← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 59

Sashe 15

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahleef ganin Niima ta koma wajen saurayinta cike da kunyar marin da Shukura tayi mata,sai ta tsaya tana nade borin kunya da hauka tana zubawa Saurayin Murmushi tare da rike hannunsa suna soyayya, Ahleef yaji haushi a kan titi ba mijinta ba saurayi kawai Amma Niima ta tsaya a bainar mutane yana tattabata harda su kiss,yana kallo yar Momeensa guda Zata lalace ba damar magana kawai yaja motarsa bai tsaya ko ina ba Sai wani Mall kato inda Saudatu ke Soya doya da kwai har wasu Sun fara siyar da Fruits a wajen, Shukura sai kallon wajen takeyi,Ahleef duk ransa ya jagule bama ya Jin zai iya komai,kawai Kudi masu yawa ya mikawa Shukura tare da cewa shiga nan ki siyo kayan sawa, Shukura ta fita dukkan mutanen data Sani saida ta fara tsayawa suna ta gaisawa ana wasa da dariya sama sama,Ahleef yana cikin mota yana kallonta yanda take Faran faran da mutane yana mamaki duk ina ta sansu haka,Sai tambayarta akeyi ina Saudatu? Shukura tace ta canja unguwa ne, Haka ta shiga Mall din abin haushin tana yin layin kayan ci da sha da kayan girki sai ta manta da kayan sawa yace ta siyo, chocolate,Biscuits su snacks iri iri kayan zaki ta kwaso,tayi layin kayan dafawa Ko Bata sanshi ba indai ya birgeta sai ta siya,ko idan taga Hoton tukunya a jikin ledar, Ice Cream iri iri, taga yogourt tace laaa bamu da irin wannan a fridge dinmu nan ma ta kwasa,harda su markadaddiyar gyadar gongoni tace wannan da gani zatayi dadi da Bread, side din Drinks taje nan ma taga wata katuwar kwalaba tunaninta lemo ne ashe giya ce duk tsadarta Sabo da kwadayi da son dadi saida ta siya,karshe taga wani wajen Shawurma da ake yi a ciki ta siyo abinta,sai data kashe kudin wajen kayan ciye ciye sannan taje side na kayan kwalliya ta kwaso iri iri babu duhun kai duk abinda Bata gane ba sai ta tambaya an wayar mata da Kai,Sai data gama sannan ta tuna me akace ta siya,a fili tace ai wlh gwara kayan dadi abinda zanji dadi akan wasu kayan sawa,ai da ragowar kudin bari na siyi kala biyu sun isheni kafin nayi kudi ai na kusa zama me kudi.
doguwar Riga ta dauka da Riga da skert Engliish wears sai panties guda biyar,da wani 3qutr tight legins,sai flat shoe kala biyu tace Sun isheni zaman duniya bana kiyama ba taja kayanta takai ta biya Kudin sai dubu uku ce ta ragu change,tace kai bani abin dadi na sauran Canjin babu Awara da kwai a nan ne wai ? Dariya me auna kaya yayi sosai yace babu Hajiya,tace to Kantu me sugar fa ko na gwangwani babu ? Yace sai Snail da frog na gwangwani abincin yan China ne,ido ta zaro tace kwado da dodon kodi ? yace ae,musulmi suna ci ? Ya halatta ? Yace sosai ma ai abin ruwa ya halatta,tace da dadi ? Yace sosai ma, tace to bani Snail kawai banda kwado bana sonsa,yace kin San dadi yafi dadi musamman kika hada shi da vegetables yasha miya me kyau,tace ka hado da ganyan miyar,Mutumi dai ya bata snail da wani ganye kala uku na turawa da suke girki dashi,Ahleef yaga ana ta fito da ledoji kawai boot ya bude aka zuba komai sannan ta zaga ta shiga suka tafi sai murna takeyi kamar zata tashi sama.

tsoro ne ya shigeta ganin yanda yake tuki ransa a bace kamar an aiko masa da mutuwa sai tsaki yake ja,shuru tayi itama Bata ce komai ba,tunaninta ma ko ita tayi masa laifi a hankali tace ko Budurwarka ce na mareta ban Sani ba ? Shuru bai kulata ba,to ko kanwarka ce ? Da kyar yace Budurwa tace,baki ta bude tace Allahhhhh.... Sarki yi hakuri ungo kumatuna rama mata marinta,Dariya ta bashi sosai,tace ka rama mata mutum yana ci da kai ya baka wajen kwana,Sutura ka Isa ka Bata masa maza dalle ni da mari,dariya ya shiga yi nan take Ya koma normal cikin farin cikin da ya dade rabon da ya samu,tace gaskiya Budurwarka Bata Sonka kana gani sai kula wani takeyi yana yi mata abin cikin Film din turawa amma kayi shuru gaskiya mijin tace ne kai,mijin Hajiya ka bada maza, murmushi yayi kawai, Kallonsa takeyi yanda yake me mugun kyau kamar Saudatu musamman idan yayi dariya, yee...wlh irinku daya da wata Tsohuwa me saida doya,juyowa yayi ya dan kalleta ta kwalla da karfi Yeee wlh Saudatu ce kai, Dan kara yin dariya mu gani ? Yaki yi,Shagwaba ta fara dan Allah kayi kaji Kawu Ahleef,har kwakwalwarsa saida tayi wani dumm yanda tayi shagwabar, Yana tuki ta bigi kafadarsa kadan ya sake juyowa suka hada ido ta kyalkyale da dariya tace Saudatu ce wlh, baki ya tabe tare da cewa ki daina hadani da wata yar tasha me doya kinma rainani ki rasa wacce zaki ce muna kama sai me soya doya a titi,Kai wlh ba yar tasha bace mutuniyar kirki ce mace ta gari kuma kyakyawa balarabiya baka ji larabcin da takeyi ba, Ahleef yace koma me takeyi ina ruwana,Dan Allah karka ciwa Inna Saudatu mutunci wlh yanzu nafi sonta a duniya bani da kamarta,ina ma zan ganta da a gidan dadi take wajenta zan koma ta rikeni,Oh sai gidan dadi ke kike so ? Wlh kuwa to bakina ya saba da dandano taya zan so wahala ai sai dole.uhmm kawai yace Jin yanda yar karama da ita ta iya zance haka.suna zuwa gida yayi parking yace to Saudatu muje,Dariya tayi tace suna na yafi na Saudatu dadi wannan na tsofaffi ne, Saida ta kwashe komai ta shigar dashi zata boye yace kawo sai naga me kika siyo nan fa kuma tayi miki miki tana zare ido tace ni dan Allah tunda Sabo da Allah ka taimakeni basai ka gani ba, U are Crazy dalla miko na gani a tsawace ya furta,da Sauri ta dauko komai ta jera a gabansa ya shiga Dubawa,mamaki ya cika shi ganin kayan da suke cikin ko wacce leda,bai San sanda ya kama kunnenta ya murde ba cike da bacin rai kara ta saki sosai ya murde da karfi,ya zuba mata rankwashi yafi biyar masu zafi sannan ya saketa tare da tureta gefe saida ta fadi kasa,Kuka ta zauna tana ta yi a wajen tana ni nafi son kayan dadi kawai kace kayan sawa zan siya, kuma ai kala biyu Sun isheni,Kwalbar giyar ya dauke yace wannan fa Alcohol ce kika siyo,Shuru tayi tana kallo tace to meyasa suke siyarwa idan ba tsinannu ba ni na Zata abin dadi ne ma,giyar kawai ya dauke yace kwashe tarkacenki ki bar min palo,tace nima ai yar gidance palonmu zaka ce abinda na kusa siye gidan ma baki daya,ki cire wannan hakorin makkah naki na karya,wlh bana karya bane kuma ba Makkah zaka ce ba Makoki zaka ce Sabo da zuwana makkah sau bakwai ba daya ba kaga ya wuce Makkah sai makoki, nifa yar me kudi ce ka daina ganin kai wani me kudi ne, Babu me kudin babana a garinmu.Harara ya watsa mata yayi Gaba abinsa ya haura sama tare da zubar da Alcohol din ya jefa kwalabar a Dustbin.

Saudatu har yau kullum sai taje kofar gidan Alhj Dauda tana Jiran Ahleef amma Shuru bai zo ba har ma ta cire rai yau katsam tana zaune ita da mijinta sai ga Ahleef cikin zugar motocinsa tare da Escort Sun bashi tausayi ganinsu a rakube gefen bishiya da sauri ya fito daga motar katsam Saudatu ta Ganshi Murna kamar me haka Alhj Amadu sai yau ya fara ganin Ahleef Shi kanshi sai yaga suna kama da Matarsa Saudatu kadan amma bai kawo komai ba Sabo da ya manta ma Sun taba Haihuwa, Cike da ladabi Ahleef ya gaishesu tare da cewa ya na ganku a kofar gida? Saudatu tace ai tun ranar da kuka tafi suka Sallamemu nan ta labarta masa komai,Ahleef yace ku shiga mota muje kawai,Bayan Sun shiga mota yayi tunanin ya kai Dattijuwar da yake kira da Umma gidansa su zauna tare da Shukura sai yayi tunanin ai kwanan nan Shukura zata tafi ba wani zama zata yi ba, sannan baya son Zargi kar Umma da mijinta taga Shukura budurwa ta dauka ko karuwarsa ce yana kare mutuncinsa a ko ina,Momee dama tana neman me dafa abinci dattujuwa Sabo da Latifa tare da Niima Me musu girki tayi aure ta bar gidan Momee kuma Bata gari,Alhj Amadu kuma da yasa masa suna Baba zai dinga share masa Office da gogewa etc,Gidan Momee kawai ya wuce dasu,sannan ya bugawa Momee da Abba waya ya sanar musu da komai,Part guda karami komai akwai a ciki har kayan sawa dama Ahleef ya tanadar musu babu wani abu da zasu nema su rasa na amfani a bangarensu,Duk ya nunawa ma'aikata su sannan ya daga darajarsu fiye da ko wanne ma'aikaci dake aiki karkashinsa cewarsa su tsofaffi ne baza suyi aikin wahala ba, Latifa ma Ahleef ya hadata dasu Saudatu, ba laifi ta mutuntasu,Niima ma bai fasa ba sai da yace ga me dafa musu abinci,Alhj Amadu kuma a Office dinsa zaiyi aiki.
Ganin Ahleef yana son su Saudatu kuma ya daga darajarsu yasa ita kuma ta tsanesu zasu kara mallake musu iyaye da dukiya,gashi ma taga Saudatu da mijinta suna yanayi da Ahleef sannan mutanen kirki ne kowa Sonsu yake kawai sai ta tsiri wulakantasu,duk wulakancin Niima rabin kafar su Hafcy Bata kama ba, Sai Saudatu take ganin ma ita ai me kirki ce akan su Hafcy Amma duk da haka Bata kaunar Niima a ranta duk da Wulakancin su Hafcy haka kawai sai taji gwara mata Hafcy akan Niima,Ahleef yana gidansa amma yana yawan zuwa ya tambayi Saudatu ko Amadu idan Sun hadu a office ko suna da matsala Ko wani yana yi musu wani abun sai suce ba komai wlh lfy suke.
Chapter 15 · 0% Book details