Sashe 49
Jalilah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kara hade fuska ta fizgi robar yoghurt din da karfi daga hannunsa ta budemai sannan ta mikamai.
Amsa yai sannan ya kurba.
Takaici yasa tace "yunwa kakeji amma kaki cin abinci?"
Yace "dama dan mutun najin yunwa sai ya zama dole sai yaci abinci?"
Tace "ba dole tunda cikin mutum ne."
Yai shiru tare da cigaba da tukinsa, meyasa nace haka? Ahh meke damuna? Abinda zuciyarsa ke fadamai kenan.
Jalila kuwa ta kara kumbura, kallanta yadanyi kadan sannan ya mika mata yoghurt din, tace "me zanyi kuma?"
Yace "sha?"
Tace "nace banasha."
Yace "ke da kikejin yunwa meyasa bakici abincin ba?"
Ta kalleshi sannan tace "Yaya wai dan Allah me yasa kakemin haka?"
Yace "me?"
Tace "yau sai ka min magana cikin sanyi, anjima sai kamin cikin zafi, wata anjimar kuma amsa ma ban isa samuba."
Yace "haka kike gani?"
Cikin wata irin murya da ita kanta bata sani ba tace "hakan ne mana."
Da sauri yai gefen titi dan jiyai wani abu ya tsirgamai, kallanta yai sannan ya kalli kirjinta, da sauri yamaida kansa titi ya hade rai, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, fizgar motar yai da karfi.
Haushi ne ya kara kamata, ta juya tana kallan titi.
Can dai ta daure tace " ina zamu siyo kayan?"
Yai shiru kafin yace " me kike tunani akan nemawa Goggo wani gidan? Ko a cikin gidajen Abba ne dan yanada na haya."
Jalila tace "Goggo tace wani abun ne?"
Yai shiru, ta dan yi ajiyar zuciya tace " dama tunda naje gaisheta da safe naji tana cewa ina ita ina zama gida daya da sirikai? To ni ban gane me take nufiba, dana tambayeta kuma sai tace bakomai."
Hassan ya kalleta yace "me kike tunani?"
Ta kalleshi tace "Yaya nikam tsoro nake, kar Goggo ta zauna inda mutanen nan zasu sani, dan wlh Inna bazata barni ba tunda na bata mata plan."
Hassan ya kalleta yace " karki damu dasu, ba abinda zasu iya."
Jalila tace "Yaya bakasan Inna bako?"
Yace "me zai sa na santa bayan banida hadi da ita?"
Jalila tai murmushi tace "ya kake gani?"
Yace "yanzu muje ki siyo mata kaya, da abinda zata bukata sannan sai ki mata magana akan gidan da zata zauna kiji."
Jalila tai shiru tana kallansa, juyowa yai ya kalleta yace "kallanfa?"
Tace "wani sa'in rasa abin cewa nakeyi."
Yace "kin huce kenan?"
Tace "ai ba fishi nai ba, kaine fa kacemin wai bazakaci ba."
Yace "bazanci ba so kike nace zanci?"
Tace "ba haka nake nufi ba.
"To me kike san ji?"
Shiru tai tare da tambayar kanta, me nake sanji?
Hassan bai kalleta ba ya cigaba da tukinsa.
Can Jalila tace "Yaya nagode sosai harma bansan ta ya zan yi godiya ba, yaushe Ameera zata dawo ne?"
Yace "Ameera batanan?"
Kallan mamaki tamai tace "bangane ba?"
Bai tanka mata ba, ta cigaba "dan Allah bakasan bata gida ba? Ta dade fa batanan."
Nan ma baice komai ba.
Haka suka isa ya zauna a mota yace ta shiga ta siyo kayan, ya mika mata Atm dinsa.
Kallan mamaki tai tace "wai ni kadai zani?"
Yace " badai kina tunanin dani zaki shiga ciki ba?"
Jalila cikin mamaki ta kalleshi tace "Yaya ni wlh tunda nake bantaba zuwa irin wannan gurin ba, sannan bantaba siyo abu ma da Atm ba bare nasan ya akeyi."
Kallanta yai kamar zaiyi magana sai ya fasa.
Kallansa itama tai tadan shagwabe fuska tace "Yaya Please!"
Shiru yai yana kallanta kafin ya bude kofar ya fito, yana fitowa itama ta fito da sauri ta matso inda yake.
Can gefe yaje ya tsaya yana kallanta wai ta gama zaba, tsayawa tai a gun atamfofi tana tunanin wanda zata dauka tare da duba kudin da aka rubuta a jiki.
"Bakya tunanin wannan yafi kyau?" Abinda taji an fada kenan, muryar daga bayanta ta fito.
Da sauri ta juyo, baya tadanyi kadan ganin mutum a bayanta.
Murmushi ya sakar mata yace "Sunana Al-Ameen Abbah."
Dan baya ta sakeyi tace "Malam......."
Ganin Hassan tai a bayanshi, hannu yasa ya dan bugi kafadarsa, mutumin ya juyo rai a bace yace "Malam meye hakan?"
Hassan yace "zaka tafi abinda ya kawoka ne ko kuwa?"
Yace "mene? Kai."
Wani kallo daya bugama Jalila ne yasa tai saurin matsowa kusa dashi, kallanta yai yace "wuce muje." Gani tai ya nufi kofar fita tace "bamusai kayan ba."
Yace "banasan shagon."
Jalila ta bishi fa kallo, tare da binshi mota.
Waya ya dauko ya kira Ameerah.
Yauce rana ta farko data fara ganin kiran yayanta a wayarta, cikin mamaki ta daga tace "Hello."
"Kina ina?"
Tace "Yaya? Ina gidan Aunty Nana."
Yace ki shirya zanzo in daukeki." Mamaki ya kamata bayan ya kashe wayar tabi wayar da kallon mamaki.
Da sauri ta mike ta hau shirya kayanta.
Aina'u tace "Ameera tafiya?"
Tace "eh yaya ne zaizo ya daukeni yanzu."
Aina'u tace "Kice yau akwai zolaya gun Yaya Sageer?"
Tace "Yaya fa ba yaya Sageer ba."
Mamaki ne ya kama Aina'u bata dade da shiryawa ba ya kira wayarta yace ta fito yana waje."
Aina'u tace "Ameera tafiya zakiyi ga Mamana batanan?" Tace "inta dawo kya fada mata." Cikin hanzari tai waje.
Mamaki ne ya kama Aina'u ta biyota waje dan tabbatar ma idanta, aikuwa shine a zaune matarsa na gefensa.
Aina'u kishi da takaici ya kamata ko fita daga gate din batai ba ta koma ciki ta fada gado tana hawaye, itafa ya kamata ta zauna a kusa da Hassan ba wannan yarinyar ba.
Ameera ta shiga baya bakinta yaki rufuwa, yauce rana ta farko da yayanta zai fita da ita guri a motarsa.
Jalila sai murna take taga Ameera tana ta neman jan ta da hira, Hassan yai gyaran murya sannan yace "maganar ta isa, inkunje gida kwayi."
Jalila tai gum da bakinta.
A kofar wani store ya ajiye su ya kalli Ameera yace "Ameera kuje tare kaya za'a siyoma mahaifiyarta, sannan ya mika mata Atm dinsa."
Tace to yaya, ta fita.
Jalila na neman fita ya riko hannunta, juyowa tai ta kalleshi yace "yanzun ma inkin je ki kara bari wani katan ya miki magana."
Tace "wancan din ma ni na bari? Sannan bafa komai yace min ba cemin kawai yai wannan yafi......."
Wani kallo ya maka mata, ya rufe bakinta tace "to."
Ya saketa ta fita.
Da kallo ya bita har ta shiga cikin shagon na Jifatu.
Meke damunshi? Meke damunshi????
Abinda yaketa tambayar kansa kenan.....
#OneLuv💕
🗯 *JALILAH* 🗯
Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_💡)
*47*
Hankalinsa ya kasa kwanciya, fitowa yai daga motar tare da dan matsowa kadan da kofar shiga yadan leka ciki kadan.
Security din dake gun ne ya kalleshi yace “Yallabai shiga zakai?”
Hade rai yai ya juya jikin motarsa, hannayensa ya hada yana dan hadasu da waresu, kafin ya koma cikin mota ya dauko wayarsa.
Mintinsu sha biyar kenan da shiga, me sukeyi haryanzu? Ko alert bai gani ba bare yasa ran sun biya.
Wayarsa ya dauko ya danna number Ameera.
Sukuwa suna ciki Jalila kome Ameera ta dauko indai taga kudi sai ta maidashi, Ameera ta tsaya tace “to nidai bansan me kikeso mu siya ba, duk abinda na dauko sai ki maida.” Ta karasa maganar tana kallan kwandon nasu da bakomai a ciki sai atamfa kwaya daya.
Kiran Hassan ne yasa ta kalli Jalila tace “Yaya!”
Jalila ta kalleta bayan ta amsa kiran, Ameera tace “Yaya....”
Yace “me kukeyi haryanzu? Badai shirme kuka tsaya yi ba?”
Tace “a’a Yaya, ni narasa me zamu siya ne, duk abinda na dauko sai Yaya Jalila tace wai yayi tsada sai ta maida.”
Hassan ya kashe wayarsa baijira ya gama jin abinda zatace ba.
Tahowa yai ya shiga ciki, security din ya bishi da kallo yana yan kunkuni, inkasan shigowa zakai gulmar ta menene? Tun dazu ka tsaya kamar mai jira.
Hassan na shiga ya sake kiran Ameera ya tambayeta inda suke, ta sanar dashi.
Yana isowa ya bugama Jalila kallan harara sannan ya kalli Ameera yace “ina kayan da kika zaba?” Nan ta shiga daukowa tana sawa a cart din, mamaki na kara ratsata, bata dade a gidansu Aina’u ba yaushe har yayanta ya koma haka?
Jalila na tsaye tana kallansu sai zuba kaya sukeyi a cart din har sai da ya cika sannan suka nufi gun biyan kudi.
Tana can gefe suka biya kudin sannan ya kalleta ya nuna mata ledoji, matsowa tai ta dau leda biyu manya itama Ameera tadau biyu suka nufi kofar fita.
Yana kallanta da yanda ledojin suka mata nauyi dan kamar ma janta sukeyi, kallanta ya sakeyi sannan ya kalli ledar ji yake kamar yaje ya amsa sai dai inaaa bayaji zai iya yin hakan, balle agaban Ameera.
Taje kusa da motar bata kula da saman interlocks din daya dago ba, jitai tayi tintibe da sauri yasa hannu ya riko cikinta.
Ajiyar zuciya tai dan ta tsorata ga kayan da suka kara rinjayarta.
Juyowa tai ta kalleshi kawai sai tai dariya tace “yaya wlh na tsorata, har na hango kaina ya bugu da jikin motar.”
Jawota yai ta mike daidai sannan ya kalli gun datai tuntube, lalai mutanen nan basuda hankali tayaya bazasu gyara gun ba? Fuska a daure ya kalleta yace “meyasa bakya kallan kasa in kina tafiya? Da bana kusa ko da banyi hanzarin kamoki ba me kike tunanin zai faru?”
Ta kalleshi jikinta yai sanyi tace “wlh ban......”
Gani tai ya wuceta rai a bace, ledar hannunta ya amsa ya sa a boot din motar sannan ya bude ciki ya shiga.
Ameera ta ajiye nata itama ta shiga baya sum sum.
Jalila ma jiki a sanyaye ta shiga, to laifinta ne? Itama ai da saninta bazata bari ta fadi haka ba.
Harya tada motar ya fito daga ciki ya nufi gun secuydin.
Kallansa yai fuskar nan a daure, security din ya kalleshi yace “Yallabai da wani abun ne?”
Shiru yai yana tunani, menene damuwarka da har kazo nan zakai fada akan su gyara gun da yarinyarcan zata fadi? Menene damuwarka Hassan.
Bai tanka mai ba ya juya, security din ya bishi da kallo yace “yau ni kuma ina na samo wannan?”