← Book details Jalilah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 53

Sashe 40

Jalilah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

So? Hassan ya kalleshi ya sake cewa, so? Abba so kace?"

Abba yace " Hassan wai me yasa kake kokarin juya kalamai na zuwa abinda ranka ya raya maka?"

Hassan cikin dan daga murya yace "ta ya bazan fassara ba? Ta yaya Abba zaka kalleni kacemin wai so? Ta yaya zaka furtamin kalmar so, sannan kalmar san bawai akan Ummy kake yinta ba, ta ya........"

Kasa karasawa yai saboda numfashinsa dayaji yana seizing.
Abba ya mike da sauri yazo kusa da shi yace "Hassan menene?"

  Hassan ya zare jikinsa daga rikon da Abba yamai ya dan ja baya cikin takaici yace "ni danka ne, banida ikon hanaka abinda kai niyya, sai dai wlh Abba kamar yanda na fada in dai had ina numfashi bazan taba bari ka tozarta Ummy ba."

  Kofar dakin aka bude, Abba ya kalli kofar shikam Hassan kai ya juya cikin takaici dan yayi tunanin Jalila ce.

  Muryar Ummy yaji tace "Hassan!"

Juyowa yai da sauri ya kalleta, Ummy ta share kwallarta data zubo mata sannan ta matso kusa dashi dariya yaga tanayi tana share hawayenta, tace " Hassan yanzu Sageer ya kirani, Dr yace sauki ne ke samuwa a gareka,  ya gama min bayani naga bazan iya hakuri ba sai na ganka."

Ta kara share hawayenta tace "Hassan bansan yanda zan kwatanta maka dadin da nakeji ba."

  Cikin takaici ya kalli Abba sannan ya kalli Jalila wacce ta juya ta fita, Hassan ya kalleta yace " Ummy?"

Tace " fadanku da Abbanka a kaina?"

Ya kalleta cikin tausayawa, tai murmushi tace "karka damu Hassan bakomai, ko ka manta ba mace daya aka halarta ma namiji ha aura ba? Ta yaya zaka nemi mahaifinka ya zauna da mahaifiyarka ita kadai? In mukai haka bamuyi san kai ba? Ko baka ga na fara tsufa bane?"

  Idanunsa ya rufe cikin takaici yace " ya wani irin  zance kikeyi Ummy? Waye zai ga Ummy yace ta tsufa?"

Ummy tai dariyar takaici tace "ba wani kai dai sankai zakai, Hassan gashi nan na fara gani."
Yace "me?"
Tace "samun saukinka mana, rabon da kayimin magana mai tsayi haka har na manta, yau gashi nan kana min magana."

  Shiru yai kawai yana kallanta, Ummy cikin jin dadi tace "Kar kasa komai a ranka, ka manta da maganar da kukai yanzu, kayi kokari ka dawo Hassan dinka ma da, I really miss that Hassan."

  Baice komai ba sai kallanta kawai da yakeyi, Abba ne ya share kwallar data dan zubo mai, sannan yai waje da sauri.

Ummy ta kalli Hassan tace "Please ka kula da matarka, wannan shi kadai ne abinda ni nakeso, kaji?"
Hassan yai shiru, ta juya tai waje.

  Jalila na zaune a kasa a falo ta sa kanta akan gwiwowinta, gaba daya abinda ke faruwa ya sa tausayin Ummy ya sa ta zubar da kwalla, wannan wace irin macece? Ita lafiyar Hassan ce a gabanta bawai abinda taji ba?

  Tana kallan Ummy ta fita, mikewa tai ta shiga dakin, gani tai har ya tada sallah.
Nan itama ta wuce tai alwala tai sallah, ganin bashida niyar mikewa daga kan sallaya yasa ta fito daga dakin.

  Abba kam daki ya shiga ya shiga zagaye dakin cikin takaicin abinda zuciyarsa take sashi aikatawa, wani irin butulci ne hakan yake shirin yi? Ummy ce ta shigo dakin tacemai, yallabai ka fito kaci abinci, ko in kawo ma nan?"

Jiki a sanyaye yace "muje can din."

  Ya zauna akan kujera ta zubamai sannan ta turamai abincin gabansa, sannan ta juya tai daki.

Da kallo ya bita dan baisan ta ina zai fara magana ba, shi yanda takeyi kamar ma batasan me ake ciki ba shine ya kara tsoratashi, dana sani ya kara kamashi.

  Jalila kam, sai yamma liss ta samu taci abinci kadan, sam ba fuska agun Hassan, dan ko kallanta baiyi ba bare ta samu damar yi mai magana.

Haka tai tayin abinda zatai har dare, shikansa Abba har dare bai samu damar yi mata magana ba.
Bayan sallar Magrib ne Sageer zai shigo yaga motar Dady.

Nan yasa aka budemai yai parking din motarsa, Dady ya fito suka gaisa, Sageer ya jashi ciki.

Yau gidan tsit ba dadi, Hassan na daki, Jalila na falo a kan carpet a kwance tana latsa waya, Ummy na falo shi kuma Abba yana daki.

Sageer ne ya shigo ya kalli Ummy yace "Ummy dadyn Jalila me yazo."

Mikewa tai da sauri tace "ka shigar dashi falon Abba"

Nan Sageer ya shigo dashi yai bangaren Abba.

Ummy ta bude dakinsu ta kalli Abba dake zaune yayi shiru abin duniya ya dameshi tace "Abban Ameera ka fito Baban Jalila ne yazo."

Abba ya mike tare da cewa to.

Ta juya ta fita, Sageer ne ya karaso yace "Ummy na kaishi."

Tace "Sageer dan hau sama kama Jalila magana, bari na shirya abin sha."

Yace to, sannan ya hau sama har zai kwankwasa kofar yaji motsi a falon, nan ya juya ya falon, a kasa ya ganta tana ta latse latsen waya, tv din ma ba'a kunne take ba.

Kallanta ya tsaya yana yi cikin tausayawa, sai dai ya taya yayansa murna ta fara samun lafiya, sai dai shikam tausayin kansa yakeyi, anya zai iya san wata kuwa?

  Jalila ce ta juyo, ganinsa tai a tsaye ta mike zaune tana kallansa, yace "ashe kina nan?" Ya dan sosa keyarsa.

Tace "Eh."
Yace "Uhmm dama Ummy ce tace nazo na fadamiki Dadynki yazo."

Kallansa tai cikin mamaki tace "Dady?"

Yace "eh, yana fallon Abba." Ya fada tare da juyawa.

Jalila ta mike gabanta na faduwa, me yazo yi? Badai wani abin bane ya samu Goggon ta?

A rikice ta shiga dakin tana neman hijab dinta, gashi a gabanta wanda ta ninke bayan tayi sallah amma tsabar hankalinta baya jikinta sam ta rasashi.

  Hassan dake zaune yana kallanta shine yace "menene?"

Matsowa kusa da shi tai kamar dama jiran kiransa takeyi, tace "Yaya! Dady ne yazo, baka tunanin ko wani abun ne ya faru da Goggona? Ko kuma wani abun suke shirin yimata?"

  Ganin yanda ta rikice ne yasa yace "Dan yazo shine kika rikice haka?"

Tace "Yaya bansan........"

Tai maganar cikin wani irin murya mai raunin gaske, da yatsarsa ya nuna mata hijab din sannan yace " a haka zaki?"

Ta kalleshi alamar rashin fahimta, yace “ bazaki daidaita kanki ba?”
Tsayawa tai tana ajiyar zuciya wai tana calming din kanta, baisan yanzun ma bakinsa ya motsa ba saboda yanda takeyi.

Yace “yimin magana naji.”
Tace “Yaya!”
Yace “sake.”
Tace “Yaya.”
Yace “bai yi ba.”
Baki tadan turo tace “dazu amma inasan maka magana ai hade rai kayi.”
Ya kalleta yace “ ni yanzu inaji damuwar dake gabanki tafi tawa, ke mahaifiyarki zaki ceto wace take hannunsu, ni kuma i am confidence akan I will protect mine.”

Tace “ni ma.......”
Sai kuma tai shiru dan tasan she is not confident.

Yanzu ma bakinsa sai da ya sake motsawa yace “jeki, bari na jira naga yanda zakiyi.”

Ta kalleshi tace “yaya zakazo?”
Yace “ina kenan?”
Tace “ gun Dady, tsoro nakeji kar ya sani abunda banzan iya bijerewa ba.”
Kafada ya daga mata alamar ba ruwansa.

Jalila tai raurau da ido tace “Yaya Please!”

Samun kansa yai da kallanta cikin wani yanayi sannan yace “ki wuce kije ko?”

Ta dau hijab jiki a sanyaye ta fita..........

Da kallo ya bita har ta fita daga dakin, yabi kofar da kallo.

#OneLuv💕

🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*

     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*39*

  Fitowa tai jiki a sayaye, abin duniya duk ya dameta ga tsoron abinda zai fito daga bakin Dady da takeyi.

  Tana sauka kasa taga Ummy, Ummy ta nuna mata hanyar falo tare da mika mata tiren dake dauke da juice da cup, Jalila ta amsa tare da yin murmushin dole sannan ta nufi falon.

A gefen kofar da zata shiga da ita falon taga Sageer a tsaye, kallansa tai da idanunta wanda suka cika da taoro, yace "Jalila, menene wai?"
Kai ta girgiza mai alamar ba komai, zata shiga yankara kasa da murya yace "Jalila?"
Juyowa tai ta kalleshi, yace "Bakyasan ganin mahaifinki ne? Naga tunda na fada miki yazo naga fuskarki ta canza."

  Murmushin yake tai sannan tace " bakomai, nagode."
Kawai ta shiga, dan batasan me zatacemai ba.
Abba na falon suna ta magana ta shiga bakinta dauke da sallama.
Abba da Dady suka amsa, Dady ya kalleta cikin farin ciki yace "Jalila!"
Jalia tace "naam sannan ta karasa ta ajiye tiren a gabansa ta gaisheshi.
Abba ne ya mike yace "yanzu ba abin business kazo ba, uba ne yazo ganin yarsa, kaga bai kamata na shiga tsakani ba, later mayi magana."

Dady ya mike yana godiya har ya fita, kallan Jalila yai wacce ke tsugunne a inda ta ajiye juice din, Dady yace "zauna mana."

Ta gyara zamanta tana kallansa, gabanta sai faduwa yake.

Dady ya zauna sannan ya kalleta yace "hmm ya gidan?"
Tace "lafiya, wani abun ne ya samu Goggona?"

Yace "wani abun? Kamar me kenan?"
Tai shiru ta kasa magana, yace "dan uba yazo ganin yarsa sai ya zama sai akwai matsala?"

Jalila ta kalleshi tace "a'a ba haka bane."

Yace "Jalila ni mahaifinki ne, ki daina dararewa da ni."

Ta kalleshi kawai bata ce komai ba.

Matsowa ya danyi kusa da ita yace "jalila magana nakesan muyi."
Kallansa tai cikin tsoro, yace "Nikam ya kukai da mijin naki?"
Tace "wani mijin?"
Yace "wanda kukazo tare mana, badai wani abun kika fadamai ba ko? Naga kamar baiji dadi ba ranar."

Jalila ta kalleshi gabanta na faduwa ta kasa magana, Dady yace "amma yasan Goggo ce ta haifeki ko?"
Jalila ta daga kai alamar eh, Dady yace "ya fadama wani ne?"

Tace "ban gane ba?"
Yace "ya fadama wani kamar mai gidan nan cewar Goggo ce ta haifeki?"
Jalila tai shiru, yace "ba dai duk wani sirri na gida kin fadamai ba?"

Jalila ta kalleshi yanzun ma batace komai ba, ya kalleta ransa a bace, badai duk wahalar da wulakancin da ya hadiye ba lokaci daya wannan yarinyar zata zo ta ruguzamai? Dan ya tabbatar in har Taura ya kwace kudin daya basu tabbas Inna korar sa zatasa ayi daga company din.
Chapter 40 · 0% Book details