← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 59

Sashe 26

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ne ya fara magana Alhmdllh gaba daya gashi mun hadu,Ahleef kaine babba ta dalilinka kuma abubuwa suke faruwa a gidan nan marasa dadi Wanda bamu gane gaskiyar faruwan hakan ba, ke Niima gamu baki daya a nan fada mana abinda ke faruwa,Momee cikin fushi tace Abban Latifa ba haka za ayi ba gwara farko kowa yasan waye Ahleef a wajenmu har Wanda yake fifitawa akanmu su Sani ni bazan lamunci haka ba, nan fa Momee ta refe baki ta fara kwararo labari tun farkon batan sa har zuwa dalilin da yasa suka je gidan raino suka dauko shi har jarin da Abba ya bashi ya zama me kudi zuwa yanzu komai saida ta fada, Cikin fushi Abba yace Haba Momeen Yara ina hankalinki yake,mene na bayyana jarin da na bashi,wannan gori kika yi masa kuma shi ma danki ne kuma sai da kowa ya sheda kinfi sonsa da yaranki na cikinki,kuma jari dana bashi ki Sani kyauta ne halak malak ba bashi lauyoyi Sun sheda Sabo da irin wannan ranar dama nayi haka,nasan ku mata tunaninku kadan ne abinda zuciyarku ta baku sai ku aikata, ke ai abin kunya ne aji wannan a bakinki,halayen Niima waye bai sansu ba amma kin kasa fahimta.

Ahleef yace kuyi hakuri Abba da Momee Idan na Bata muku kuma bari na fada muku dalilin da yasa bana saurarar Niima da kuma haduwata da Shukura,Haka ya basu labarin Irin wulakanci da cin mutuncin da Niima ke masa da Wanda tayiwa Shukura iri iri, sannan ya basu labarin Haduwarsa da Shukura har zuwa yau, sai ya bada labarin haduwarsu da su Umma har Baba Bayan ya gama ya kara bawa Momee hakuri.

Saudatu tare da Baba Kuka suka fara yi,Abba yace kuyi hakuri wannan ba abin kuka Bane,Momee tace sayi Shuru tunda sunzo zasu dasa mana rashin zaman lafiya a gida musamman wannan kodaddiyar ta furta tana nuna Shukura, Shukura tayi murmushi Sabo da ita Bata wani fushi sai tace kodaddiya kamar Tsohuwar atamfa fa Momee...Babane ya Katse ta da cewar wannan Ahleef dai danmu ne na jini wlh,na dade ina bincike a kansa sabo da yanda mutane ke cewa kamarmu daya,ban fadawa kowa ba Sabo da kar ace karya nakeyi, bari nayi lokaci yayi na furta yau Allah yayi,Momee tace tanan kuka Bullo kuma ? Baba shima ya bada labarinsa dana Saudatu kaf bai boye komai ba har sace Ahleef,sannan yace abokin Ahleef Farhan shine ya sameni ya sanar dani tarihin Ahleef kaf anan na gane danmu ne, karshe Baba yayiwa su Momee Addua da godiya na rike dansu da Amana, Saudatu kukan Murna takeyi kawai,Abba yace tabbas biri yayi kama da mutum Yanzu muje asibiti ayi gwajin DNA kowa ya fita daga Zargi, Momee ta zabgawa Shukura harara sannan tace muje a duba amma wlh wannan Tunda Bata neman zaman lfy Baza ta zauna a gidan nan ba, kuma Ahleef indai har ni na raineka na Isa da kai sai dai ta koma kauyensu tunda babu dangi tsakani taje can inda ta fito kuma kar naji ka kaita wani waje ka ajiyeta wlh.

Shukura batayi fushi ba duk da taji haushi sai tayi murmushi tare da cewa Momee zan tafi dama amma dan Allah kiyi tunani akan Niima ki daina yarda da zancenta karya ta shirya miki,wani murmushin mugunta Niima tayi taci nasara akan Momee an kori Shukura,Abba yace Kiyi hakuri yarinya ki koma gaban danginki kawai yafi miki mutunci, Shukura tace inshaallah Abba ba damuwa amma bari na baku lbr na,Momee tace ba sai kin fada ba bama bukatar ji,iyayenki Sun rasu mun Sani thats all, Niima tace hakane kawai ya ishemu,Abba ya harareta tayi Shuru.

Ahleef tausayin Shukura ya cikashi ransa ya baci sosai ji yake dama shi aka kora,Da fara'a Shukura tayi musu Sallama ta fita daga palon da sauri Sabo da dab take da tayi kuka,Ahleef ya mike da sauri zai bi bayanta,Momee ta daka masa tsawa dawo ka zauna, Saudatu tace kayi biyayya itama kamar mahaifiyarka ce ta fimu iko da kai a halin yanzu,Baba ma haka yace daga nan suka dunguma zuwa asibiti,kafin su tafi saida Umma ta jadaddawa Shukura ta zauna ta jirasu kar ta tafi, tunda Momee ta kori Shukura batayi adalci ba Sam ta nuna son kai suma bar mata gidanta zasuyi su tafi da Shukura,ita kuma Shukura tasan me Umma ke shirin yi dan karta kara raba da da iyaye kawai ta shirya kayanta kala biyar da komai ta dauki kudin break dinta da Ahleef ya Bata ta ajiye a hannunta dubu goma ta zuba a jaka ta dauki katuwar Yogourt me kauri tare da soyayyun naman kaji Zata dinga sha a hanya ta ta sadada ta fito kenan suka hadu da Niima Zata fita da car key a hannunta, dariya tayiwa Shukura tare da cewa ba a ja dani yarinya, Dutse kato Shukura ta dauka tayi kan Niima dashi ta rotse mata kai,Kara Niima ta saki ta fadi sumammiya jini na zuba a kanta, Shukura tace dama na fada duk ranar da zan bar gidan nan dole sai wata ta tafi gadon asibiti, na yarda zan bar gida amma dole kema kiyi gadon asibiti.

ruwan cikinta Shukura ta taka da karfi tare da tsallakewa tayi tafiyarta ta bar gidan kawai tana goge hawayenta yanzu ta daina ganin Yayanta Ahleef,Niima kuma yan aiki Sun taru a kanta ba abinda basuyi mata ba amma Bata farfado ba,Momee suka bugawa waya,Momee ta fashe da kuka a asibiti tana ka gani ko Ahleef abinda ka jawo mana gashi nan ta kashe min yarinya,Wayar Ahleef ya karba yace a kawo Niima asibiti itama, Abba yace Good yarinya tayi daidai nasan Niima ce ta tsokaneta ai hakan yayi kyau ina ma ta karyata gida uku da kowa ya huta.
Likita yayi gwaji ya tabbatar Ahleef dane ga Umma da Baba Saudatu da Amadu kowa yayi farin ciki musamman Ahleef Farhan ma yana asibitin Ahleef yace yayi sauri yaje ya dauki Shukura kar ta tafi kafin su dawo gida.

sai da Shukura ta shiga taxi sannan ta fara tunanin ina Zata je, kawai tace a kaita tasha tana zuwa ba Bata lokaci ta shige motar Kaduna state motar Bata cika ba Baza ta tashi da wuri ba Shukura ce dama farkon Shiga motar,Lokacin Farhan kuma yaci uban birki a gidan security yace ai ta bar gidan tuni, da sauri Ya kira Ahleef a waya yana sanar masa,da Sauri Ahleef ya bar su Momee gaba daya tare da fadawa motarsa ya fusgi mota a gigice Bai tsaya ko ina ba tashoshi ya dinga bi har ya je tashar da Shukura ta shiga mota saura mutum biyu motar ta cika Ahleef yayi parking motarsa ya shiga tambayar Masu mota yana bada kamannin Shukura,Wani dattijo yace ina tunanin tana waccan yellow Bus din indai kyakyawar nan ce,Ahleef ya je motar har jikin motar ta Window ya hango Shukura ciki tana shan Yogourt dinta tana hawaye,Murmushin da bai shirya ba ya saki ta Window ba zato tana waigowa ta ganshi a tsaye,tunaninta gizo yake mata sai taga da gaske ne,Murmushi tayi masa sabon hawaye ya shararo mata,alama ya mata da hannu ta fito sai ta makale kafada,dariya yayi yana yafitota da hannu ta sakko amma sai ta makale kafada, ga Hadari ya hada gab ake da fara ruwa,Driver yayiwa magana Shukura Zata fita,tace Ni Bazan fita ba Driver,Ahleef ya zaro kudi wanda bai san nawa Bane ya bawa Driver kan ya sauke Shukura,Conductor yaga kudi a banza yace kowa ya fito dole sai Shukura ta fito ta karfi,Ahleef yace duk Wanda yake motar ma an biya masa kudin mota zuwa inda zaije ya fito da wasu kudin ya kara bawa Driver,da sauri passengers suka sauka sai Shukura a ciki taki fitowa gashi an fara yayyafi,Ahleef ganin Baza ta fito ba ya shiga da kansa ya fara miko kayanta kasa conductor ya kai jikin motar Ahleef ana dariya ana shan kallonsu,hannun rigarsa ya nade ya daukota a nutse cikin dabara suka sauko kasa,Ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya passengers suka koma motarsu,ita kuwa Shukura wutsil wutsil takeyi har ta kwace a hannun Ahleef yana Damkota tana kwacewa mutane suna kallo, Shukura ta fara ihu tans zan tara ma mutane ka kyaleni wayyo jama'a a taimakeni barawo ga dan mafiya, Ahleef shima yace kuyi hakuri kanwata ce jiya aka sallameta daga asibitin Mahaukata,tana da tabin kwakwalwa,mutane suka fara Allah bada lfy ai ga alama ma ta nuna Allah sawwake yarinya Allah baki lfy kinji.

jawota yayi jikinsa har yogourt na zubo masa kadan a rigarsa kamar zai maidata cikisa ga ruwa ana shimfidawa,daukanta yayi cak amma ta fara kokawa dashi tana wutsil wutsil ruwa na dukansu,wasu da suka fake a shaguna ta glass din Windows suke ta kallonsu suna dariya,da kyar ta kwace kanta har ta zura da uban gudu cikin zafin nama ya damkota yana dariya ita kuwa ta maida abin da gaske ta wani hade fuska,jawota yayi sosai ta fada kirjinsa ya rungumeta tsam a jikinsa wani irin yanayi suka tsinci kansu ciki musamman Ahleef bai taba Jin irinsa ba sai a jikin Shukura, a kirjinsa ta lafe tayi shuru tana shakar kamshinsa ta daina Wutsil wutsil, ruwa ya kara tsugewa a hankali ta dago da fuskarta tare da zuba masa kallo na musamman Wanda dole sai mutum yaji a jikinsa,Hannunta yarike tare da furta Muje mota duk yayaninsa ya canja,kwar jini ya mata nan take ta kasa yi masa musu ta bishi suka shiga mota,sun jike sharkaf da ruwa,motar yaja zuwa gidan su Farhan, Shukura sai fushi takeyi tana share Hawaye har suka karasa gidan su Farhan.
su Umma dasu Momee saida suka je har gidan Raino aka tabbatar da komai gaskiya ne sannan suka wuce gida,Momee ta zauna tana Jinyar Niima.
Chapter 26 · 0% Book details