Sashe 10
Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
sai data yi nisa sannan ta samu wata bishiya ta zauna tana hutawa,ko 2mnt batayi ba sai ga wasu mutane Sun koreta wai ba a zama a wajen,Shukura tace da a kauyene wa zai koreka ko a filin tsakar gidan Me unguwa ne sai yanda kaga dama zakayi,a hankali take tafiya ragowar 2k dinta Cikin Wanda Igbo yace nurse ta Bata suka zube a hanya,baya ta koma tana dubawa amma Bata gansu ba gashi kafafunta Sun gaji kawai sai ta fashe da kuka tana ci gaba da tafiya tana goge hawaye tare da cewa na Kawo kaina gashi ni dama ban iya komai ba zuciyata ta gama mutuwa Iyayena gata suka nuna min,ita kadai take maganarta har tazo dai dai inda Haj Saudatu take soya doya da kwanta me dan karen dadi, har ta wuce sai ta dawo Baya ta kafe Saudatu da mugun kallo a fili tace wlh tana kama da dan gidan Gwaggo Momee, Haj Saudatu ta kalli Shukura itama tana murmushi tace yan mata lfy ? Shukura tace wlh Inna kamarku daya da wani dan gayu baki ganshi ba idan kikayi dariya komai naku iri daya ne,Murmushi kawai Saudatu tayi tare da cewa ni kinga bani da yaro a zuci kuma tunanin danta abin sonta ya fado mata,Shukura tace Inna da zaki bani aiki sai na dinga tayaki ina miki wanke wanke kina bani dan Ladan aiki mu daga kauye muka dawo nan Abuja bamu samu aiki ba,Saudatu taji dadi dama tana neman me tayata aikin tana biyan lada, yarinya a ina iyayenki suke,Shukura gani takeyi idan ta fadi gaskiya za a hanata aikin sai tace daga kauyen Jos muke yankin Fulani,muka dawo nan neman aiki iyayena suna can Nyanya a nan Abuja gidanmu yake,Saudatu kuma ta tace muma yan Niger ne a Kaduna muka fara zama, sai muka dawo Abuja,mijina gadi yake a wani gida,nan muke Zaune hakan ma da kyar masu gidan suka barmu muke dan rabawa a gidansu basu da kirki.
Shukura a ranta tana Sa rai ko Saudatu Zata dauketa ta koma gidanta da zama ta samu wajen kwana sai taji Gaba daya ba harka, Shukura cikin karfin hali tace Inna idan zan kawo miki ziyara watarana fa ? Saudatu ta rike baki tare da cewa wuuuu yar nan rufa min asiri ai Ko baki basu bari muyi idan ma zaki zo sai jefi jefi kuma babu dadewa mu gaisa ki tafi gidanku in ba haka ba ki jawo mana masifa,Shukura taji ba wajen zama kawai tana tunani ga dare nayi to ina zata je ta kwana,jiki a sanyaye tace to Inna yaushe zan fara zuwa ina tayaki aikin ? Saudatu tace banda yau tunda kinga na kusa tashi dare yayi ki bari sai gobe kizo,yanzu maza ki tafi gida kar a nemeki,Shukura tace da na tayaki daukan kayan sai na rakaki gida,Saudatu tace na gode Allah miki albarka baza ki jawo min ba yar nan kiyi hakuri dan Allah ki barshi,Shukura Badan taso ba ta juya tana cewa sai goben zanzo, 3pm cewar Saudatu har ta zubawa Shukura doya da yawa a leda ta Bata kyauta.
Shukura ta rasa ina zata je har 8 na dare kawai sai ta tuna da Address din gidan Ahleef Wanda yanzu yafi rayuwa a cikinsa kawai taxi ta shiga ta bashi Address din gidan Ahleef,bayan me taxi ya kaita sai da ta tabbatar da gidan ne sai ta tsaya can farkon layin dan kar a ganta,ta juya wajen me taxi tace ita wlh kudinta Sun fadi yayi hakuri Bata da ko sisi amma yana binta bashi nan da 3days su hadu a wajen Saudatu me doya inda ya daukota,Me taxi ya dinga masifa har ya gaji karshe yace zaizo wajen Sauden nan da 3days din in dai ba a bashi kudinsa ba to wlh Ko Sauden ce kamata zaiyi,Godiya tayiwa Allah sannan ta fara dube dube sai da ta tabbatar ba Wanda ke ganinta sai tayi sauri ta zaga ta bayan katangar Ahleef inda babu security,Dalaf ta kama wata bishiya dake jikin katangar ta dane bishiyar ta gama kwalkoleta sannan ta lallaba ta taka dalaf ta dane saman katangar gidan Ahleef,Tayi sa'a a saitin garden ne sai ta kara tsalle kamar biri ta hau Saman wata bishiyar goba dake cikin garden din Sabo da katangar tayi stayi haurawa sai da dabara,ta kan bishiyar ta dirga a katafaren gidan nasa sannan ta fara tafiya cikin Sanda dan kar a ganta,ta kofar baya tabi sai gata a kitchen ta tura kofar a hankali,ta bi ta wuce ta fito ta wani katafaren palo tana son tayi kallo ba hali,da sauri tabi ta wasu wuraren har ta samu ta ga Steps taga wata Hanya ta kasan Benan da gudu ta shige tabi ta nan sai gata a wani part din guda ba abinda babu,wani katon wuri ta shiga Gaba daya kayan motsa kiki ne, ta wuce sai gata a wani kitchen din ba abinda babu, cikin inda kayan motsa jiki Suke a nan ta samu wani lungu Wanda idan mutum ya shiga ciki babu me iya ganinka a nan ta samu ta shimfida dankwalinta a kasa harda kashe Light ta kwanta sai bacci ya kwasheta.
Shukura Bata iya bacci lfy ba sai tayi birgima da shure shure taji gida me dadi sai juyi take tana bige bige har ta bige wani karfen motsa jiki kadan, Lokacin Ahleef ya dawo yayi shirin bacci cikin Fararen kayan baccinsa tunda ya shigo yau yake Jin kamar ana motsi a gidansa,kamar ba shi kadai bane,idan kuma ya kasa kunne sai yaji shuru,Yana Saman Bed yana latsa system sai yaji kamar abu yayi motsi,tsoro ya kamashi kawai dai ya dan daure ya Mike ya fara lallabawa yana sanda kamar sabon barawo,a haka ya duba ko ina na gidan sai yaga ba kowa,kawai sai yace ko kunne na ne ? Baki ya tabe tare da kashe Light na ko ina ya koma ya kwanta bacci.
Washe gari da safe ta lallaba ta fada wani bedroom wanda yasha kayan alatu masu kyau, Da sauri ta shige toilet din ciki,ta samu sabon brush da toothpaste tayi brush tare da wanka ta daura Alwala ta shirya cikin kayanta tsab sannan ta kara lallabawa ta fito inda take boyewa anan tayi sallar asuba tare da adduointa, sai 10am taji motsin Ahleef ya fito dakin da take zai motsa kiji,kara boyewa tayi sosai tare da leko da kanta tana kallonsa daga shi sai Boxers yana motsa jiki,shiko bai san da mutum ba,Yana ta motsa jiki,itako mamakin kyawu nasa takeyi ga kyan sura kasa dauke ido tayi a kansa kamar zata lasheshi,tana kallo ya hada zufa har ya gama sannan yayi wata mika sosai,Dariya ya Bata yanda yayi mikar saida ta murmusa,tana kallo ya juyo kamar yana facing nata da dan tight boxers din dake jikinsa Kamar tsirara haka yake Sabo da shape din komai ana gani,Shukura ta firgita ganin kato haka Bata San sanda tace kai..tab Amma sautin kadan ya fita baza ka gane maganace ko ba magana bace,a tsorace Ahleef ya fara waige waige yaga ba kowa,tsoro ne ya kamashi ya fita da gudu ya banke kofar,Abin dariya ya bawa Shakura namiji haka amma sai tsoro.
Sai da ya daina Jin tsoron sannan Kitchen dinsa ya shiga domin dafawa kansa Breakfast shi bai son girkin yan aiki,Chips and egg ya hada sai tea daya hada lafiyayye a cup,ya shirya komai a Dining,Shukura yunwa ta addabeta,ga kamshin girkin ya cika mata ciki,tana kallo Ahleef ya tafi bedroom din sa domun shiryawa sannan ya fito ya karya,da sauri ta fito tare da dauke Shayin ta balli Bread,Chips and egg duka ta dauke ta cinye tas da sauri ta ajiye masa empty komai sannan tabi ta inda ta shigo jiya gidan ta kara bi ta sama ta dirga ta waje can tayi sauri ta bar layin,Ahleef ya dau wanka yana zuba kamshi yazo dining ido ya zaro cike da tsoro jikinsa ya fara mazari ya ajiye komai ya shirya abinci amma yaga ba komai a wajen sai plate da cup,a tsorace ya fice da sauri tare da Umartar Driver dinsa ya kaishi Hospital wurin Momee,ganinsa da driver yayi a firgice tunaninsa Ko jikin Momee ne ya tashi Da sauri Driver yaja zukekiyar motar zuwa asibitin,Momee ma ta kasa gane kan Ahleef taga kamar a firgice yake ta tambayeshi ko lfy yace normal Sabo da abin kunya ne ya fada cewar kamarsa yana Tsoron Aljanun gidansa.
Shukura kuwa kowa ya kalleta yasan tana Cikin Nishadi yau tayi kwanan dadi,idan ta tuna yanda Ahleef ke firgita sai ta kwashe da dariya haka ta yini tana gantali a gari Bata da wajen zama,gashi kayanta Gaba daya suna Hotel ta barsu Bata da abinda zata canja kaya doguwar rigarce kullum a jikinta ko wanki Bata samu ba duk tayi dirty,lokaci yana cika 3pm ta wuce wajen Saudatu me Doya Zata fara aiki,gashi tunda ta cinyewa Ahleef abinci Bata kara cin komai ba, yunwa ta gama kwakwuleta.