← Book details Jalilah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 53

Sashe 24

Jalilah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummy ta rungumota jikinta, zafin da jikinta ya dauka ne yasa hankalinta ya tashi.
Ta kalli Sagir rai a bace tace "buga mai kofa."
Sagir ya mike ya nufi dakin Hassan.

Yana kwance akan sallaya yanajin lecture na Sheik Ahmad Deedat, jin knocking yasa ya mike ya bude kofar.
Sagir ya kalleshi yace "kazo."
Haka kawai yace ya juya, bai musa ba yabi bayan Sagir, gani yai ya shiga d'akin sa na da.
A bakin kofar ya tsaya, Jalila ya gani a kwance a jikin Ummy.

  "Ummy!"
Kallansa tai rai a bace tace "Hassan me kenan?"
Yace "me ya faru?"
Sagir ta kalla, tace "Sagir muje akaita asibiti."
Sagir da sauri yai waje, duk ya rikice, gani yake kamar duk laifinsa ne.
Ummce y ta kalleshi tace "ni zan kaita mota?"
Karasowa yai ya d'agata.
Jin an d'agata yasa ta bude ido a hankali, kallansa kawai tai sannan ta maida idan ta rufe dan wani irin jiri take ji.

Shikam fuskar nan a hade ya ajiye ta a bayan mota.
Ummy ce ta fito itada Ameera ta kalli Sagir tace "Sagir ku kaita asibitin, sai muje ya ake ciki."
Yace to, sannan ya shiga mota.

Ko kallan Hassan batai ba ta juya ciki.
Sagir ya kalleshi yace "Yaya mu tafi?"
Yace "kuje ni banasan asibiti ka sani, amma me ya sameta?"

Ameera tace "Yaya aikai za'a......"
Kallan daya mata ne yasa ta guntse maganar ta, juyawa yai kawai yai ciki.
Sagir ya kalli Jalila dake cikin mota, shiga motar yai yaja suka fara tafiya.
Ameera tace "muje Standard tunda yafi kusa."
Bai musa ba ya wuce, Ameera ta kalleshi tace "Yaya menene? Naga hankalinka a tashe."
Kai ya girgiza kawai baice komai ba.
Shiru sukai har suka isa asibitin.
Ameera ce ta kamata suka shiga ciki.

Sagir yaje a ciro musu file, yace Ameera ta zaunar da Jalila.
Jalila ta kalli Ameera tace "Dan Allah zan hau sama."
Ameera cikin mamaki tace "me zakiyi?"
Jalila tana numfashi sama sama tace "Dan Allah ki rakani."
Ganin yanda ta damu yasa ta rike hannuunta suka hau sama.
Suna zuwa kusa da dakin Goggo, Jalila ta zare hannunta daga cikin na Ameera sannan ta tura kofar d'akin.

  Goggo na kwance tana bacci, Jalila ta shiga.
Ameera cikin mamaki itama ta shiga d'akin ta tsaya a jikin kofa.
Jalila ta karasa kusa da gadon Goggo sannan ta riko hannunta.
Wasu hawayene suka taho mata, Goggo ta bude idanunta jin an riketa, kallan mamaki tama Jalila tace "Jalila kece?"
Jalila tace "in ba ni ba wacece Goggo na?"
Goggo tai dariya tace "wato dana ce ki zauna a gida ki huta kasa zama kikai ko?"

Tace "ina zan iya zama banganki ba?"
Goggo ta kara riko hannunta da sauri ta mike zaune sannan tasa hannunta a goshinta tace "Jalila! Bakida hankali ne? Kina irin wannan zazzabin kika fito?"

Jalila tai murmushin yake tace "karki damu Goggo ba wani wahala yake ban ba."
Goggo tace "ga wanda bai kalleki ba kenan, duk kin rame a dan kwana biyun da ban ganki ba?"

Jalila tai kasa da kanta.
Ameera ta kalla sannan ta kalli Jalila, tace "wannan fa?"

Ameera ta matso ta gaisheta sannan tace " ni kanwar yaya......"

Da sauri Jalila tace "kawatace Goggo, biyoni tai dan ta gaisheki."
Mamaki ne ya kama Ameera wacece wannan da har batasan asan matsayin ta? Sai dai ba shakka suna tsananin kama, dan kamar ma harta baci.

Jalila ta kalli Ameera, Goggo ta kara kallanta tace "Allah sarki na gode sosai."
Ameera tace "bakomai."
Kallan Jalila tai tace "bari inje gun Ya Sagir."
Ta juya ta fita, tana rufe kofar ta kara bin kofar da kallo, tabbas dabadan ance yar Mumy bace da tace wannan ce mahaifiyarta.

  Kwanciya Jalila tai a gefen Goggo dan tana jin jiki, Goggo ta shafi kanta tace " ki koma can ki kwanta dda kyau mana."
Jalila ta girgiza kai tace "barni anan."

Goggo ta kalleta tace " naji yarinyar nn tace Yaya Sagir? Ko Sagir din da ake bani labari?"
Jalila tai shiru dan batasan me zata ce ba.

Goggo tai murmushi, Jalila kam idanunfa ta rufe kawai, tana san sanar da mahaifiyarta sai dai tana tsoron kar jinjnta ya sake hawa, dan kuwa sanda aka kwantar da ita sai da akace a kiyaye sata a damuwa, wanda ta tabbatar in Goggo taji, ba magana kawai.....

  Acan gidansu kuwa Hassan ya shigo cikin gida, Ummy na zaune afalo tai shiru.
Tsayawa yai yanasan mata magana kuma baisan ta inda zai fara ba.

  Ganin bata da niyyar kallansa yasa ya juya jiki a sanyaye zai hau sama, jiyai tace "yanzu Hassan abinda kai ka kyauta min?"
Juyowa yai sannan ya matso kusa da ita, yace Ummy ni ban gane me na aikata ba.

Tace "kafi kowa sanin yanda matsala da lalurar cikin dare ke faruwa, taya zaka bar yarinya ita kadai a daki, yanzu inda ciwon ya gama cinta cikin dare fa?"
Yace "Ummy kinfi kowa sanin bana iya kwana da wani kusa dani....."
Tace " Hassan kanaso kace bakasan dalilin dayasa muka nemarma aure ba? Ko kuwa san kanka ne ya maka yawa da baka duba halin da nake ciki?"

Kallanta yai jiki a sanyaye, tace " akoda yaushe hankalina baya kwanciya da barin ka kai kadai a daki, saboda ina tsoron abinda zai iya faruwa, sannan yanzu an maka aure nan ma kace kai kadai zaka dinga kwana? Fad'amin Hassan menene marabarka da kafin kai auran?"

Kallanta yai sai dai baice komai ba.

Tace "In har na isa dakai na kuma isa in fadama kaji to daga yau inganku a d'aki daya, ban damu da duk abinda zai biyo baya ba sai dai jiya ya zama rana ta karshe da zaku kwana tare, sannan ko kunya ka barsu suka tafi asibiti kai ka shigo."

Yace "Ummy kinsan bana san asibiti."
Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa, dolene subi komai a sannu tunda gaggawa ma aikin shedan ne.

  ****
Sagir ne ya kalli Ameera yace "ina kuma kuka je?"
Nan ta fadamai abinda ya faru, cikin mamaki yace "yanzu tana can?"
Tace "eh."
Sagir ya haura saman.

Jalila na kwance kusa da Goggo suka bude kofar tare da sallama.

  Jalila na jinsa ya shigo, kallab Goggo yai sannan ya gaisheta.
Ta amsa fuska a sake tace "Malam Sagir ashe da rabon zan ganka?"
Dasauri Jalila ta d'ago ta mike tsaye tace "Goggo sai mun dawo."

Mamaki ne ya kama Sagir, ya mike yana cewa "ki zauna...."
Tace "muje kawai."

  Sai da suka kai kofa sannan ta ma Goggo salama suka fita, suna sauka ta kan beni mai kula da Goggo tana hawa.

Gaisawa kawai sukai suka sauka.

An mata gwaje gwaje sannan aka bata magunguna, akace su jira a gama test, Ameera tace "Ya Sagir ka maidamu gida, kai ka dawo ka amsa."

#Oneluv💕
[08/10, 02:16] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*I am really Proud of you! Can't believe Kainuwa has reach more than 300k views on wattpad, Heart U* 💕💕💕💕💕💕💕

*No 24*

   Shiga d'aki yai ya tsaya yai shiru, tunani yake mai yai? Shi dai a iya saninsa baiga laifin da yai ba.
  Bandaki ya shiga yai wanka, zama yai shiru, ga wunya da ta fara cinsa, yau Ummy mantawa dashi tai? Ko laifin daya mata ne yasa tai fishi dashi?

  Kwanciya yai ya d'au jornal din da yake karantawa.
Jiyai yau karatun sam ba dadi, shi yace amai aure? Mikewa yai zaune sannan ya shafi fuskarsa, makullinsa ya d'auka da wayarsa ya fito, ba kowa a falon hakan yasa yai waje.
Yana kokarin shiga mota, su kuma suna shigowa.
Sai daya jira sukai parking sannan ya shiga mota ya tada ta.
  Sagir ya fito da sauri yanasan mai magana, kafin ya karaso Hassan yaja motarsa yai gaba.
Sagir yabi motar da kallo, a ransa yace "anya nama Jalila adalci kuwa?"
Ameera ce ta bi motar sa da kallo sannan ta kalli Jalila ta mika mata hannu, Jalila tai murmushin yake sannan ta fito.
  Ameera ta kamata suka shiga ciki.
Ummi najin motsin mota ta fito, tana kallan sanda Hassan yai waje, ga Abba tun safe yau ya tafi Abuja.
  Suna isowa falon Ummy ta rike Jalila ta shigar da ita dakin Ameera tunda a kasa yake.
Ummy ta kalli Ameera tace "Ameera dauko abinci."
Nan Ameera ta fita, Jalila ta fara kokarin mikewa tana cewa "Ina kwana?"
Ummy tai saurin riketa tace "Karki damu, ma gaisa inkin ware."
Sagir na tsaye a jikin kofa yana murmushi, yasan halin Ummy ya tabbatar Jalila bazata taba wulakanta ba indai har Ummy na nan, kaf a duniya shi agunsa bai taba ganin mace kamar Ummy ba.

  Ameera ce ta shigo da tiren abincin, Ummy tace "zubo mata dankalin kadan"
Ameera ta zuba mata ta mika ma Ummy, da kanta ta gyara mata zama sannan ta mika mata abinci, kallan mamaki Jalila take mata, bata taba tunanin zata samu kulawa haka ba, balle daga zuwanta ko sanin ta ba'ai ba.

Haka ta dinga dan ci dan samon kanta tai da kasa yima Ummy musu, sai data gama Ummy ta miko mata magani da ruwa.
Sai data sha, sannan Ummy tace karki kwanta kidan jira abincin ya tsirga miki kadan sai ki kwanta.

Jalila ta d'aga kai, sannan ta maida idanta kasa.
Ummy tai murmushi ta fita.
Ameera ta mike ta biyota.

Sagir na zaune a falon suka fito, yace "Ummy na!"
Tace " Sagir sannu da kokari."
Yai murmushi sannan yace "Ina Yaya yaje? Naga ya fita yanzu."
Yanayin fuskarta ne ya canza, tace "yaushe rabon da insan inda Hassan zaije?"
Sagir yai shiru dan ya fahimci yayi laifin tambayarta, Ameera ya kalla yace "Ashe kawarki ta koma gida?"
Ta dan turo baki tace "sai yanzu ma ka kula?"
Yace "kinsan dazu muna kan Jalila sam ban kula ba."
Ya mike yai kitchen.
Ameera ta kalli Ummy tace "Ummy nikam dazu a asibiti, na rasa wa taje dubawa."
Ummy tace wa kenan?
Chapter 24 · 0% Book details