← Book details Jalilah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 53

Sashe 39

Jalilah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Sageer ya kalleta yace "Ummy akaishi daki."
Ta matsa tana share hawayenta, hannunsa ya zare daga jikin Sageer sannan yace "take care of Ummy zan karasa da kaina."

Sageer ya kalleshi har yai gaba, Jalila tabi bayansa da sauri.

Ummy kam jingina tai da motarsa tana share hawaye, Sageer yace "Ummy muje ciki."

Kallansa tai tace "Sageer kaji karar da ya saki? Bai tabayin irin haka ba, ina murna ya fara samun sauki, Sageer meke shirin faruwa?"

Sageer yai shiru tausayin Yaya da Ummy ya hanashi cewa komai, ta share hawayenta sannan tace " Sageer kaje gun Dr kajii ko da matsala."

Sageer yace "To Ummy, amma muje ciki ki zauna tukun na."

Hassan na shiga ya zauna a kasa jikin gado ya jinginar da kansa a jikin gado.

Jalila ta tsaya a bayansa ta rasa ta ina zata fara mai magana, ta dade a tsaye dan tayi wajen minti ashirin kafin ta juya jiki a sanyaye, hannu yasa ya riko hannu ya riko hannunta ta baya.

Juyowa tai da sauri tana kallansa, haka suka tsaya hannunsa na rike da nata ba kuma wanda yana wani magana, har na tsawon minti goma sha biyar, kafin ta tsugunna jin kafarta na dan zafi, ji tai ya saki hannunta.

Kallansa ta sakeyi sannan tace "Yaya jikin ne ko wani abun ne ya faru?"
Bai kalleta ba, sai dai yanzu ya mike daga kasan da yake ya zauna akan gado.

Sannan ya kalleta, idanunta na kansa ta kara cewa "yaya!"

Kallanta yai sannan yace " are u worried about me? Or are u scared?"

Ta kalleshi tace "Yaya dan Allah kadaina min tambayar nan, dan bansan me zance ba."

Yace "okay, jeki to."
Tace "naam?"
Yace "ba fita zakiyi ba na tsayar dake?"

Kallansa ta sakeyi tace " Yaya."

Kallan daya mata ne yasa ta mike tai waje jiki a sanyaye.

Zama tai a falon tana tunanin abinda ya faru yanzun nan, ya riketa sannan yace jeki, mekenan? Itakam tana kasa ganeshi wani sa'in.

**********

A Abuja kuwa Abba na gama waya ko kallan Hafiz baiyiba ya fada motarsa yai gaba hankali a tashe, kayansa kawai ya dauko a dakinsa sannan yai check out ya fito tare da ajiye motar.

Airport ya nufa dan hankalin sa a tashe yake, yana zuwa yai sa'a akwai jirgin da zai tashi karfe 3:00pm zama yai yana jira sai dai zuciyarsa ta kasa nutsuwa.

Lokaci nayi kuwa ya mike da sauri, ba nisa daga Abuja zuwa kano a jirgi kan kace me sai gasu sun sauka.

Bai tsaya neman Mamman ba kawai ya hau taxi zuwa gida.

Ummy na kwance a falo, tayi shiru tana tunanin Hassan, tana jiran dawowar Sageer daga gun Dr.
Jin an taba kofa ne yasa ta mike da sauri dan ta dauka Sageer ne.

Da sauri ta bude kofar tana cewa “Sageer me Dr din ya.......”

Ganin Abba yasa ta tsaya da maganar tana kallansa, kafin tace “ Sannu da zuwa.”

Kallanta yai jiki a sanyaye yace “Yauwa, sannan ya fara kokarin shiga ciki.”
Hannu tasa ta amshi jakarsa tai gaba fuskarta ba walwala.

Kallan falon yai sannan ya kalli hanyar sama, kafin yace “ina mutanen gidan?”
Tace “Ameera tace sai jibi zata dawo, Sageer ya fita.”

Yace “Jalila fa?”
Tace “Tana sama.”

Yace “Hassan fa? Ya jikin nashi?”

Kallansa tadanyi kamar zata fadamai sai tace “da sauki.” Sannan tai gaba.

Ba abinda yakesan ji ba kenan, so yake yaji ko wani abun ya faru dashi, sai dai baisan ta ina zai fara ba shiyasa yai shiru.

Ummy tana ajiye mai jaka ta juya zata fita, har takai kofa yai sauri yace “ kinje taron kuwa?”
Kallansa tai tace “banje ba.”

Yace “Naga kamar bakya farinciki da dawowata.”

Wani murmushin takaici tai kafin tace “banasan musu ko fada dakai daga dawowarka, mu bar maganarnan, kai wanka kafin ma shiryama abinci.”

Kallanta yai hartabar dakin, zama yai a bakin gadon sannan ya sa hannayensa ya rufe fuskarsa.

Jalila kam ganin hankalinta ya kasa kwanciya yasa ta mike ta kara turo dakin a hankali.
Yana zaune yasa farcensa yana karzar bayan hannunsa, idanunsa nakan bango yana tunani, idanunsa da fuskarsa a hade suke.

Jalila ta shigo ciki, har taje kusa dashi bai san tazo ba, hannunsa ta kalla taga yana ta karza har yaji ciwo ga jini nan.

Kallan tsoro tamai sannan tasa hannunta agun dayake karza, tana kallansa.

Dagowa yai ya kalleta sannan ya kalli Hannunta sannan ya kalli nasa hannun, sake kallanta yai sai dai yanzu idanunsa sun canza.

Idanunta ne suka ciciko tace “Yaya wani abun ne yafaru ko? Menene dan Allah? Ko akan abinda na fadama ne?”

Hannunsa ya janye sannan ya mike daga kan gadon zai nufi toilet.

Tace “kayi hakuri dan Allah, laifinane dana sani ban tsaya naji abinda suke cewa ba, sannan dana sani ban fadama abinda ke faruwa ba, kayi hakuri dan Allah, it’s all my fault.”

Tafada tare da share kwalla.

Juyowa yai ya kalleta kanta na kasa, tana share hawaye, ya dade yana kallanta kafin yace “ ba akanshi bane, sannan in ma shine ba laifinki bane laifinane tunda ni na matsa miki sai kin fadamin.”

Kallansa tai sannan tace “ akansa ne ko?”

Kai ya girgiza mata alamar a’a sannan ya shiga toilet.

Kallansa tai sannan tai ajiyar zuciya tace “Goggo ya zanyi? Inaji nayi laifi ga wanda zai taimakeki, na tambatar da ban fadamai ba kila yau zai dauke ki daga asibitin sai dai da alama wannan bakin nawa ya ja min........

**************

Inna ce ta kalli Dady tace “Abakar!”

Kallanta yai sannan ya amsa, tace “ sai yaushe zaka gidan Jalila?”
Yace “so nake sai Taura ya dawo, naji ance yayi tafiya.”

Tace “meye damuwa ta da haduwarka da Taura?”

Dady yai kasa dakai yana cewa “ai kinga ya kamata mu sake mai godiya da taimakon daya mana.”

Inna tace “wace godiya bayan abinda muka aikata yana neman wargajewa saboda shirmanka.”

Dady yace “Inna ni......”
“Dalla rufemin baki, so kake kace ba laifinka bane? Ka tabbatar ka lalabata da mijin nata, dan kafi kowa sanin dayan plan dinmu da mukesan sake bude wani branch dinmu, ka kuma tabbatar inba da taimakon Taura ba abin nan bazai yiwu ba, ya kamata kasan abinyi, kafin ni insa hannu, kasan in nasa bazata ma kyau ba.”

Dady yace “To inna.”

Ta kalleshi sannan tace “tashi kaje, ka kuma tabbatar kaje gun Jalila, dan a yanda na ganta da yaran nan ina tsoro karta fadamai komai, wannan yaran idanunsa kadai zaka kalla zaka fahimci ba kara a idanunsa balle ya mana.”

Yace “to sannan yai waje.

Shiru tai tana sake wani tunanin, yanzu me ya dace tayi??????

(Nace “ kya tambaye ni😏”)

*********
Sageer ne ya kalli Dr yace “kana nufin hakan alamu ne na samun nasara?

Dr ya kalli Sageer sannan ya jinjina kai yace “Sageer kasan Hassan yana dauke da trauma ne wanda shikadai yasan abin da kuma faruwar abin, tunda abin ya faru ka taba gani yayi ihu ko fada da karaji?”

Sageer yace “a’a sai dai zafin rai, rashin magana da kadaicewa, sai kuma rashin nuna emotion na farin ciki ko na tsantsan bakin ciki a fuskarsa, a koda yaushe fuskarsa a hade take wanda yake nuna alama ta bakin ciki ba alama na canji.”

Dr yace “Good, yau kuma fa?”

Sageer yace “ yau yayi kara sannan kana kallansa kasan ransa a bace yake wanda bacin ran ne da alama yasashi yin karan.”

Yace “Very Good, ka gano improvement?”

Sageer yace “na fahimta Doctor, a da yana fada sai dai bawai da jikinsa yakeyi ba, ko zuciyarsa yanayi ne da fuskarsa da bakinsa.”

Yace “Very Good ka fahimceni yanzu?”

Sageer ya daga kai cikin gamsuwa da jin dadi yace “nagane Dr, na kuma gode sosai.

#OneLuv💕

🗯 *JALILAH* 🗯

Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*

     *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
  (_D home of expert and perfect writer's_💡)

*38*

  Saukowa kasa tai, tana matatakalar karshe, taha an bude kofar dakin Ummy, tsayawa tai tana jira Ummyn ta fito sai ta karaso.
Ganin Abba tai ya fito daga dakin, mamaki ne ya kamata da sauri ta karaso dan yana fitowa suka hada ido, tsugunawa tai ta gaisheshi.

Kallanta yai bayan ya amsa yace " Jalila Hassan yana sama ne?"
Tace "eh."

Da sauri ya wuce ta ya nufi sama, bata kawo komai a ranta ba kawai ta wuce falo.
A kitchen taji Ummy nan ta nufi gunta, tanashiga tace "Ummy ashe Abba ya dawo?"

Ummy ta juyo tace "eh, ya jikin Hassan din?"

Jalila tace "da sauki." Ta fada tare da karasawa gunta tana neman taimaka mata gun rufe kullar da ta gama zuba ma abinci."

Ummy tace "dauki abincinku la'asar har tayi ba wanda yai lunch."

Ta amsa da to.

Abba kam dakin ya karasa yai knocking din kofar, Hassan daga ciki ya fito daga toilet kenan daure da alwala ya bude kofar.

  Tsayawa sukai yana kallansa hannunsa rike da kofar, fuskarsa kuwa ya kara hadeta tamau, Abba ya kalleshi yace " Hassan baka ganni bane?"

Hassan ya saki hannun kofar baice komai ba ya wuce ciki.

  Abba ya shiga dakin sannan ya maida kofar ya rufe, yace "Kayi mamakin ganina ko? Bayan dazu mukai waya."

Hassan bai kalleshi ba balle yai magana, Abba ya zauna akan sofa sannan yace "Hassan!"

Hassan ya juyo ya kalleshi da jajayen idanunsa, yace "How can u? Of all people?"

Abba ya runtse idanunsa cikin takaici sannan ya mike ya kamo hannun Hassan suka zauna akan kujerar.

Hannayensa na cikin na Abba yake kallansa, Abba yai shiru kafin yace "Hassan."

Hassan ya kalleshi cikin takaici sannan ya zare hannunsa daga nashi yace "Zina kake?"

Abba cikin mamaki ya kalleshi yace "Hassan wani irin magana kakeyi haka? Taya zaka cemin ni mahaifinka? Ka kalleni kace zina nake?"

Hassan ya mike tsaye tare da dan matsawa daga inda yake yace " Ni kaina ina fatan hakan ya zama laifi ne na aikata."

  Abba yai shiru yana kallan Hassan, gaba daya ma ya rasa ma mai zaice.

Muryar Hassan yaji yace "wacece?"

Abba yai shiru tare da shafar fuskarsa, Hassan ya juyo ya kalleshi cikin bakin ciki yace "Budurwarka ce?"

Abba yace "Hassan ni kaina ina mamakin kaina, wai nine nakesan........"
Chapter 39 · 0% Book details