← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 93

Sashe 92

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bya samu cigaba sosai acikin shekara shiddan nan da ta gabata ya kai Baba Makka har da Magajiya ta je ta sauke farali, Sannan gidan wanzamai a garin gombe da ke anguwan arawa in kasan gidan a baya a yanzu in ka so ba za ka gane gidan ba, an buge shi an gyara shi zuwa na zamani har da katon get. bangaren Magajiya an haɗe mata har da in da Maeesha ta tashi a ka mata flat mai girma sannan itama Maeeshan can bangaren an haɗe mata na in da Inna ta tashi ya zama Flat mai girma sannan kuna bangaren su Gaje man an maida shi na zamani sai wanda ya gani, gidan ya fita dabam a anguwa saboda kyan shi sannan ya gyara masallacin kusa da su an yi masa bene ya koma na zamani, sannan matasa anguwa da sauran jama'a ya na taimakon su daidai gwargwardo ba ma iya anguwansu ba kaf kafatin Gombe da kewayenta suna alfahari da samun zaƙwaƙuri daga jihar su. Har can gidansu na mallam Sidi ya gyara ya maida shi na zamani Yalwa dai an gama jinya an koma ga Allah ya ba ma Baba karimu jari mai kauri yana kasuwanci.

Inna kuma ta je saudiya sau biyu sannan ta je Umra, Mu'azzam ya samu karin girma an sake cilla shi kaduna shima yayansa uku, su Bintu kuma dukkansu suna cikin rayuwa mai kyau, Aji ya ba ma kowacce jari suna kasuwanci, Auwalu kuma ya zama babban Enginer har gidan kansa ya yi shi kuma Saddiqu na zama a shagon da Mimi ta buɗe na Abaya da Takalma da Jaka mai suna MIAJ STORE shima yana saida jallabiyan maza da huluna ba ta masa mugunta yana samu sosai ya na rufa ma kansa asiri. Aji ya siya mata sabuwar motar ya yi mai kyau sannan ya siya ta yara wacce ake kai su makaranta har Inna ya siya mata mota ya kuma ɗaukan mata direban da zai riƙa zirga zirga da ita, tsohuwar motarsa kuma ya ba ma Baba ita, mashin ɗin kuma aka siyar sai a siya ma baba Danlami da Baba Sani sabbi suna hawan su, babu wanda Aji bai taimaka ba adanginsu ba, Mu'azzam ma yana iya bakin ƙokarin shi. Tunda bai kai Aji samu ba shi da a wata yana samun sama da Miliyan albashinsa( ba ƙarya ba yan kwallo suna samun mahaukata kuɗi balle shi Aji da kasa ke alfahari da shi).

Gidan gwammatin Gombe ba ya da shamakin shiga haka ma can Villa a garin Abuja, sannan ya zo ya na taimakon Gombe United camp din su, su zinder suma duk sun samu cigaba sai wasu ne eake cigaba da rain sannan har Coach ɗin su bai manta da shi ba alheri daidai gwardo yana yi masa. Shi dai burinsa matasa su cika burinsu, har Team na shi na musamman ya kirkira daga anguwan Arawa mai suna M.I AJI ARAWA TEAM, jaririya ce horar da matasa ake yi masu sha'awan ƙwallon kafa.

Kaf ƴayan nan huɗu a gombe Mimi ta haife su, sai karamin su ne Mu'azzam ta haife shi a garin Abuja ko da yaushe Aji na kan hanyar zuwa ya gansu ko kuma in sun samu hutu su je ita da yara, Inna ta gaji da zirga zirga ta zaunar da shi ta ce ta yafe masa ya ɗauki iyalansa zuwa in da ya e zaune domin Mu'azzam ne ya gaya mata abunda ya sa Ajin ya ƙi maida Mimin can Abuja gaɓadaya, lokacin daman an maida ta Editer a ma'aikatansu na karamchi ta daina karanta labarai Office gare ta duk ta dalilin Aji domin kishinsa bai ragu ba, sai ma abin da ya karu, dole ta ijiye aikinta ta tattara ita da yara suka koma Abuja gida kuma sai megadi tunda in suka zo garin nan suke sauka har Mu'azzam ma yanzu ya mallaki gida an garin Gombe. Su Nasir ma duk sun samu cigaban rayuwa, amman duk da haka Aji bai manta da su ba ana tare har yanzu kamar baya sun zama manyan mutane sun girma sun yi 6aƴa girma ya kama su shekaru sun ja, A shekaran da ta Mimi ta koma Abuja suka je suka yi aikin Hajji tare da Aji a kuma wannan lokacin tana karatunta na Phd ta online a wata jami'a a america sannan gefe ɗaya ga kasuwaancinta yanzu kai tsaye take oder kaya daga India ko Dubai.

Da kyakyawan takardunta da ƙwarewanta wajen aiki ta samu aiki a NTA Abuja matsayin News Editer again, burin Aji ya cika an daina nuno fuskarta ta daina karaɗe duniya ya zama shi kaɗai yake kallonta ya na jin daɗi, ya na nan faɗacin sa amman kuma rayuwa tasa ya rage wasu abubuwan sai mai hali baya fasa halinsa, kuma hausawa sun ce hali zanen dutse. sannan itama Mimi ta nan a yadda take yar gayu mai kyau domin ba ta amince ta bar jikinta ya lalace ko da yaushe cikin gyara take, tunda ta rike surayya dee mai gyaran amarya da uwargida ta zama tauraruwar mata a zuciyar Ajin ta.+234 803 277 3332
Nemi Surayya dee Bojuwa domin dacewa da sahihin kayan gyara.

Sannan bayan haihuwan Mu'azzam ta so yin tsarin Iyali Aji ya ce bai amince ba dole ta haƙura, saboda in ma ta je ta yi wani abu ya faru ita ta sani. ƙaton gida Aji ya siya musu mai kyau da tsari duk da suna ɗan nesa tsakaninsu da Mommy ba ta damu ba tunda ai suna gari ɗaya a kallah dai ba za ta yi zaman kaɗaici ba.
Khadi ma ta na can an zama uwar garke itama yayanta biyar Madiha ce yan boko Æ´aÆ´anta uku ba ta kara ba, mataimakiyar shugaba ce ta kanfaminsu kuÉ—i sun zauna musu, Rukky ma yayanta biyu suna Lagos suna aikin su ita da mijinta Jaheed.
Mommy sun aurar da Asma'au a garin Jigawa ita da Baba Alƙali, Walida dai ba ta yi aure ba ta samu jinkiri amman tana cigaba da Masters ɗin ta a kaduna state University KASU, ta na kuma zaune tare da su Mu'azzam har lokacin. amman ta samu miji anan kaduna tare suke masters ɗin su har yazo gida manyan sun shiga mganar.

Hajiya kuma ta na nan da ranta tsohuwa ce mai ran ƙarfe. Daddy ma rayuwa ta inganta hankula sun kwanta duk da ba dari bisa dari ake samu ba amman an gode ma Allah tunda daman ba lalle sai ka samu abin da kake so ba.
Mimi sun shekara a Abuja Gombe sai dai sallah ko wani abu ya faru. zuwan su na karshe sun je sallah sun dawo saboda makaranta yara, fati ne kawai da Mu'azzam basa makaranta Ummi yar primary 2 ce sai Babangida 1, sai batul ta na Nursery sectiion ne, itama bayan sun dawo Abuja ne a ka saka ta tare da su Ummi a makaranta mai tsada ta Æ´aÆ´an gata.
A shekaran da ta shiga ne za'a buga World Cup kuma Nageria tana ciki ana ta shirye shirye wannan shekaran a Agentina za'a buga ƙwallon duniyan gabaɗaya.

******

*MURFI.*
_ABUJA, 99POBOX MAITAMA._
*202....*

Gidan na su Mimi cike da baki mutanen Gombe da mutanen kaduna har da ma Abujan gabaÉ—aya.Saboda ta ya murna ga É—an wasan kwallon kafa ta kasa wato MANSOOR IBRAHIM AJI bisa nasaran da suka samu na hayewa matakin karshen na cin kofin duniya sai dai sun ci É—aya kodubuwa suka cire su amman duk da haka Nageria take murna da alfaharin wannan nasara da suka samu, tun suna can Argentina murna ya zagye kasa baki É—aya yau jirgin su zai sauka, kuma walima ce Mimi ce ta shirya Aji bai ma san da ita ba.

Mu'azzam da matarsa Hibba da Yayansu sai Nasir da Makama da Ahmad duka da matansu da yayansu, su Binti su Yaya Amina Inna ce kaÉ—ai ba ta zo ba su Auwalu da matan su har da Saddiqu, Khadi ita da Mijinta da yayanta har da Dr tare da Jawahir suma da yayansu su Madiha ne kaÉ—ai da Rukky suna can Lagos ba su taho ba amman suna ganin komai a waya. Gida ya cika manyan mata suna gefe suna hira mazan ma suna yin na su na dabam yara kuma suna ta wasannin su duk abin da za'a ci a sha duk Oder su suka yi an riga ma an kawo an gabaÉ—aya gidan an cika shi da Bloon da fulawas da kuma wani katon Allo an rubuta WELCOME BACK CAPTAIN MANSOOR AJI.
Wani kuma an rubuta CONGRALATULATION OUR NIGERIAN CHAMPION.
Wani kum an rubuta ISSE GOAL AJIN FROM NAGERIA.

Kuma a tsarin nasu da yara ne su Ummi da Junoir za su jere a layi da symboll É—in in ya iso so zuwa tarbansa amman kuma sai ya ce sai sun fara biyawa ta gidan Shugaban kasa tunda shugaban kasan da kansa da wakilan gwammati za su tarbesu sai suka hakura amman suna gida suna ganin komai a kafafa sada zumumta suka ga saukan su ga Aji nan sanye da riga fara mai ratsin green da fari haka wandon ma mai ruwan ganye sun sauko suna rike da tutar Nageria bakinsu har kunne amman ban da angon Fatima fuskar nan ko da yaushe dai kamar yadda kowa ya sani,suna tashan yabo da addu'o'i kuma ma abun alfahari kwallo É—aya nan ma da suka ci Aji ne ya samu nasaran je fa ta a raga. Sai ki ka ga kasa ta ruÉ—e da kirarin AJI IS A GOAL ko Mimi ma haka ta saka a status É—in ta bayan ta saka hoton shi da ya tura mata a can Argentina É—in tunda Nageria ita ce ta yi na uku sun dawo tare da kambun girmamawa .
Chapter 92 · 0% Book details