← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 59

Sashe 19

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari da safe Sunday Ahleef yana gida,Shukura taki yarda ta fito karma ya ganta wai kunya take ji akan maganar Aure da yayi mata tun jiya,tana so ta fito amma ta kasa gashi yana Palon,Leko da kanta takeyi sai ta koma da sauri tana yarfe hannu ita ya za ayi yau ta kalli Ahleef, yau ji take baza ta iya yini a gidan ba, gwara ta fice yawonta har sai dare ta dawo, fuskarta ta rufe da gyale yana Palon sai gani yayi Shukura ta fice da gudu tayi waje,ya tsorata domin kamar wacce Aljanu suka tasar mata,tana fita kamar yanda take yawonta da haka ta dinga yawo a kafa tana hutawa har Dare yayi,ta dauki hanyar komawa,tana kusa da layin sai ga Farhan ya shararo motarsa zaije wajen Ahleef, kallo daya yayi mata ya gane itace,slow yayi tare da sauke glass ya danna mata Horn ta juyo,sai da ta kalleshi ta gane kuwa shine kawai sai ta rufe fuska, yace tazo ta shiga mota taki yarda sai ma sauri data kara tana tafiya yana binta a mota,babu rokon da baiyi mata ba amma taki shiga sai da kyar ya samu ta Shiga, Ahleef kuma yana gida hankalinsa ya tashi yaga tun safe ta fice da gudu kuma har dare babu labarinta karfa Ko wani abu ya sameta,yana samansa jikin window kawai compound yake kallo, Farhan aka budewa gate ya shararo motarsa ciki,Shukura ya fara gani ta fito daga motar, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fito zai tarbi abokinsa, Ahleef yasan dole a hanya Farhan zai hadu da Shukura,Farhan kuma abinda yasa ya nace sai ya dauki Shukura Sabo da ya batawa Ahleef rai dole sai ya gano gaskiyar Ahleef ko son Shukura yakeyi yasan halinsa da zurfin ciki,cike da kunya ta shigo Farhan yana gabanta kamar Saurayi da budurwa, Shakura da Ahleef suka hada ido dake Ahleef maye ne da ido ya mata magana ina taje dake itama yar duniyace ba wuya ta gane sai ta mayar masa da ido Cikin kankanin lokaci,Farhan bai san me akeyi ba,bai taba tunanin zasuyi haka ba da idonsu zai kalla, sai yaga kawai Shukura ta wuce abinta,Farhan ne ya dameshi shi ya bashi abinci yunwa yake ji,so yake wai yaga Ko Shukura ke masa girki, idan itace yasan dole zai sata tayi yau fa sai ya kuresu,Ahleef yace sai dai kasan kaci Indomie,to kasa Babyna tayi mana me dadi mana, Ahleef dariya yake a ransa Sabo da ya harbo jirgin Farhan,Sai ya shiga kitchen da kansa ya iske Shukura ciki tana dafawa kanta abinci wai tuwo zatayi miyar taushe,Ta yanka kabewa kawai ta cika tukunya da ita ruwan cikin katuwar tukunya har baki, har tayi hadinta gaba daya komai ta zuba har Allayyahu du a ciki kuma tukunyar ko tafasa batayi ba, Gashi sai yanzu ma ake gyara nama za a zuba, naman ne karshe,Ahleef kallonta kawai yakeyi duk tayi kaca kaca da kitchen din,ko ina kwanikan aikinta ne ake ta yi,duk ta firgita kanta Bata gane me Ahleef yakeyi ta cikinta takeyi tun safe Bata ci komai ba, Ahleef gefe guda yake nasa,duk kamshin jikinsa ya kara gigita Shukura,Tukunyarta katuwa data dora ya bude kamar Wanda yaji kamshi ya wani lumshe ido tare da cewa uhmmmm... Kaji irin na manyan mata,mata fa suna girki anan yanzu naga girki anan Amma dai za a sammana wannan kamshi haka,Dadi Shukura taji an yabi girkinta ta Washe dan bakinta tace zan San muku ka daina budewa kar miyar ta lalace,Dariya ta cikawa Ahleef ciki,yace lallai zaiyi dadi kam ayi sauri a gama muna jira,me kake dafawa kai? Yace uhmm Indomie da kwai zamu ci kafin ki gama naki,kawai sai yaga ta kashe gas tace ni bana son girkina naku zanci ga me kwai ai yafi dadi wa zai hada abinda aka dafa da kwai da kuma tuwo,Ahleef yace sai kin mana tuwon sannan ki San mana nima na baki namu,baki ta turo tana kunkuni ta kunna gas taci gaba da girki,kawo na tayaki nima sai na koya Ko,tace to zo ka tayani wanke kwanikan nan,suka fara wanke wanke Shima ya fuskanci Bata iya sosai ba, sai labari ta fara bashi,Sai ga Farhan ya shigo shima ganin kwakwaf,Shukura ta fara labarinta tace Sanda Inna da Baffa suna da rai ko, Farhan yace uhmm muna ji,tace kai baka tsayawa kaji lbr sai surutu ka bari mana kaji abin tausayi sai kayi kuka,Inna ce dai Inna ce watarana da karanbaninta wai ta danawa bera tarko a karkashin gado zata kamashi Sabo da yana dauke mata soyayyen namanta, kwana daya biyu ta manta ashe tasawa bera tarko sai ta tura hannunta kasan gado wai zata ebo naman sai tarko ya saki ji kake bas ya danewa Inna Hannu ya kamota, ta fito dashi...tun wajen Suka fara tuntsira dariya Bama kamar Farhan,tace wai ku ance ku tsaya mana kuji to,Ahleef yana dariya yace muna ji, taci Gaba Inna dai da tarkonta a hannu ta kasa cirewa gashi ni na tafi yawo na,Baffa kuma yana kiwo gashi ba mayafi a jikinta baza ta iya fita haka ba,sai ta tsaya jikin katanga ta fara kwalawa mutane kira babu Wanda yaji dama muryarta kamar ta tsuntsu haka take idan tana magana Volume baya daduwa baya raguwa,kuma wai sai dai tace mutane...mutane kuzo baza tace jama'a a taimaka ba,Baffa ne ya shigo ya Cire mata Allah sarki hannunta ya kumbura Inna babba ce fa amma ta kama kuka,kaiiiii ta bani tausayi, Farhan suka dinga dariya,karshe ya tabe baki yace to shine me ? Shike nan labarin ? Ahleef yace kai amma akwai tausayi gaskiya,Allah sarki Inna,Shukura tace Kaji me Imani amma banda kai ta nuna Farhan Wanda ya fice daga kitchen,Tukunyarta har yau Bata tafasa ba, Amma ta bude sai juyawa take tana dandanawa,Ahleef yace muna jira fa, zuciya tayi wai tukunyar ta bata haushi akan me Bata tafasa ba, shine ta kwala murfin da kasa tace na gaji wlh ni bazanyi ba, Kin girma da iyayenki me yasa du baki iya girki ba,gyaran gida kawai kika iya taya zaki rike mijinki idan kinyi aure,kicin kicin tayi da fuska tace kai in dai ba me kiba bane tsab zan iya rikeshi wlh ina da karfi fa kalli damtse na ta dago hannu, Ahleef ya dinga dariya,tace yar gata ce ni fa a gida bana komai ko zanyi Iyayena hanawa sukeyi,gyaran gida nafi iyawa Sabo da kullum idan Bata nan inayi,Kai ya jinjina tare da cewa to gashi yanzu Sun rasu Sun barki ya za ayi ke nan, to ba sai ka koyamin ba tunda ka iya, Bani da time ni kinma kusa bar min gida kiyi shiri Next wk,gabanta ne ya fadi tace dan Allah kayi hakuri ka kara min ko wata goma ne ina yin kudi zan tafi kuma na kusa saura kadan.

Indomie ya juye a plate Uku kowanne da kwai biyu ciki dafaffe,plate guda ya mika mata,ya dauki nasa dana Farhan yayi waje,a kitchen din ta cinye nata sannan ta gyara kitchen din tas ta zubar da miyarta da takeyi ta wanke tukunyar sannan ta wuce palon wajen su Ahleef, Inner wears ta gani sababbi latest an kawo na maza da yawan gaske Ahleef ya zaba Farhan ma ya kwashi nasa,Shukura ta koma kusa da Ahleef ta zauna tana ta kallon kayan, Farhan yana kallonsu yanda Ahleef ya Bata rai sosai dan kar ma Shukura tace zata taba kayan,mikewa Farhan yayi tare da cewa saida safe ya,ka fasa kwanan ? Ahleef ya tambaya,Ae Bazan kwana ba a cika min ciki da Indomie Budurwata sai da safe,Shukura Kunya ta rufeta da kyar tace Allah tashe mu lfy,Ka gaida Mama zan shugo gobe cewar Ahleef.
Shukura ta kalli Ahleef a hankali tace tace Dan Allah bani guda biyu ina so Harara ya watsa mata,bata kara cewa komai ba ta Mike tayi Dakinta.
Chapter 19 · 0% Book details