← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 59

Sashe 41

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana tafiya ta kwanta a saman bed din tana zuba Murmushi tana tuno irin dadin da suka jiyar da juna,da kuma nuna Mata so da yayi zalla..tana kwance taji kamshinsa ya fito daure da guntun wani towel fari da Dan karami Yana tsane jikinsa,Ido suka hada ai da sauri ta kulle idonta tare da fadawa toilet cike da kunya,shi dariya ma ta bashi lokacin da suke romancing Sam dadi ya Hana taji kunyar sosai ta zage Amma sai yanzu take Jin kunyarsa

Kafin ta fito ya shirya tare da gyara bed din neat,da kyar ta daure ta iya shirya kanta a dakin sabo da kunya,sai da ta Gama sannan ta haura saman bed din kusa dashi tana kunya ya kashe musu light, jinka ya shigar da ita a kunnenta ya Rada Mata Unique u are so sweet,mun godewa Allah da ya halatta aure,da ba'a halatta Mana aure ba ya zamuyi kenan? Dariya kadan Shukura tayi kana tace hmm ai ko ba a Halatta ba sai anyi aure,akeyin Zina ma,ko ba aure da aka Halatta yin abinmu zamuyi mu Dan Adam,Dariya yayi ke Baby, itama dariya tayi tace Ana Jin wannan dadin za ace baza ayi aure ba ai mutane yin abinsu zasuyi, Boobs dinta ya shafa wannan sun Kara girma me kike Basu just 2mnths bamu hadu ba Amma naji sun Kara cikowa,Shuru tayi wai kunya ta kamata,tana jinsa Yana ta faman yi Mata tabe tabe a jiki har bacci yayi gaba dasu.

Washe gari har makara sukayi sai wurin 8am Shukura ce ta fara farkawa cike da farin ciki tare da tsatsan nishadi,yau Allah ya amsa adduarta gata ga mijinta kwance gado daya itakam komai yayi zam zam a hankali ta furta Allah dawwamar damu a Haka har abada.
Fuskarsa ta tsurawa Ido tana kallonsa tana Murmushi tare da yaba halitarsa a zuciyarta, gemunsa ta Dan taba a hankali, ai kamar ta taba wuta Haka ta janye hannunta Dan kar ya farka ya kureta, a ranta tace laushi da santsin gashinsa yafi nawa,tana wannan tunanin ya farka a hankali ya bude idonsa kyawawa masu matukar haske, Ido suka hada sai tayi sauri ta boye fuskarta kan pillow,Dariya ma ta bashi ya danyi Murmushi kana ya mike Yana cewa munfa makara bamuyi sallah ba ki tashi, kanta ta Kara cusawa cikin pillow tace kaje in ka fito zanyi ni., Hmm ya furta Yana Murmushinsa me sumar da yan Mata ya shiga toilet.

Ya dauki lokaci me Dan tsawo kafin ya fito daure da towel yana goge ruwan jikinsa,yanda Ya bar Shukura haka ya dawo ya iske ta, yau fa zan maida ke schl ki tashi ki shirya, da sauri ta mike zaune tace idan Su Niima suka ganni fa?suje su fadawa Momee tasa ayi min wani abu ta Karasa cikin Shagwabarta data Saba, ido ya zuba Mata yanda tayi wani kyau kamar kar ya daina kallonta da kyar ya saita kansa sannan yace ke dai bakya son schl tuntuni so kike ki zauna a Haka? Baza kiyi ilmi ki waye ba? Kana so ka fada min ban waye ba kenan? Yanda tayi tambayar zai nuna Lallai taji zafin kalamansa,yasan Saurin zuciyarta sai yace ba Haka nake nufi ba, I mean ki Kara ilmi kan Wanda kike da shi yanda kike ai anga wayayya ta karshe.

Murmushi tayi me kayatarwa ta mike tare da shiga toilet tayi wanka,brush da Alwala,ko da ta fito iskeshi tayi saman Sallaya ya idar da sallah Yana Azkhar, da sauri ta Sa jallabiyarsa da Hijab tayi sallah tare da adduointa bayan ta idar ta mike kawai ta fada saman bed din sabo da bacci ne ya cika Mata Ido, Ahleef Yana karatun Qurani sai da ya Gama sannan ya zare kayan jikinsa daga shi sai boxers ya haura saman bed din Nan ya iske har tayi bacci abinta, jallabiyar dake jikinta ya lallaba a hankali ya zare Mata daga ita sai pant ya lullubesu da bargonsu me laushi suka ci gaba da baccinsu Manne da juna kamshinsu ya mamaye su suna Shaka cike da kwanciyar hankali tare da Shauki.

Basu tashi ba sai misalin karfe 11am,wanka kowannensu yayi,creazy Jean fari yasa tare da t-shirt purpple ba karamin kyau yayi ba karshe,Yana fesa turarukansa masu Dan Karan dadin kamshi Shukura ta fito daga wanka daure da towel guntu,wani kuma ta daure gashinta dashi tana tsane ruwan, ta Mudubi suka hada Ido tare da sakarwa juna Murmushi me tsada, sai kunya take ji da kyar ta iya Shafa Mai a hakan ma sai da ta rufe jikinta da bargo, da kansa ya duba kayan tsarabarta ya zabo Mata wata fitted gown Ready made Golden color me dogon hannu,tayi matukar kyau a ciki kamar a sace Shukura,Ita kanta tayi mamaki, a Mirror ta kalli kanta tace Yaya ban taba sanin Ina da kyau ba sai yau, dariya yayi yace to ai ba a yabon Kai,Ni ya dace na yaba,Dole ne na yabi kaina kuma na godewa Allah cewar Shukura tana dariya.

Gashinta ta gyara sosai sai sheki da kamshi yake fitarwa,Wata top ya dauko Mata black me budadden gaba adon Gold da baki ta daura saman rigar tsayinta ya Kai gwiwa wata pencil ce sai ta fito kamar wata sarauniya, gashinta tayiwa acuci sannan ta Yana siriri gyale black, takalminta Black me Dan tudu tare da tsadarjiyar bag dinta du black.
Powder kawai ta shafa da Vaseline a lips dinta.
Ahleef ne ya tako har gabanta ta baya ya rungomota jikinsa ya Rada Mata a kunnenta kinyi kyau Baby, Amma Ni Ina son Jambaki ki shafa kadan, cike da Shagwaba tace ai sai naci abinci zan shafa,kafada ya makale kamar yaro Shima da Shagwaba yace uhm...uhmm nidai a shafa min yanzu idan ya goge a kara mene amfanin kayan kwalliyar Dana yi dakonsa zuwa kasar Nan, a hankali ta zare jikinta ta juya suna facing juna,rungumeshi tayi tare da kwantar da kanta a saman kirjinsa sannan ta Mika Masa Jambaki Red ta furta shafa min.

a hankali Yana wani Murmushi me kayatarwa ya dago da kanta da hannu biyu tare da shafa Mata kadan Yana kare Mata kallo ji yake kamar ya lashe ta ya huta, knocking suka ji,ya Dan bude kofar kadan ya karbi abincin da yayi Order, Zama yayi tare da jawota jikinsa ya fara ciyar da ita Shima Yana ci har suka Gama cike da shauki, shiri suka Kara yi sun dau kyau ya rike hannunta suka fito, dalleliyar sabuwar motarsa Tasha wanki tana kyalli ya fara bude Mata ta shiga Shima ya shiga yaja su suka tafi.

Momee rike da waya hannunta tana faman Kiran number Ahleef ta kasar waje Amma sai wani bature ya daga Wanda kuma ba turanci yakeyi ba wani yare yake faman shekowa a cikin wayar, idan zata Kira sau Dubu yaren Nan take ji, Niima ta matso kusa da Momee tana har yanzu Baki samu Ya Ahleef din ba? Momee tace hmm Na rasa me ya sameshi yau kwana biyu kenan wannan yaren nake ji Haka suka yini suna gwadawa Amma sai yare.
Yau da Safe Latifa ta fito cikin Shirin schl sai tace Anty Niima ki saukeni a schl pls Driver yaje kauye kuma Ina da Test, Niima tace da zamu fita Hafcy da Zahra kanwarta muna da wani Uzuri Amma muje sai mu saukeki.

Hafcy da Zahra Driver ya saukesu gidan su Niima suka shiga motar Niima gaba dayansu suka tafi Zasu fara sauke Latifa, Sunyi Parking kenan Dalleliyar motar Ahleef da Basu San da ita ba tayi parking, yasha kana Nan Kaya harda pcap,Shukura kuma sanye cikin Ready made dinta tasha kyau kamar Queen,Ahleef da kansa ya bude Mata ta fito,Allah yasa su Niima Basu ga fuskarsa ba, shi kuma ya gansu Yana sani yayi yanda baza su ganshi ba,Shukura ma ta gansu Sarai ta fito,Hafcy tace Kai kun gani kamar Ahleef da Shukura,Zahra tace ke Ahleef Yana turai fa Farhan ne kin San fa rannan yaje kauyen shine ya dauko shegiya,tabe Baki Niima tayi tare da furta dama kunsan suna yanayi da Ahleef,Da alama Amanarsa yake ci suna iskancinsu shi kuma yana waje,,Ihu Latifa ta kurma tace wlh Farhan ne suke iskancinsu kalli ya rungumeta suna ta yiwa juna Rada.

Salati Zahra ta saki tare da cewa kunga suna ta kiss ko kunya Yana cin Amanar abokinsa,Niima tace Alhmdllh mun samu hanyar da Ahleef zai Mata saki uku ba tare da wahala ba,Nan take Niima ta dakko waya ta danno Camera ta fito daga motar cikin sanda ta bayan motar take ta faman kyasta Shukura da Ahleef suna rungume rungume sannan suka shige schl din hannunsu cikin na juna,Hafcy harda daukan Video.maimakon su bisu su tabbatar da gaskiya sai suka tsaya jiransu a waje,Shukura sai dariya takeyi ta kalli Ahleef tace wai Nan fa du sharri za a Kulla min,shi yasa na hugging naka da hujja suji dadin dauka,Tabe Baki Ahleef yayi kana yace Basu da aikin yi ne.

Suna jira har suka fito Ahleef ya Kara boye fuskarsa cikin pcap ya dukar da Kai suka koma mota ba tare da sun gane ba Farhan bane,yaja mota suka bar wajen yana tafiya suka turawa Ahleef ta WhatsApp dinsa sannan suka ajiye Latifa suka bar wajen cike da farin ciki harda Kure vol na radio suna Jin kida, Niima tace mu bisu muga inane masaukinsu,Nan fa ta rike wuta tana ta faman Bin bayan motar su Ahleef sai sunga Ina Farhan zai Kai Shukura,Suna ganin Hotel din suka kaure da shewa sannan suka juya kan motarsu suka nufi inda zasu,Ahleef da Shukura kuwa suna kallonsu abin ya Basu dariya.

Room dinsu suka shiga Shukura sai dariya take ta kasa tsayawa,Rungumeta taji Ahleef yayi ta baya ya shigar da ita jikinsa gaba daya Yana sinsinar wuyanta, Mood dinsa ya fara canjawa yaja ta saman Bed suka fada.

AsmaBaffa

Kuyi Hakuri fans wannan Typing din ina busy ne sosai shi yasa bakwa samu yanda ya dace,kuyi min afwa sannan bakwa min Sharhi bare naji dadin typing kawai Ina yi ne ba dadi.
[7/22, 1:14 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO

51-56

Official

By
Asmabaffa

Gaskiya Kuna birgeni masu Sharhi.

JIDDER ZARIA ga page naki.
Chapter 41 · 0% Book details