Sashe 39
Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a garin kuma Shukura tunda ta sauka Allah ya hadata da wani Dattijo da Matarsa su kadai a gidansu Basu da yaro ko daya suka ce Shukura ta zauna tare dasu ba damuwa abinda Shukura Bata sani ba tsofaffin mugayen Yan fashi ne dasu ake hada Baki Ana tare hanya,su suke yiwa Yan fashi waya,Shukura tsakar dare sai taji sun fita suna ta waya, ita Bata San me sukeyi ba,Bata da burin da ya wuce ganin Ahleef yanzu yakai kullum aikin kuka take ba dare ba rannan har ta kwashe sati biyu tare da wannan tsofaffin, wata ranar asabar katsam sai taga Yan sanda sun cika gidan tab sunzo mota mota tare da damke Dattijo da Matarsa an gane cewar yan fashi ne,Zasu hada da Shukura ta fashe da kuka tace Wlh ni bakuwa ce sati na biyu da zuwa garin,Yan sanda suka tambayi Yan gari aka tabbatar musu sannan suka kyaleta,sai gashi an samu bindigu sunfi ashirin a dakin dattijo Nan akayi gaba dasu.
Shukura Tasha mamaki tace Lallai mutum mugun ice Ina ta bacci dasu da gudu ta kwaso akwatunanta ta hau Machine tayi hanyar kauyensu da ta gudu, dai dai lokacin kuma Ahleef yazo Nigeria ba tare da sanin kowa ba,escort dinsa kawai yayiwa waya suka sameshi da sababbin motocinsa sunfi goma a Hotel din da yake ya fito cikin shiri yace a kaishi kauyen su Shukura tunda wasu daga ciki Farhan yaje dasu.
Wanka iya wanka yasha kamar baza a mutu ba,sanye yake cikin wata dakakkiyar Shadda Yar gasken gaske light blue,fitted dinkinsa links,sumar Nan ta Kara yawa an kwashe gefe da gefe kadan taci kudi sai kyalli take hade da Dan sajensa zuwa Dan gemunsa na matasa yasha gyara luf luf sai ya Kara kawata fuskar tasa abinka da farar fata ba a cewa komai,Agogonsa Gucci me tsananin tsada,ga wani takalminsa kalar shaddar irin na sarakai flat half shoe sai kamshi take ta ko Ina,cikin tafiyarsa ta kasaita ya shiga mota suka Ware wuta sai Jos,duk inda suka wulga sai anbi motocin da kallo sabo da kyawunsu.
cikin garin Jos suka ci abinci da sallah kana suka dauki Hanyar Kauyen suma, suna shigowa hanyar, Machine da Shukura ke Kai ya yanko Shima fiiiii Hijab dinta na tashi Yana gefen motocin sun jera suna tafiya, Ahleef Sam bai kula dasu ba sabo da motarsa tana tsakiya,Shukura kuma Bata taba zato ba tunaninta bazai zoba sabo da ta cire Rai da ganin Ahleef,kuma wannan kalar motocin Bata sansu ba Sam,tunaninta ma ko Gomna zasu Kai ziyara kauye,kamar suna tsere da motocin,ga akwatunanta a gaban me Machine filfila wuta kawai suke Suma.
sunzo garin dai dai Yar kasuwar kauyen karama dai dai jikin wani container me charji suka tsaya Machine ya lalace,Shukura tace nazo gida ni bari na sallameka na karasa a kafa,ta sauke kayanta tana lalubo kudi ga rugugin kidan da me chaji ke sawa ya cika kasuwar Baki daya,Sai da su Ahleef suka shugo garin ya bude Ido ya fara kallon gefensa dai dai inda kida ke tashi kamar ance ya kalla itama Shukura ta bawa me Machine kudi kenan ta juyo sukayi Ido biyu ta glass dinsa na mota,ai da sauri ya sauke Glass don ya tabbatar, itama ta kafeshi da kallo wai kuwa shine Anya? Motocin ya bawa Umarni su tsaya, Shukura tayi Masa zuru da Ido har ya bude mota da sauri ya fito a nutse kamshi ya cika wajen kaf, Shukura ta tabbatar shine Bata San sanda ta washe Baki ba kawai sai da ta bi kidan me chaji tayi girgiza da rawa duk mutanen da suke kasuwar da wajen suna kallo hankalinsu ya Kara dawowa wajen sunga Shukura tana rawa,Ahleef ya harde hannaye a kirji Yana zuba Murmushi Yana kallo Shukura tasa kafa ta daki akwatunanta suka watse tace kun zama old version, Ahleef ya Kara sakin dariya ba shiri tare da takowa wajenta itama ta taho da gudu kamar wata yar basketball Haka ta daka tsalle ta makalkaleshi, da badan me karfi bane da sai sun zube a kasa,Kara kankameta yayi Yana manna Mata kiss a ko Ina na jikinta,mutane kuwa sun taru kamar Ana kallon wasan dambe kowa ya zura Ido Ana mamakin ina Shukura tasan wannan Baturen me kudin?ko shine Mijin nata?ko kuma kwartonta ne,wasu kuma suna jinjina rashin kunya da bariki irin na Shukura da wannan saurayi,wasu ma sai rufe Ido sukayi wai baza su iya gani ba kunya suke ji.
Sun dauki Lokaci me tsawo kafi su rabu da juna,Shukura taja gefe tace uhmm kayi kiba da kyau kafi da kana can ka manta Dani,ke kuma kin Kara girma kalli yanda kikayi tsayi let's go muyi magana later.
Mutanen wajen Shukura ta kalla tace wannan ne Mijina Ahleef ku sanar duk me Bina bashi yazo kofar gidan Yafendo ya karbi kudinsa,Ahleef ya dinga dariya wato bashi aka ci Masa haka,da kansa ya bude Mata mota ta shiga Shima ya shiga guard ya rude suka karasa cikin garin kofar gidan Yafendo,kafin kace Me mutane kowa har matan aure an fito ganin Ahleef,masu bin bashi sun cika damkan suma,Iro da Yahaya ne suka fara arba da Ahleef,Shukura tace to ga Mijin,Iro yayi dariya tace bayan kin bar gari abokinsa da iyayensa sunzo,Nan Iro ya Bata labarin zuwan Farhan dasu Baba tare da alkhairin da sukayi musu.
Shukura tace ikon Allah kenan, Ahleef ya rike hannun Shukuransa kakam.
Yafendo tuni an tattaro kan Yan uwa harda kalan dangi sunzo ganin Ahleef me kudi kamar Dan Shugaban kasa shine Mijin Shukura,ga kyau kamar aljani,Kawu saida ya firgita,dangi suka fara Nadama harda bawa Shukura hakuri,Shukura a fili tace yanzu ba da aka ga Naira,da kuwa ai Mahaukaci ya fini mutunci,me zaku Gaya min,wlh kawai kuna Yan uwana Amma bazan ga mutuncinku ba dama dama Yafendo da yaranta.
Ahleef ne ya Dan matse hannunta wai tayi Shuru,tace baka San wacce wahala Nasha ba kawai ka kyaleni,Yanzu kowa ya yarda Ina da aure,kuma ga Mijina,sannan zan iya siye garin Nan kaf,zan iya maida wasu Bayi,Ba danginta ba har Yan garin sai suka fara bawa Shukura hakuri kar ta siye garin,Ahleef ne ya kwantar musu hankali da wasa take muku fa,Yafendo ta gabatar da kowa wajen Ahleef haka kawu sai waazi da Nasiha yake musu,cikin masu ganin Ahleef harda Megari da Liman, Megari a ransa sai Allah ya Isa da tsunuwa yake jawa Ahleef tafi dubu.
Bayan an Gama gaisawa Ahleef yayi musu ruwan kudi, Shukura Bata so ya bawa danginta ko kwandala ba irin abinda suka yi Mata,
Sai fushi takeyi,karshe tace Ina masu bashi,Nan suka cunkuso ciki Suma aka fara da Megari dubu goma,Ahleef ya bada,tace Ina me tsire dubu biyu ne nasa,Ahleef yace nasan za a Rina,tace me balangu da me kifi dubu daya daya,Aishalle adari biyu Amma Bata dubu goma kyauta,Me chemist kudin paracetamol da pad,Ahleef ya bude mota kawai kudi yake irgawa Yana mikowa Ana ta biyan bashi mutane masu yawan gaske,da ya gaji ma kawai wajen kudin ya bude Mata ta karasa da kanta,Wanda zata yiwa kyauta tayi Masu bashi a biyasu har ta Gama kaf,dariya ta bashi sosai yanda ta kware wajen cin bashi sabo da tana da shi tasan zai biya.
Ahleef yanaji Ana Zancen Dinki Ahleef style dama Farhan ya bashi lbr kawai dariya yake a ransa abinsa,har ta Gama tace kazo muje ko zaka ga garin?Ni pls ki shigo mu tafi Abuja dare fa zaiyi Bae ya furta cike da Shagwaba, Murmushi tayi Shagwabar tayi Masa kyau, tace to Dan jira Ni pls ta shiga gidan Yafendo,Bata tsaya jiran komai ba ta fada wanka,bayan tayi wanka ta fito ta canja atamfa cikin kayanta wata sabuwa sau daya ta sata tunda tazo da kayan garin,wata black and blue ce dinkin Riga da skert sun kamata das ba karamin kyau tayi ba,mayafi Baki ta dauka da wani flat shoe baki me tsada duk dama ta sako su cikin kayanta Amma Bata Sa ba sai yau,kamar ka sace ta,yau wankan da kwalliyarta ta dabance,sai gashi ta fito a Yan matan Abuja masu ji da kansu, Yafendo anji kudi Har ta fita ta harhadowa Shukura magungunan tsumi iri iri ta karanta Mata yanda ake amfani dasu ta Bata Leda guda, Shukura sukayi sallama tace watarana zata zo ta daukesu suga gidanta.
Duk ta Dan yiwa dangi sallama an yafi juna,Kawu ma an biyashi kudin kazarsa da ta cinye musu.
Ahleef yaga yanda Shukura ta dau kyau gaba daya ta Kara wani kyau gashi ta sake girma komai ya Kara cikowa sosai sabo da Shan madarar shanu kullum tayi wani fresh kamar ba a kauye take ba.
Bodyspray din Yafendo ta fesa me dadin kamshi,Ahleef ji yake kamar yayi tsuntsu ya gansu a Abuja masau kinsa Hotel,suna tafiya a mota kasa kyale Shukura yayi sai da ya fara kissing din lips dinta Yana lasar Mata wuya,ita kuma tana hanashi wai kunyar Driver pls ka Bari,wani wuri ya Danna kawai sai ga labile masu kyau sun sakko suuuu kasa ya raba tsakaninsu da driver.
Ko Ina ya rufe saisu kadai a bayan mota,jikinsa ya jawota ta kwanta,Shukura tace wai har yau Yaya baka canja halinka na lashe lashe ba?,Murmushi yayi tare da cewa ai ke za a tambaya har yau Baki canja halinki ba kin San mene aure me akeyi,wai ma Ina ciki na Dana yi Miki? Kunya ce ta kama Shukura tace ai yanzu fa watansa biyu da sati Uku bai Isa fitowa ba ,bakiyi period ba? Nayi Mana ai matar Iro tace wasu idan suna da ciki basa daina period itama haka takeyi idan tana da ciki,kaga maybe nima Haka ne.
Ahleef yace uhm gaskiya ne to ki lallaba min Babyna Allah yasa ki haifo min mace,Shukura ta boye fuskarta a kirjinsa tana dariya kasa kasa tace nima nafi so na haifo Mace ta,Sabo da me kike son mace ya tambaya yana kallon fuskarta cike da zallan so,tace Sabo da na dinga yi Mata kitso,Ina shafa Mata Jan Baki, Ahleef yace to ki dage ki haifo ta tunda har nayi Miki cikin,Shukura tayi Murmushi tace tam,wannan kuruciyar ta Shukura nishadi take bashi.