← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 59

Sashe 22

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunanin yan class Shukura Bata da wani kokari tunda sunji kalar turancinta duk kyanta sai suka rainata,Period din Malama ta kare wani malamin Biology ya shigo,ya fara yiwa yan aji tambayoyi what is kaza what is kaza etc,yana yin tambayar farko ba Wanda ya daga hannu sai Shukura,shi kanshi ya girgiza da kyanta yace ta fada,ta Mike ta bada amsa dai dai kuma kawai turancinne idan anji an San Bata kware ba, Malamin yasa aka dinga tafa mata,ya kuma jefo ta biyu Shukura ta kara daga hannu tare da wasu yan aji ya kara nunata ta fada nan ma ta bada amsa dai dai Kafin ya bar ajin saida ta amsa questions hudu.
Wani ma ya shigo haka ta dinga kokari gaba daya sai gashi ta kankaro mutuncinta kowa yasan me kokari ce sai ga students mata da maza Sun fara mata magana dake ita Shukura zai wahala kaga tayi fushi ko ta Bata rai haka suka dan saba kadan ta saki jiki sama sama.
2pm suka tashi ta fito bakin Gate,Drivern Ahleef ta gani Yana jiranta ta shiga suka tafi gida,Yau ma tare da Umma sukayi abincin dare suka gama komai.

Washe Gari Driver ne zai kaita amma tace ita da kafa zata je,ta fito kenan Latifa ma ta fito Sabo da Niima ta bawa Latifa labarin cewa an kawo wata yarinya gidansu Bata da kunya an sata a schl ma Sabo da haka Zata yi mata transfer zuwa makarantar su Shukura domin hana Shukura karatu da Jin dadin schl baki daya,Sannan Niima ce zata dinga shirya komai yanda zai tafi dai dai,Niima tace Latifa ta shirya yau ita Zata fara kaita schl ma, Latifa da bata yarda zatayi ba Sabo da bata San wace ba, Sun fito Compound tayi arba da Shukura ta ganeta sai ta bawa Niima Labarin fadansu da Shukura a motar Ahleef sannan tace Alhmdllh dama na tsaneta tunda itace wlh sai inda karfina na ya kare sai karatu ya gagareta, Niima taji dadi suka tafi a mota,Shukura tana kallonsu ta fice ta tafi a kafa tana ta bata lokaci har first period Zata fita sannan taje schl.

Tana zuwa gate taga Niima tare da wasu malamai da kuma seniors baki daya tana fada musu cewar Shukura kanwarta ce,bata son karatu ne shi yasa aka yi mata Transfer zuwa wannan makaranta Sabo da Sun iya ladabtar da Soudent,kuma a kula Shukura barauniya ce,sannan tana zagin iyayenta kar a raga mata a schl din Sun kawota ne domin a hukuntata idan tayi laifi, PC yace ai yayanku ne ya kawota kuma baice musu haka ba, Niima ta zaro takarda ta mika masa tace gashi babansu su ne ya bayar a kawo kan halayen Shukura yana so schl su tayashi tarbiyantar da ita,pc ya karba kuma ya gamsu haka sauran malamai ma, ta kara miko takarda tace inji yayansu Ahleef yana bada Umarnin hukunta Shukura idan tayi laifi dama haka take ta damesu a gida Bata ji,karshe ta zaro kudi masu yawan gaske ta bawa malamai har senior student,kudin da ta bawa PC na daban ne nan Take suka gigice suna godewa Niima ta juya ta shige motarta ta bar schl din.

Lokacin kuma Shukura ta shigo gate din PC yace lallai gaskiya ne ga zahiri dan Iskanci tana New student sai yanzu Zata zo schl period daya ta fita salon ta lalata musu schl, to baza su yarda ba wlh dole su dauki mataki ba ruwansu da New student ce,Bulala PC yace a kawo masa,yace Shukura tayi kamun kunne,tun kafin tayi ta fara Kuka,haka ya sata kamun kunne, tsallen kwado sannan ya sa wasu malamai biyu suka zanewa Shukura jiki sai da suka fasa mata fata jikinta yayi rudu rudu,An daki sarkin Shagwaba,su kansu malaman sai da suka ce basu taba ganin yar shagwaba irinta ba daru take iri iri ana kallonta,idonta yayi jajir Sabo da kuka haka ta Shiga Class,tasan dama tunda taga Latifa tare da Niima a schl din dole tasan sai wani abu ya sameta.

Bayan anyi musu Break Latifa Har tayi frnds masu kudi yan wulakanci ta sanar musu Shukura yar aikin gidansu ce daga kauye aka kawo ta gashi kuma su a Ss2 suke seniors ne,Shukura tana gaban me Yogourt ta karba ta bar wajen taji kawai an shako Hijab dinta ta baya sai da ya yage ta wuyanta kafin tace komai wata ta fisge yogourt din me kankara,Ido Hudu sukayi da Latifa,Shukura a ranta tace bashi kika ci,Tana kallonsu wajen su Shidda suka dinga dungure mata kai suna mata dariya tare da wulakanci iri iri Student suna ta kallo masu dariya na yi masu Tausayin Shukura suna ji,Shukura kuwa Sun mata yawa mukus tayi kanta a kasa har suka gama suka tafi sannan taja kafarta da take dingisawa da kyar Sabo da tsallen kwadon da tayi ya tashi Tsohon rauninta da Igbo Man Wanda ya taba bige ta a mota ya ja mata. Motocin Ahleef ne suka keto cikin Schl din tare da Escorts Latifa ya fara hangowa cikin kawayenta marasa kunya,kallo ya koma kansa Gaba daya,Fitowa yayi cikin shiga ta Alfarma duk Wanda ya kalli Ahleef sai yasan lallai Allah Sarki daya ne,yan mata ko kyafta ido basa yi kansa,Latifa ta fara iyayi ga yayanta suka rankaya zasu kwasar gaisuwa,Ahleef da mamaki yace ke kuma me ya dawo dake wannan schl din ? Ko iyayin ne ya motsa ? Latifa tace nafi sonta Yaya,baki ya tabe tare da cewa taki schl din tafi wannan komai fa,anyway je ki Ss1 ki kira min Shukura,Munafuka Latifa sai ta nuna Sam Bata gane wa yake nufi ba sai da ya mata kwatance sannan wata ciki tace ta gane ta suka tafi jiki na rawa suka samu Shukura ta kwanta saman Sit tana tunani iri iri,Duka Latifa ta dada mata a cinya tare da cewa kije inji Wanda ya kawoki nan,tasan Wa take nufi,ta dauki jakarta suka fisge tare da zazzage komai na ciki a kasa sukayi tafiyarsu,Shukura abar tausayi ta sunkuya tare da kwashe komai ta mayar cikin bag sannan ta fita tana dingishi amma a ranta Dadi take ji na zuwan Ahleef Sabo da yanzu ganinsa takeyi kamar dan uwanta na jini.

Yana cikin mota yana shan AC ya hangota a birkice idonta Jajir kuma ba fara ar daya saba gani a fuskarta,sannan Uniform dinta duk sunyi Dirty bayan ya santa da tsabta.
karasowa tayi jikin motar daya ke ciki ana ta kallonsu,Murmushin dole tayi ta leka kanta ta Glass din tare da cewa Sannu da Zuwa Yaya,ba tare da ya kalleta ba yana latsa wayarsa cikin iyayinsa tare da murya me dadin sauraro yace me ya samu kafarki ? Kuka kikayi ? Uniform kuma sunyi Dirty,gefen yatsanki kamar shatin bulala,Rau rau tayi Zata fara kuka da kyar ta danne tace ba komai dazu ne aka ce yan class sunyi laifi shine aka zane mu duka tare da tsallen kwado,Kuka ta fashe masa dashi tace shi yasa nace ma wlh bana son yan birni mugaye ne saura kadan su kasheni dazu Allah ne ya kiyaye malaikan daukan rai bai karaso ba, dan Allah Sir bana son karatun ni na hakura wlh.
Ba kya son zama likita ko Lawyer,teacher etc ? Shuru tayi tace ni Soja nake son zama Sabo da na rama dukan da aka yi min yau ko Roadsafety wlh duk sai na kama motocin Malaman nan da sauran duk Wanda ya Bata min,Murmushi yayi tare da mika mata Wata ledar abinci da ya yi mata take away yace jeki to class,Murna ta lullubeta wannan kadai ya yaye mata bakin cikinta,godiya tayi tana murmushi, ko kallonta baiyi ba yace Farhan ne saurayinki yace a kawo miki, Allah sarki kayi Masa godiya ko ka bani number dinsa kawai pls? Zai baki da kansa nan gaba tafi class bye suka ja motocinsa, Class taje ta baje abinta kowa na kallo babu Wanda ta kula tunda Bata da kawaye haka ta cinye Namanta da sauran tarkacen ciye ciye dana sha,Students ana ta hadiyar yawu.

Bayan 1wk kuwa Latifa lallabawa tayi ajin su Shukura lokacin ta fita anyi Break ta Saci Dubu biyar wata a cikin jaka ta zuge bag din Shukura ta saka mata dubu biyar inda baza ta gani ba ta bar class din.
Bayan an dawo daga Break yarinya ta nemi dubu biyar finta ta rasa kuma aikenta akayi a gidansu after schl Zata kaiwa telansu,ta sanar a class duk Wanda ya dauki kudinta ya dawo mata Dashi class kowa yace bai dauka ba,aka ce ayi caje aka fara caje jiki da jaka a gaban Malamin da ya shigo shima yana taimakawa,sai aka samo dubu biyar cas a jakar Shukura aka fara ihu Thief...Thief.... aka fito da Shukura Waje Malamin yayi mata bulala goma yace dama yayarta tace barauniya ce ita haka a gida ma take sace kudin iyayenta,Hakan ma wai ya raga mata Sabo da New Student ce,Shukura Bata saba ba ta barke da kuka tana cewa wlh Sharri aka yi mata amma ba wanda ya saurareta sai ma dariya da yan Class suke mata,ita kanta Bata San waye ya kulla mata sharri haka ba, amma ta barwa Allah, Tun daga wannan rana Shukura ta daina zuwa late,ta fara taka tsan tsan da jakarta Sabo da kar a kuma kala mata sharri,bata kula kowa daga mata har maza Bata kulasu Sabo da Sun Bata Haushi da suka kala mata sata,duk Wasu doka na schl ta kiyayesu sai wani Masifar kokari da take tashen yi ba a magana turancinta kullum gyaruwa yakeyi ga kyau ga diri data kara.
Chapter 22 · 0% Book details