← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 59

Sashe 50

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momee dake saman Bed ta zuro hannu ta zubawa Niima rankwashi tare da cewa ke dai kika cuci kanki marar mutunci ,Latifa ce ta shugo ta dawo daga yawonta ta iske su Niima da Momee kowannensu Yana Hawaye cike da Nadama,Itama tsugunawa tayi a wajen ta fara kalar nata kukan tace Momee kece du kika jawo Mana,Momee tace Dan ubanki wacce tarbiya ce ban baku ba? Ai sai daga baya shedan ya rudeni na canja hali akan son duniya,yanzu sai mu fara istigifari ko Allah ya taimakemu,su Momee yau sunyi Nadama,sunji karatun Duniya Dole uwar naki,Nan take suka fara istigifari suna tuba,Baji ba gani,Niima tace sai mu nemi Ahleef ya yafe Mana,Latifa tace shegiya bariki gashi da kaina naji wahala na tuba,Allah dai ya karbi tubanmu,Shukura ma munyi Mata kazafi,Momee kinyi silar lalacewar dubban alumma shi yasa Allah ya Rama musu akan yaranki,nayi shaye shaye da duniyanci Ina karamata,ga Niima itama an Rama akanta tayi ciki,da Baki sa an lalata yaran wasu ba wlh da muma Allah bazai Bari mu lalace ba,ga kudin gado duk ya Kare yanzu ko kin warke bamu San ya zamu Kare da talauci ba, naje Neman Ahleef wajen Farhan yace ai Ahleef yayi kudin da yafi na da,Kuma ya dauki Matarsa sun koma London,Haka Su Umma Saudatu basa kasar,nayi nayi ya bani number din Ahleef wlh yaki bani..yanzu Kuma talauci ne kawai zamu karba a jikinmu matukar Ahleef Bai zo ba, Niima da sauri tace wlh rannan a tv Naga Ana nuna shi tare da Shukura Kinga yanda suka dawo kuwa kamar turawa nayiwa kaina nayi asara,duk nice na dinga zuga Umma har na cusa Mata kiyayyar Ahleef,gashi mun kwace dukiyar da take halak dinsa har mukace ya daina zuwa gidanmu,gashi Allah yayoshi ba talaka ba ya sake yin new Money.

Momee tace to a Ina ya samu kudin da zai juya? Latifa tace hanyar Allah ko Kuma Farhan ne,Niima tace Allah ya nuna Mana Ahleef na bashi hakuri sannan Kuma na Masa tayin kaina ko zai aureni,wlh sai yanzu naji sonsa Yana ratsani,Dan Allah Momee idan ya dawo ki nemi Alfarma ko zai aureni Bayan na haihu ya Kara ta biyu Dani,kin San Yana jin kunyarki Kuma Yana sonki,baya manta alkhairi idan kin Sa Baki da wuri zai aureni.
Momee tace Allah yasa zanfi kowa farin ciki.
Latifa tace Ni Kuma Farhan nake so Momee,Momee tayi Dan Murmushi tace Allah nuna Mana zan nema muku Alfarma.

Latifa da Niima su sukaci gaba da kula da Momee da Dan ragowar kudin da ya rage musu,har aka samu akayiwa Momee aiki aka cire Mata Koda daya data lalace sannan ta samu sauki sosai sun Dade a asibiti har ta warke sannan aka sallamesu ammafa kudinsu sun Kare karaf sabo da Mubaraq ya Gama kwashe komai ya bar kasar abinsa ba a San inda yake ba.

Mama dasu Hafcy ma kansu Mubaraq ya gujesu Basu San inda yake ba,duk murnar da suke zasu Shana da kudi a banza domin ya gujesu,Alhj Adamu Bai San komai ba sai aikin neman Mubaraq yake, Mama Sai kuka kullum danta ya bace, Su Hafcy kuwa sai tsinewa Mubaraq sukeyi yayi kudi ya gujesu sun taimaka Masa Amma karshe abinda ya musu kenan, Momee bayan ta warke report ta kaiwa Yan sanda Mubaraq ya gudu da kudinsu,su kansu Yan sanda ganin ba wata sheda kwakwara sannan Momee Basu da kudi sai suka share Zancen kawai suka sallamesu bayan Dan karamin bincike da sukayi.

A kwana a tashi yau abincin da su Momee zasu ci gagararsu yakeyi sun tsiyace sai katon gida ba ko sisi a ciki, Momee tace Dole mu saida wannan gida mu koma cikin talakawa mu siyi karami ko zamu samu na cin abincin,Momee suka daga tallan gida ba Wanda ya Taya,sai Momee ce da kanta taje wajen Farhan kan ya taimakesu ya samo musu Mai siyan gidan,Nan take Farhan ya bugawa Hamshakin me kudi waya ya siyi gidan su Momee suka siyi karami can unguwar talakawa suka zauna,sauran kudin kuma suka siyi kayan abinci etc.

London

Ahleef suna Bedroom dinsu ko hutawa basuyi ba ya cirewa Shukura kayanta tare da nasa suka Shiga wanka, damunta yayi da tabe tabe tare da tsotsar inda yaga dama, ganin ya fara susucewa cike da Shagwaba tace pls ka Bari sai dare Mana kamar zata narke Haka tayi maganar, wani nataccen kallon so yake aika Mata, a hankali ta rungumeshi tana me bashi hakuri sai dare can,kafada ya makale shi bai yarda ba sam,Dole ta hakura taba da amanna suka farantawa juna rai sannan sukayi wanka suka fito da kanta ta shirya sannan ta shirya Ahleef dinta tana Gama taje Masa gashi tace to oya karbo Mana abinci yunwa nake ji, fita yayi Yana tsokanarta Wai ciki gareta tunda yanzu tafi cin abinci.

15mns ya dawo dauke da ledoji Niki Niki,da sauri Shukura tace sannu da zuwa ta karbi kayan tana wani farin ciki kamar yau ta sanshi, abinci ya siyo musu da Kuma kayan sawa hadaddun gaske,Shukura sai Murna takeyi tace Allah ya Kara budi, Ameen yace Yana kashe Mata Ido daya, Hero gaskiya Ni ka daina min irin kallon Nan nafa San me kake nufi, ta furta cikin tsantsar shagwaba, da sangarta tana cuno Masa Dan bakinta,wani birgeshi takeyi idan tana Shagwabarta har cikin jininsa yake Jin wani yarrr..

Murmushi ya saki me kayatarwa kana ya jawota jikinsa ta Fado saman cinyarsa zuwa kirjinsa Fuskarta ta dago tana kallonsa sannan tana Wasa da yatsunsa, Harshensa taji cikin bakinta a nutse Yana tsotsa kamar alawa baya gajiya da Shukuransa,ga Tsafta tana kula da jikinta sosai ko ina kamshi zaka ji,itama a ranta tana mamakin Tsafta da gayu irin na Ahleef kullum neat ko wacce gaba ta jikinsa kamshi take lungu da sako, ci gaba yayi da Shafarta ba tare da Bata lokaci ba Shukura ta rude jikinta Yana rawa daukan ta yayi zuwa saman bed Wasa ya canja salo sai da suka Raya sunna abinsu,Bayan sun samu nutsuwar,Ahleef ya kankameta a jikinsa kamar za a kwace Masa ita ya furta kullum Honey sweet kike karawa, you are too sweet har ban San me zan ce ba, Fuskarta ta fara goga Masa a tasa cikin kunnensa tace Kaine kake bani abinci da yawa Ina cinyewa yanzu zaka kaga na haihu ai ance idan mutum Yana ci Yana koshi ba yunwa a gidan mijinta to yanzu zan ta sullubo yara.

Dariya ta kama Ahleef sosai Yana ta yi Yana Kara kankame Shukuransa yace ai ban sani ba dama haka abin yake? Da sauri Shukura ta ae kwarai to Alhaji gidanka ba yunwa ni Naga na Dade ma kamata yayi ace na haihu tuni,Ahleef ya Kara kyalkyalewa da dariya, fushi tayi ta turo Baki Wai sai dariya kake min na daina kulaka ma sakar min jiki tunda Haka kake,sorry Bae na daina kin kusa Haihuwa saura kadan ai mace kike so ko Namiji? tab me zanyi da Namiji nafi son mace Yar yarinya ta na dinga Mata lalle da kitso,idan ta girma na dinga aikenta,tana min girki da aikin gida, na daka Mata tsawa nace je ki gyara room din Dad Hero Dina,Ahleef Yana dariya kasa kasa yace to Yar taki Zaki cewa Hero dinkin a gabanta ba kunya,Kai nifa ba ruwa na da wata kunya Baturiya ce ni,gidan turawa ne mu ba ruwanmu ko? Ahleef yace gaskiya gidan Yan gayu ma kuwa,Shukura tace da su Momee Basu raba mu ba ai da tuni na haihu,Amma na koma kauye yunwa zata karasani Taya zan haihu da wuri kuwa, Me gari da Matarsa sun Gama azabtar Dani, Wai Ni yake so in baka lbr ya dinga kallona idonsa kamar na aljanu, Ahleef Nan take ya Bata rai, kishinsa ya motsa yace kyale maganar karki jawo nasa a kamo min Me gari na kaishi prison.

Murmushi tayi tare da furta calm down Hero,abinci ya jawo suka ci tare abinsu Yana Bata a Baki da kansa tana ta bashi dariya da hirar kuruciyar ta, Bayan sun Gama, shiri sukayi sun dau wanka kamar baza a mutu ba suka fita yawon zaga gari abinsu gwanin Sha'awa da birgewa.

Ayi min hakuri Fans wannan Novel din bana bada page da wuri wasu Abubuwa ne suka rikeni in busy ne sosai,Dan Allah kuyi min hakuri da afwa da kyar nake samun time na typing.

AsmaBaffa
[7/22, 1:14 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO

71-75

Official

By
AsmaBaffa

Ahleef Yan London sun kwashe 2wks a garin suna zuba amarci kafin suka tafi Russia sun kwashe 1wk sannan suka wuce Saudi nan suka Iske Baba da Umma Sunyi Ibada sosai,sai kyau da haske da suka Kara tare da Yar kiba kowa ya gansu yasan suna Jin dadi,Shukura tana ta siyayya Ahleef Yana kashe Mata kudi sai abinda take so, Bayan sun Gama aikin hajji Su Umma suka dage zuwa Nigeria,Ahleef kuwa Shukura ya dauka suka wuce Dubai abinsu, Baba da Umma suna hutawa suka tafi Niger a jirgi wurin dangin Baba sada zumunci,can ma Sunyi Mamakin ganin Baba,domin tunaninsu baya Raye sai gashi ya kawo Musu ziyara tare da kyautuka na alheri, sunji dadi sannan Ya Basu labari dansa Ahleef, satinsu biyu sannan suka dawo Abuja cike da murnar ganin Yan Uwa.

Bayan 3weaks Su Shukura jirginsu ya sauka a Nigeria,Murna take faman yi zata ga su Umma, escort din Ahleef ne suka dauko su daga Airport zuwa gida, Umma da Baba ma murna suke sosai da dawowar yaran nasu,Shukura jikin Umma ta lafe sun Dade suna Hira har Ahleef tare da cin abincin Umma me Dan Karan dadi sannan suka wuce hadadden part dinsu cike da kaunar juna.
Chapter 50 · 0% Book details