyi,yana lallabawa a tsorace har ya bude kofar inda yake Jin kukan na fitowa a hankali ya Shiga,Yaga Gashin mace ai ba shiri ya jefar da kujera zai gudu regarsa ta makale a kujera ya fasa kara,Shukura kuka ya dauke dif tasan asirinta ya tonu shike nan korarta zaiyi kwanan kan titi ya ganta,Fuskarta ta dago suka hada ido da Ahleef yana kokarin guduwa rigarsa ta makale,Cak ya tsaya da yaga kamar yarinyar da suka kwanta a Hospital da Momee,kuma wacce ya gani sanye da Jallabiya irin tasa,tabbas itace ashe dama Kusan 2wks kenan tana gidansa ashe itace take sawa yana tunanin Aljanunee,wani bakin ciki ya kamashi,tana jira taji saukar duka sai taji cikin fushi yace Amma kin zalunceni kin cutar dani,all ths While ashe kece,why baza ki fada min ba ki rokeni na baki inda ya dace dake,hawaye ya kwararo mata na tsoro cikin rawar murya tace uhmm..tsoro...tsoro naji karka koreni wlh zan baka labarina ni marainiya ce,Hey...u better stop tht nonsense ina ruwana da maraicinki Who even care,Mikewa tayi ya kare mata kallo wato kayana ma kike sawa Sabo da kin rainani,ashe duk abincin nan kece kike cinyewa,shuru tayi ta wani turo lips Gaba,tace Allah baka hakuri, dan Allah kayi hakuri bari na bar ma gidanka,ta kwaso kayansa sunkai kala bakwai da take ta sawa tace ga kayanka,mamaki ya cikashi ashe barnar har ta kai haka ji yake kamar ya kasheta,rokonsa tayi dan Allah ka taima kamin da wajen kwana kafin na samu kudi,Kin San da haka me yasa baki rokeni ba tun wuri,har Ya juya zai tafi ya dawo yace sai kiyi ta zama Mayya,ya Leka lungun da take boyewa tana bacci yace hmmm tare da bude Bedroom din da take shiga toilet din ciki tana wanka yace ga daki nan kuma wlh kina min shirme sai kin bar gidan nan tunda bana ubanki bane,Murna ta kamata ashe haka yake da mutunci, bata taba zato ba gashi ya bata daki ma tsantsarere, kallonsa tayi baki a washe tace ashe mutunci ne da kai haka na gode,Allah yaji kan magabata,Allah kara budi da arziki ya biyama bukatunka na alkhairi yasa Aljanna makoma,Baki ya tabe tare da cewa yar Maula,Shuru tayi murna ta isheta Bata ma ta ciwon da taji tace ba dadewa zanyi ba ina samun wasu kudi zan bar ma gidan,ina sa rai da wasu kudade naji a jikina zanyi kudi kwanan nan sai na barma gidanka karka damu saura kadan.tsaki yaja yayi gaba abinsa yana cewa sai kinyi kudi ma zaki barmin gida? Ba rana kenan ya barta a wajen tana murna harda tsalle.

AsmaBaffa
[7/22, 1:12 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO

7

Official

By
AsmaBaffa

ZAMA NA AMANA 2 FACEBOOK wannan page naku ne,na gode Allah ya bar kauna.

FLOWER jinjina gareki wajen Sharhi ba daga kafa tnx alot.

Fans bana son tnx fa Sharhi nake bukata ni.

Bedroom din daya Bata ta fada ciki tare da kwanciya saman Bed tana faman murna,yau ba wani tsoron Aljanu yayi bacci sosai shi kanshi washe gari yayi mamakin baccin daya kwasa ya nisa tare da cewa amma yarinyar nan ta cuceni wlh yaushe rabon da nayi bacci haka,ko gidansu zai maidata wajen Momee ina shi ina kwana gida daya daga shi sai budurwa ina bazai iya ba, wani tunani ne ya fado masa sai kuma yace no Momee zata kwasheta tace zata zauna a wajenta har abada shi kuma bai Son kwashe kwashe kawai ta gama kwanakinta ta bar masa gida shike nan,Saudatu ce ta fado masa a rai yace dama dawo dasu yayi gidan suka fara aikinsu kawai yace da yamma zai tura Driver ya dauko masa su.

Saudatu kuwa tunda aka koresu basu da wajen zama sai can karkashin gada suka koma suna kwana ita da Alhaji Amadu,ruwa,iska komai a kansu yake karewa suna Cikin yan cirani suna fadi tashi,Babu wurin kwana ina wata sana'a idan ma Sun bar gari to basu da wajen zuwa, Ahleef yana ranta Sabo da yace zai daukesu aiki dan haka Kullum Saudatu da mijinta sai sunzo kofar gidan Alhaji Dauda Sun yini Ko zasu ga Ahleef yazo daukansu,Saudatu da ta gaji da wahala Duk dauriyarta Yanzu kuka takeyi sosai wai su me yasa tuntuni rayuwarsu a wahala suke ne,yau ma suna nesa da gidan Alhaji Dauda ta tsuguna a kasa Bata San sanda ta fara hawaye ba, shi kuwa Alhj Amadu kusa da ita ya zauna yana tausaya wa kansu matarsa balarabiya talaucinsa yasa duk ta tsufa, da yasan hakane da bazai aure ta ba, tunda yasan talauci a jininsu yake gashi har yau ya jawowa masoyiyarsa ma, Lallashinta ya fara suka samu wurin inuwa suka zauna Kafadarsa ya miko mata tare da cewa kwanta Saudat ki huta,ita kuwa dama dake balarabiyace ko a jikinta ba ruwanta da mutane ta lafe a kafadar Alhj Amadunta.
Haka yauma suka karaci zamansu har dare ba Ahleef ba alamarsa suka hakura suka koma Karkashin gadarsu inda yan cirani ke taruwa su kwana mata da maza babu iya shegen da ba ayi a wajen sai dai ka sharesu kawai.
Chapter 13 · 0% Book details