← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 93

Sashe 69

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Suna ta fe Mimi na masa ƙwatance har ƙofar gidan Inna Meri, Jaheed ya bi gidan da kallo kafin ya ce"Nan ne gidan?
Sai ta kaÉ—a masa kai ta na share hawayen fuskarta da mayafinta lokaci É—aya tana faÉ—in" Eh nan ne Mahaifiyarsa ke zaune."
Sai suka yi shuru gabaÉ—aya. Jaheed ya mika mata jakarta da ledar mganinta kafin ya ce"Ki kula da kanki, kinsan dai ba ki da lafiya."
Ta buɗe baki za ta yi mgana da sauri ya tare ta da faɗin" Na sani ba zan gaya ma kowa ba. Ciki ko har da  Rukayya, ba na fatan na zama silar samun matsala ga auran ki, ki yi masa bayani in ma bai yarda ba akwai Rukayya ita za ta zama shedarmu."
Wani mirmishin takaici Mimi ta yi kafin ta ce"Kada ka damu ba abin da zai faru. Na gode kwarai ka gaida su Daddy."
Da ga haka ta buɗe mota ta fita. Ta ɗaga masa hannu shima ya ɗaga mata sannan ta juya tana tafe a hankali jiri ma take gani, mamakin ta wai tana ciki? Bayan ɓatan watan nan ba ta fahimci wani alamun tana da shigar ciki ba sai yau da zazzaɓi ya rufe ta.

  Gidan ya na buɗe sakayawa kawai a hankali ta tura kanta ta shiga  yamma ta yi tunda shidda saura ne, Inna Meri na tsakar gida tana kwashe shanyar zogalan da ta zo da ita daga can gida ɗanya shi ne take shanyawa tare yakuwa, ganin mangariba ta kusa yasa ta fito tana kwashewa. Tana duke ta na tsince na kasan da ya zube lokaci ɗaya tana sakawa cikin farantin gabanta,  ba ta ji sallamar Mimi na farko ba sai da ta ƙara yi sannan ta ji ta, da sauri kuma ta ɗago kanta tana kallon Mimi take tafiya dakyar kamar za ta faɗi, Cikin mamaki Inna Meri ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin" Binta?  ke ce da yamman nan?
Kalamanta sun tsaya sanda ta ga Mimi ta dafe kanta. Jakar hannunta ta sulale tare da ledan mganinta wani irin juwa ce ta kwashe ta za ta kai ƙasa cikin zafin nama Inna Meri ta tare ta lokaci ɗaya tana faɗin" Subhanallah Binta ba ki da lafiya ne?

  Ba mgana sai kawai Mimi ta saka mata kuka, Inna ta ruɗe ga shi ita kaɗai ce a gidan Walida ba ta dawo daga wajen koyon ɗinki ba. Sai ta rike Mimi ta taimaka mata zuwa cikin falo ta zaunar da ita a kan Kujera, amman sai ta koma ta kwanta Inna Meri ta yi mata zuru tana kallonta lokaci ɗaya da nazarinta ba ta raba ɗayan biyu Fitinannen yaron nan ne ya yi wata tsiyar, Sake fita ta yi ta je ta kwaso jakan da ledan mganin ta duba daman ai daga ganin Binta ba ta da lafiya duk ta wani ɗashe, Inna ba maganin ta gani ta fahimta ba ita fa uwace tun lokacin da ta dawo Mimin ta zo mata sannu da zuwa ta ga yadda ta yi wani fari ta ga alamun Bintar na da shigar ciki, kuma a tunaninta daman dukkansu da ga ita har Baban Inna ba su san dashi ba.

  Falon ta koma ta iske Mimi na rawan sanyi sai ta shiga ɗakin walida ta ijiye mata jakar da kedan ta ɗauko mata blanket bargo ta rufa mata sai faman jera mata sannu take yi, ta koma ta kashe fanka  falon sannan tunda mangriba ta kusa. Sai ta saki labulayen falon ta kuma rufe ƙofar falon da Window saboda ɗakin dai ya yi ɗumi, kitchen ta shiga ta kunna gas tunda ta iya sai ta ɗora ma Mimi ruwan zafi ta samu ta yi wanka ta gasa jikinta sai taci wani abu ta sha mgani ruwan na tafasa ta fito falon sai ta isken Mimin na barci sai ta kyaleta.
Har a ka kira mangariba tana barci Inna Meri kuma ba ta tashe ta ba. Ta shiga ciki ta ɗauro alwala ta zo nan falo ta shimfiɗa sallaya tana cikin sallar ne Walida ta shigo gidan Inna ma jin ta tana faɗin"Laa Anty Mimi' Sai kuma ta leƙa ta kafin ta ɗago tana kallon Inna, goshinta ta taɓa ta ji da zafi kaɗan sannan ta ga tana zufa.

"Inna Anty Mimi ba ta da lafiya ne?

  Innar na sallah ya sa ta san ba za ta samu amsarta ba. Sai ta kwashi hijabinta da jakarta zuwa cikin ɗakinta ta na shiga ta ji ana ta kiran waya a jakar Mimi ta gani yasan ta san wayarta ce ta buɗe kenan ta ɗauko wayar ta ga an saka Baby kafin ma ta yi wani abu wayar ta ɗauke da alamu ƙila ba chaji ne, ba ta yi tunanin saka mata chajin ba sai dai ta maida mata wayarta cikin jaka, ledan maganin ta ɗauka ta duba abun ya ba ta mamaki Yaya Mansoor ya yi tafiya ne? In ba haka ba me Anty mimi ke yi a gidan nan a dai dai wannan lokacin?
Ba ta da mai ba ta amsa ba ya sa ita ma ta sauke kayan hannunta ta faɗa tiolet ta yi alwala ta zo ta yi sallah tana cikin tahiyar karshe ta ji Inna na ƙwalamata kira shi ya sa tana sallamewa ta fice zuwa falo tana ce ma Inna ta na sallah ne lokacin da take kiranta.

  Inna Meri ta kalli Mimi da ta farka ta janyen bargo daga jikinta saboda zazzabin ya sauka zafi ma take ji, cikin tausayawa Inna ta ce" Sannu Binta ya jikin?
Mimi kamar mai ciwon baki ta amsa ma Inna da sauƙi, Walida ma ta karisa kusa da ita ta zauna lokaci ɗaya ta na faɗin"Anty Mimi Allah ya baki Lafiya.".
Ta amsa da Amin idanuwanta sun tasa abun ka ga farar fata duk fuskarta ta bayyana halin da take ciki.
Walida Inna Meri ta kallah kafin ta ce"ki je kicthen na saka mata ruwan zafi ki sake ki kai mata bayi ta samu ta yi wanka ko jikin nata zai saki."
Daman abin da Mimi take bukata kenan wanka, da sauri ko Walida ta mike ga aikin da Inna ta sakata. Sai falon ya yi shuru Inna sai ta maida hankalinta kan laziminta amman tana ganin Bintar na share ƙwalla, tausayinta ya kamata wai har yaushe ne Baban Inna zai bar rayuwar ƴar mutane ta zauna cikin salama ne? Ta san wlh tsiyar shi ce amman bari Bintar ta natsa ta ji abin d kuma ya sake aikatawa wannan karon.

  Bayan Walida ta kai mata ruwan zafi saboda jikinta ba karfi, ta mike Walida ta riketa hannun da a ka yi mata karin ruwa har ya kumbura da walida ta taɓa wajen sai da Mimi ta yi wash, cikin sauri walida ta saki hannu kafin ta ce"Sannu ƙarin ruwa a ka yi miki?
Mimi ta gyaɗa kanta kafin ta ce"Daga wajen aiki ne na fara ciwom sai Rukayya ta kaini asibiti can na yini aka sakamin ruwa da Allurai." Inna Meri da Walida suka haɗa baki wajen faɗin Allah ya ƙara lafiya.

  Cikin kayan Walida. Walidar ta zaɓo mata wata doguwar riga, da yake daman rigar ta mata yawa ta kuma san za ta yi ma Mimin,Ai ko ta ji daɗin gasa jikinta sosai sannan ta ɗauro alwala salla tun ta asuba rabon ta da yi, rigar ta saka ta yi mata sai dai tsawon ne ya yi mata kaɗan sai ta ce Walida ta bata zani ta ɗora saman rigar ta yi salla kuma Alhamudulillah a tsaye ta yi sallar tunda ta samu sauƙi tana idarwa Walida ta kawo mata Tea mai ƙauri da buredi ta sha, sai ta fara dawowa daidai, bayan tea ta  dafa mata Indomie da ƙwai taci ta yi kat sannan ta sha ruwa, ba ta da alwala ya sa ta koma Tiolet ta yi alwala ta zo ta yi sallar Isha'i ta sha mganinta sannan Walida ta gyara mata gado ta hau ta kwanta, Inna Meri ta zo ta dubata ganin har ta kwanta ya sa ta kyaleta ta huta zuwa da safe.

  Walida ce ta kasa hakuri ta koma falo tana faɗin" Inna wai anan Anty Mimi za ta kwana? Inna ta amsa mata da eh, cikin ƙarim mamaki ta ce"To ko Yaya Mansoor ya yi tafiya ne?
Inna ta kalleta kafin ta ce"Ban sani ba, ba na son tambaye tambaye mara amfani, ki je ki kwanta ki kula da ita tunda ba ta da lafiya." Ganin Inna ta haɗe rai ya sa Walida ta kama bakinta ta yi shuru, ta yi ma Inna sai da safe ta koma ɗakin ta shimfiɗa bargo a kasan cafet ta yi shirin kwanciya sannan ta kwanta ta ɗauki wayarta tana danne danne. Ba su farka ba sai asuba Mimi ta ji daɗin barcin nan ta kuma ta shi kamar ba ita ba. Bayan sun idar da sallah Walida ta fita gyaran gida tunda da wuri take fita, Mimi ba ta san wayarta ta mutu ba sai da ta ɗauko domin kiran Rukayya ta gaya mata ta cike mata takarda za ta ɗauki hutu ba ta da lafiya sai ta samu wayar a kashe, da chazar Walida ta saka chaji sannan ta koma ta zauna a wajen har ta ɗan farfaɗo ta kunna wayar ta na gama saituwa sannan saƙo ya shigo wayar daga Aji tana gani ko dubawa ba ta yi ba, tana shirin kiran Rukky sai ga kiran jaheed ta san yana ta neman lambarta bai samu ba.
Chapter 69 · 0% Book details