← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 93

Sashe 8

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Hajiya ta ce"A'a Hamza abun bai dace ba ka yi hakuri a bi komai a sannu mana"
Daddy ya mike ya na gyara  babban rigansa lokaci ɗaya yana faɗin" Hajiya kar ki hanani shiga wannan mganar, ki duba mganar yarinyar nan gabaɗaya gani yake ba ta da wani daraja a wajenza tunda mun bi umarninsa mun aura masa ita ai bai eahala ba tunda har ya ke fama da jin kai yana cewa gwara ta tafi ɗin zai gane a baya alfarman ki yaci yanzu ne zai gane shayi ruwa ne, Mimi ki daina kuka sha kurimin ki kin ji?
Sai ta gyaÉ—a masa kai kafin ta ce" Daddy a kwaso min kayana."
Kai tsaye ya ce"Dole ai akwai sabon zama, in har ya na son auran ku muma sai mun zuba masa namu sharuÉ—dan ciki har da gama zaman ki a wannan gidan nasu zan yi magana da Maman yara duk yadda ake ciki za ta kira ki zuwa gobe za'a dawo miki da komai naki gida in sha Allahu."
Sai Mimi ta ji dadi acikin ranta domin gwara dai kowa yasan ita kan ta gama zaman aure da Aji.

  Hajiya kuma sai cewa take yi a bi a sannu amnan Daddy ya ce wannan karon Hajiya ta cire bakinta gani ya yi kamar sun ba shi auran bai wahala ba.
Mimi tana tunanin in da ta zauna ta faÉ—a nusu yadda ya tafiyar da ita tun farkon auran fa? Da mganganun da yake gayamata da zarafin iyayenta da yake ci? Ta tabbata sai sun ji sun tsane shi shi ya sa ta sakaya maganar.
Bayan tafiyar Daddy Hajiya ta dawo tana nuna ma Mimi illar abin da za ta aikata amman ta ce ita fa tana kan bakanta, abun haushima shi fa bai ma san ya aikata ba dai dai ba sannan ita ba za ta cigaba da zama da mara afuwa ba, sannan ba za ta iya zama da wanda bai iya sarrafa zuciyarsa ba Sannan da bakinsa ya ce baya sonta ba ta ga amfanin zamanta ta da shi ba.

  Zuwa da safe dai tuni mutanen dake kusa susan Mimi na gidan Hajiya, Mommy ma ta sani saboda Hajiya da kanta ta kirata ta sanar da ita abib da ke faruwa ta ce za ta shigo Gombe cikin satin, sannan bangaren Daddy kuma da ya koma ya tattauna da Mama itama ta ba da hoyan bayan haka, ta ce haba auren ai ya yi kaskanci ba Dole ya yi abin da yake so ba saboda an ba shi Mimi kamar sadaka.
Ita ta kira Jaheed taa gaya masa abin da ke faruwa ya yi mamaki kwarai.Har Maman na zolayanshi da cewa ƙila in da rabo Mimi rabon shi ce nan da nan farinciki ya cika zuciyarsa.

  Kuma Daddy ya ba da umarnin a nemo mota a je a kwaso duka kayan Mimi a kai mata gidan Hajiya, amman ko shi a cikin ranshi ba shi da niyar kashe ma Mimi aure ita kanta a mganganunta fushi ne kawai amman tana son mijinta kuma shima yana sonta amman girman kai ne ya hana shi zama ya fahimci yadda zai iya nuna ma mimin so. Shi ya sa ya zaɓi ya yi amfani da karatun siyasar sa ya gyara auran Mimi sannan ya cire wannan jin kan da fushi daga zuciyar Mansoor ba tare da ya bari ko Mimin ta san ga manufarsa ba.

*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3003*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

Daddy na yi ma Mama maganan kwaso kaya ta kira ƙanwarta Hajiya Turai suka yi maganar ta nema musu mota, Har tana ƙyanƙyasa mata abin da ya faru Hajiya Turai ta ce"Haba ni fa daman na sani duk burgan banza ne, yarinyar nan ba za ta iya zama a wannan gidan ba."
Mama na ƴar dariya ta ce"Uhm to ai komai ya ƙare" ita kamar har wani jin daɗi take yi ita da suka yi mgana da Daddy sai ga shi har Antyn yara sai da ta sanar mata da ga abin da ke faruwa kowa ya ji sai ya ce gaskiya daman wannan auran na Mimi sai a hankali.

  Jaheed ya fi kowa murna da faruwar haka, Tun bayan auran Mimi yake cikin garari, sai dai kule kulen ƴanmatan zamanin nan da ba ka raba Mazan zamani da shi, bai san Yaddiko ba ta sani ba sai da ya kirata ya gaisheta kawai ya faɗa mata saboda ya san tana goyon bayansa ko a baya aiko nan da nan ta ce ba ta sani ba amman anjuma za ta leka gidan Hajiyan ta ga abin da ke faruwa, Lamarin ya daure mata kai, ita fa ba ta son ta ga mace da ƙuruciyarta tana bin ɗakuna in ya zama jiki bshike nan duk in da ta yi aure ba za ta zauna ba.
Da daddare ta saka Æ´aron makotan su ya kawo ta gidan Hajiya, Ta kuma gasgata abin da Jaheed É—in ya faÉ—a mata tunda ta ga Mimi a gida sannan da ta yi mganar ba'asi Domin sai ta nuna Kamar ba ta san abin da ke faruwa ba.

  Nan Hajiya ta yi mata bayani da zuwan Daddy jiya da maganar da ya yanke a kan Mimi ɗin, Yaddiko ta gyara zama lokaci ɗaya ta na faɗin" Haba Hajiya me ya sa za ku biye mata? Tun farko sai dai a ka nuna mata ga Ɗan'uwanta ta dage sai abin da take so an kuma yi auran nan amman kawai sai ta kamo kafa ta dawo ta ce ta hakura da zaman aure? Haba dai Hajiya ai ya kamata ku ma ku zauna ku yi tunani kar ta maida mi kananun mutane mana"
Hajiya ta kalleta kafin ta ce" To yanzu tunda mu ba mu iya ba, ya kike son ayi?
Kai tsaye Ta ce" A kira shi mijin nata Yaya ya zauna da shi sai a ji shima ta bakinsa."
Hajiya ta gyaÉ—a kai kafin ta ce"To kuma har yanzu bai zo kuma bai kira waya ba, shi kuma Hamza ya ce ba wanda zai neme shi."
Sai Yaddiko ta yi shuru ta kasa mgana Hajiya ta cigaba da faɗin" Ba na nufin Auran Binta ya ƙare har ga Allah Yaddiko.  Amman mu ba su lokaci mu gani ina ji a jikina ko ba yanzu ba nan gaba kaɗan za su daidaita in sha Allahu."
Yaddiko dai ba ta kara mgana ba saboda ta ga Kamar wannan karon ma Hajiya tan goyon bayan Bintar ne.

  Kuma ba ta hakura ba da za ta tafi, sai da ta leƙa har ɗakin Hajiya ta na ce ma Mimi" Binta rayuwar nan ta aure duka fa hakuri a ke yi, ke shaida ce irin hakurin da Murja ta yi da Yaya Allah ya jikansa da ba ta yi haƙuri ba,da ba ku ta shi kun ga iyayen ku waje ɗaya ba, kowa ki ka gani a gidan auran shi ya na zaune to karki so ki ji irin haƙurin da yake yi a zamantakewarsa, in ka ji na wani sai ka ce naka nafila ne, auran dai kika na ce kina so kuma a ka bi abin da kike so a ka baki shi sai kawai aure ko shekara bai yi ba sai ki dawo gida ki ce ba za ki koma ba? Kar  fa saboda kin ga ana bin abin a kike so ki riƙa zuwa mana da renin hankali aure ibada ne ba wajen wasa ba."
Har Yaddiko ta gama maganarta Kan Mimi na ƙasa ta kasa mgana sai dai Idanuwanta sun tara ƙwalla ai ba ta da wani ikon kare kanta yanzu shiyasa ta yi shuru.

  Yaddiko na fita ta koma ta kwanta tana kuka, Mommy ma da safe ta kira ta tana yi mata faɗa akan wannan abin da ta yi har ta na cewa ta shirya ta koma gidan Mijinta,  ita kuma ta saka mata kuka cewa ba za ta koma ba ta yi ma Daddy magana kuma shi yace ta zauna. Da Mommyn ta kira Daddy bai saurare ta ba ya ce in ta samu lokaci ta shigo Gombe su tattauna da haka suka rabu da juna, Mommy da kanta ta sanar ma Khadi, ita kuma khadi ta sanar ma da Dr . Sulaiman da Madiha a bakinta suka ji L
labarin abin da ya faru tun daga lokacin suke rige rigen kiran wayarta amman ba ta É—auka ba, Madiha ma ba ta kira ba cewa ta yi daman ta faÉ—a ma Mimin ba abun kunya ba ne in ta dawo gida ta nemi Saki, ita kuma Khadi kanun zencen ta ke so ji.
Dr. sulaiman kaÉ—ai ta daga kiransa suka yi magana shima dai bakinsu É—aya da Mommy in ma wani abu take so ta yi mgana a yi mata amman ta bar mganar kashe auranta gwara ta koma zai fi mata alheri.
Chapter 8 · 0% Book details