← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 59

Sashe 12

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana Shiga Hospital yayi arba da Niima tazo itama yau,kirjinsa ne ya buga ganin yanda ta kara wani kyau da kiba gashi ta sha kyau,Nan take Tsohon ciwonsa ya motsa ji yake kamar ya rungumeta,ita kuwa Niima wani kallo ma take masa na wulakanci ita tunaninta kyau shine so,ganin tana da kyau yasa sai yanda taga damar juya maza,sai kallonta yakeyi kamar ya hadiyeta zuciyarsa tayi rauni Hawaye ke shirin zubo masa shi kadai yasan azabar da yakeji a kirjinsa.Momee ta gano hakan ranta ya kara jagulewa tana son Ahleef fiye da kowa,Abba ma bakin cikin Niima yake ta gama Bata masa rai,haka su Suhail,Abba ne yayi magana Ahleef an sallameta fa muje gida,Momee Hannunsa ta riko Cikin kasa da murya tace My Dear Son ya akayi ne ? Kayi hakuri kaci gaba da addua kaji,ka daina damun kanka zaka sa ciwona ya dawo,murmushin karfin Hali yayi kawai yace to Momee ba damuwa lets Go, har Abba sai da ya murmusa ganin yanda Momee da Ahleef suke magana a hankali babu me jinsu,Suhail yace Bro ko sannu da zuwa baka yi mana ba, Salman yace nayi fushi ni suna ta dariya Gaba daya banda Niima dake taunar chewgum ta wani hade rai,Ahleef ya kalleta dan kar Momee taga kamar ya tsani yarta yace yan mata ba magana ? Kamar gimbiya da kyar tace sannu ya kk ? Yace Hmm Kawai ya shareta,ba karya Niima satar kallonsa takeyi yanda ya gaji da haduwa ga kyansa ba a magana kullum karuwa yake,tabe baki tayi tare da cewa can da matsalarsa.

Momee tasan idan tace Ahleef sai ya dawo gida da zama ta shiga hakkinsa Sabo da Niima ce bai son ta zauna a ransa shi yasa yayi dan nesa dasu gwara ta kyaleshi ya samu Nutsuwa,suna Komawa gida tace Son tashi ka tafi gidanka ka huta naga ka gaji jeka gobe ka dawo jeka huta,dama Kadan yake jira Sabo da Niima tana ta faman shige da fice hankalinsa yana tashi soyayya tana matsa masa,sallama yayiwa kowa ya wuce zuwa gidansa zuciyarsa a jagule,lokacin Shukura ta dade da dawowa gidan tuni.sai yanzu Yaga Bedroom dinsa an lalata masa shi kamar wani ya kwanta,kayansa kuma kamar an taba su, sai yayi tunanin idonsa ne ke masa gizo Amma gobe zai fadawa masu gyara gidan su kara gyara gidan,kudinsa ya duba ya gansu yanda suke ba a taba ba, shakira halayenta ba sata a ciki,ko nawa zata gani komai talaucinta baza ta dauki abinda ba nata ba bare kudi.

Bayan yayi shirin bacci sai ya fito zai duba gidansa tare da kashe Light lokacin Shukura ta shiga kitchen dinsa ta kwaso su Apple da sauran kayan Fruits tana wucewa shi kuma ya fito yaji kamar an rufe kofa da gudu yabi bayanta amma kafin ya kamata tuni ta boye shi kuma gani yakeyi kamar mutum kamar ya gani,a hankali yace lallai aljanu ne a gidan nan masu yawan gaske,amma akan na koma gida da zama gwara nayi rayuwa da Aljanu Sabo da Niima ta dawo gida yanzu,bazai iya canja gida ba Sabo da yafi son gidan da yake ciki, to ko Security camera zansa koma mene ai zan gani,to ai aljanu ne kuma ba a ganinsu idan kuma ya gansu zai tsorata,motsi yaji kamar an bigi wani karfe da sauri ya juya baya fara gudu gudu sauri sauri ya kulle kansa a Bedroom tare da kudundunewa cikin bargo yana addua iri iri har bacci ya kwashe shi,Shukura tana kallonsa tana ta dariya kasa kasa lallai wannan matsoraci ne na gaske.

Saudatu yau Alhajin da suke aiki a gidansa zaiyi baki zasuyi Meeting na business Ogansa me gidansa tare da Dansa zai kawo masa ziyara gidansa a nan zasuyi Meeting Sabo da Alhaji Dauda abokin Abba ne kuma suna Business da Ahleef yana ta musu mitar sunki zuwa gidansa,gaba daya gidan yan mata da samari tare da iyayen duk Sun rude Sun gigice sai kwalliya Suke zubawa kamar zasu je ganin sarki Sabo da Dan Abba yace yana sonsu,Mama Cewa take yawwa yan matana kuyi kyau sosai so nake Ahleef ya zabi daya a cikinku ya aureku burina ku auri me kudi irin babanku Wanda zai dinga kaini Makkah da kasashen turawa,wanda zai dinga siyo min super England ba wanda zai siya min Nichem ba,gidan da zaku huta gidan Naira,Ko Abban ne yace yana Son daya dole na bashi komai tsufansa,Yan mata suna dariya tare da cewa ai sai Mama Allah bar mana ke, Wani Saurayi zai kai shekarun Ahleef Mubaraq yace ni kaina da Abban yana da budurwa lallabawa zanyi nayi Auren jari da ita,Karaf Mama tace tana nan sunanta Niima har Company gareta ban San me yasa aka fasa aurenta da wani ba ban San kan lbr ba Amma tana nan batayi aure ba kaje kayi duk yanda zakayi ta soka dama gaka kyakyawa da kai duk yarana babu me kyanka,duk abinda suke fada Saudatu tana goge goge tana jinsu sai da gabanta ya fadi da taji an ambaci Ahleef me sunan jaririnta Amma tasan shekaru 31 ba wasa ba, tuni ta hakura tasan danta yan mafiya Sun yankashi tuni,Har so take a duniya ta ga waye wannan me sunan danta daya bace gashi sai rubibinsa akeyi Sabo da yana da kyau da kudi.aranta tace ai kuwa sai ta labe ta ga waye wannan baza tayi nisa ba.

tsawa taji wata budurwa ta buga mata me suna Hafsy,Hafsy itace budurwa Babba a gidan kuma tana da dan kyau kadan shi yasa Momee tace lallai ta makalewa Ahleef har ya aureta,gashi kuma duk gidan ita ke wulakanta Saudatu fiye da kowa, watarana har marin Saudatu ta taba yi, tafi kowa fitsara,daga ita sai Mubaraq a rashin mutunci,sai kanwarta Zahra sauran suma ba tarbiya amma mutum uku sune kan gaba, Mama kuwa itama haka take har Alhaji Dauda amma bai fiye wulakanci ba shi sai kadan kadan.Hafsy ce ta watsawa Saudatu Harara dalla malama wuce inda kika fito sai sa ido,Mama tace hmm kuma dai kwa fada suka sheke da dariya gaba daya,Saudatu ta riga ta saba kawai sai ta wuce abinta a ranta tace duniya ce, tazo zata wuce ta kofa Zahra ta bangajeta ta wuce abinta.

Yamma 5pm kowanne dake gidan yaci kwalliya yana jiran manyan baki suzo,Hafsy sai kwarkwasa akeyi,5:30pm motoci laba laba Sun kai 6 ne sukayi parking a cikin gidan,Yan mata fa ansha kyau,Guards ne suka fara Budewa Abba ya fito sai Salman da Suhail Sun dau wanka suna zuba Kamshi,Wata rantsatsiyar mota suka sake budewa sai ga Ahleef yaci uwar uban Wanka kamar baza a mutu ba,cikin manyan kaya farar Shadda kal tasha dinki fitted ta samarin Abuja, sai kyalli da sheki yakeyi,Yana uban taku kamar Sarki yana basarwa ga kyau kamar wankin Engine,kamshinsa duk ya cika gidan,yan mata sai leke suke ta Window,Hafsy tace wai...wai... Zahra na riga ki wannan me farar shaddar nake so,Zahra ta hayayyako da masifa wlh na rigaki shine nawa,ai wlh baki Isa ba,Babba sai babba,yaro kuwa na yaro ne, Jamila wacce suke kira Jamcy itama tace Ahleef take so suna leke ta window,Nan fa fada ya kaure a tsakaninsu sai da Mama ta raba su da kyar, Mama tace ku nuna min akan Wanda kuke fada naga kyan nasa da kuke fada,Zahra tace leka ki gani Mama gashi can da Farar Shadda tunda muke bamu taba ganin me kyau irinsa ba a duniya,Mama ta leka nan take ta hangame baki tare da cewa ina ma ana tariyo baya nima na dawo yarinya Akan wannan wlh sai nayi kisan kai,Dama sun San Mama akwai budurwar zuciya duk harkar charting baya wuceta,Mama ta wuce tace na tafi tarbar baki anjima kuzo ku gaisheshi.

Alhaji Dauda yana tare dasu a katafaren Palonsa suna ta Hira daga nan suka fada harkar Business,Mama ce itama ansha wanka taje suka gaisa taci kitson attach kamar arniya tana zaune a palon kusa da mijinta,bayan 30mt sai ga su Hafsy suna ta layin gaishesu suna karairaya,daga nan Mama tace suzo aci abinci,Ahleef kawai waya yake dannawa Ko kallo basu isheshi ba,babu wacce ya amsawa gaisuwa sai Mama kawai,su Salman kuwa harkar gabansu sukeyi suma,Jikin yan matan yayi sanyi amma basu hakura ba.
Bayan nan Ahaji Dauda yasa aka kawo musu abinci a nan Palon ba sai anje Dining ba,duk Sun zagaye ciki harda Zahra da Hafsy, Mubaraq yana ciki sai Mama da Jamcy.
Yan aiki aka bawa Umarnin kawo abinci ciki harda Saudatu sabo sunfi yarda da tsabtarta,Saudatu ta kawo katon Flask ta ajiye a saitin Ahleef cikin Nutsuwa tana Tsoro karta yi ba dai dai ba, tsaki Hafsy taja tare da cewa dan Allah madam ki ajiye ki tafi ke kullum baki San aikinki ba,Zahra ta kara Jan dogon tsaki uwar kinibibi tsohuwa dake,Mama maimakon tayi fada sai tace hmm Saudatu kenan Uwar Iya,Alhaji Dauda ne yace ku fa bakwa kyautawa Allah kyauta abinda yace kenan,Mubaraq ya shekawa Saudatu harara.
Abba dama shi ya dade da sanin gidan abokinsa ba tarbiya baiyi mamaki ba, yana Allah wadai da halayensu,Salman suma mamaki ya kamasu dattijuwa kamar wannan ana zaginta,Ahleef kam da sauri ya kalli matar da akayiwa tsaki dattijuwa sosai irin wannan ita kuwa ta bar aikin mana idan ba son kudi ba, ana zaginka kana zaune,Su Hafsy yaji ya kara tsanarsu yanzu sosai,Saudatu ya gani ta kawo wasu cups,Mama ta daka mata tsawa zubawa baki abinci mana,su duk ganinsu birgewa sukeyi su masu kudi.
Chapter 12 · 0% Book details