← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 93

Sashe 75

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

  Ya na nan zaune ya na ɗuba saƙonnin sa na kan WhatSApp da ya kwana biyu bai duba ba, har da na Makama ya tura masa hoton jaririyar, tun ranar da a ka yi haihuwar bai ma duba ba kuma ko barka ma bai kirasa ya yi masa shima yana cikin wani hali alokacin. Sai yanzu hankalinsa ya dawo jikinsa tunda Mimi ta dawo gare shi, a kasan hoton jaririyar da Makama ya turo masa ya yi tagging ya rubuta" Allah ya raya, nima nan da lokaci kaɗan za'a haifa min irin ta ko irin shi a gidana."
Ya gama rubutawa kenan ya ji buÉ—e kofa, Ya juyo sai ya ga Mimi ce ta yi wanka ta saka rigar barci riga da wando masu taushi, ba ta kalle shi ba ta nufi jakarta da ledan mganinta ta É—auka ta juya kenan ta ji ya ce"Tuwon fa? Ko ba za ki ci ba ne?
Ba ta juyo ba a sanyaye ta ce" Na ƙoshi."
Daga haka ta yi shigewarta ɗaki, yana jinta tana saka key sai kawai ya yi zaune yana bin ɗakin da kallo, tun bayan auransu ba su taɓa raba ɗaki ba, ko da sun samu matsala ba ta kai su ga raba makwanci amman yanzu kan ya san bashi da gaskiya shi ya sa ya kasa wani motsi. Zai jure har sai ta sauko ya godema Allah tunda Inna ta ba shi matarsa.

  Haka ya zauna ya ci tuwon nan sosai leda ɗaya ya rage kawai sannan ya tattara komai ya maida kitchen miyar ya saka ta acikin Fridge ya kashe komai na falon sannan ya shiga ɗakinsa ya yi wanka ya yi shirin kwanciya sai ranar ya samu yin barci sosai da safe shi ya tashi ya buga ma Mimi ƙofa sai ya ji ta na tashi tunda ta yi masa gyaran murya, Mimi gasan ƙuma ta ke yi ma Mansoor ba ta masa mgana ko zai yi mganan duniyan nan daga eh sai a a ne, Tunda ta dawo za ta yi masa abun karyawa da na rana da na dare, a baya in ta ce ya zo ya taya ta aiki sai ya ce shi ta na bashi wahala amman yanzu haka ya ke zagewa ya na shige mata da faman nacin da me zai taya ta sai ta ce bakomai, har girkin ya ce ta daina yi tunda ta na da  juna biyu, itama fa haushi yake ba ta tunda har bai yarda da ita to ba ta ga amfamin soyayyar dake tsakanin su ba.

  Sannan duk shi ya haɗa mganar cikinta har Mommy sai da ta ji,Hajiya da Baaba uwani sun zo dubata, ta ji sauki sai dai kasala da jiri take fama da shi da tsinkewar miyau sai zazzabin dare, ba ta koma aiki ba amman Rukayya ta zo dubata, kuma daga can ma'aikatansu ana ta kiranta ana gaisheta. Jaheed ya kira ta sau biyu shima bai samu natsuwa ba sai da ta ce masa ta koma gidanta sannan ya samu salama har ya na cewa"Kina ganin kiran ma da nake yi miki ba matsala? Kai tsaye ta ce"Kada ka damu ba zai kara kuskuran da ya aikata ba, ko ba soyayya kai shakikina ne saboda haka bai isa ya hanani mu'amala da kai ba."
To ai bai ma ga fuska ba,Mimi ko da yaushe fuskarta a kirne kuma ba ta son ma kallon shi in zai fita ta ce masa a dawo lafiya in ya dawo sannu da zuwa ta yi masa duk abin da yake bukata ta shige É—aki ta kwanta.

  Ko zai yi ta mgana ba ta amsa masa, Saboda dai ya saka su fita ya ce ta shirya su je barkan matar makama. Jin gidan Bibi ne ya sa ta shirya suka je da daddare suka yi mata barka an dawo da ita gidan su wajen mamanta tun bayan sallamota daga asibiti ba ma za'a yi taron suna ba saboda yanayin rayuwar da ake ciki, bayan sun baro gidan suna hanya ya yi mata surutun ba ta ga yadda jaririyar ta mata kyau ba kamar ce ta ta ce, sannan ya koma mata magiyan me ta ke so ya biya ya siya mata.
Sai a lokacin ta kalle shi kafin ta ce" Abu ɗaya nake so shi ne ka ƙyaleni."
Daga haka ta kauda kanta muryanta kamar za ta yi kuka dole ya kyaleta amman tsakani ga Allah ya gaji da wannan horon bayan fagen.

  Fiye da sati biyu suna cikin wannan rayuwar, ya gaji ya fara bin ta da ban hakurin ta yafe masa ,ita kuma ta ce ta yafe kawai dai ta kasa sakin jiki ne tunda har shi bai yarda da ita ba, in ta tuna haka har kuka ta ke yi saboda bakin ciki. Tana mamakin yanayin cikinta baya sakata amai sai dai tashin zuciya wani lokacin, ita dai sai dai kasala da jiri sai zazzabin dare ba ta kuma zaban abinci amman dai ta na cin goro, saboda sauƙin tashin zuciya ta na iya kula da kanta da gidan aikin ma za ta koma ranar Monday tun da ta samu sauƙi.
Ranar da Allah ya nufi su shirya. Ranar asabar ne Walida da Mariya a gidan suka yini suka girka shinkafa da miyar kifi. Kifin ma tun Tsaraban Inna ne na Argungu, ba ta ma sani ba suka saka shi a miyar sai kuma ta yi mata daɗi taci sosai a daran ma ta ƙara ci ta dora da maltina ta kwanta ai misalin sha biyun dare cikinta ya hana ta barci sai tashin zuciya, haka ta rarrafa ta shiga Tiolet ta rika kwara amai kamar za ta amayar da hanjin cikinta.

  Da jan jiki ta dawo gefen gado ta ɗauki waya ta kira Aji, daman bai yi barci ba yana duba wani tsare tsaren wassanin su na gaba me ya ga kiranta, kuma sai da gabansa ya faɗi ya san ba lafiya.
Sanda ya zo har ta fara galabaita tana son yin aman amman ba komai a cikinta, ganin yanayinta ya sa kawai ya saka mata hijabi ya taimakamata suka fita falo,da gudu ya ɗauko key ɗin mota jallabiyansa a juye ya saka ya rike Mimi zuwa wajen mota megadi ya taso  ga gudu ya na jera mata sannu, kawai sai Mansoor yace a buɗe masa get.

  Wani asibitin kuɗi ya kaita mafi kusa,  suna zuwa a ka karɓe ta saboda emergency ne  Mimi ta sha wahala duka sai da ta amayar da abin da ke cikinta sannan a ka mata allurai bayan an saka mata drip anan asibitin suka kwama ita an ba ta gado shi kuma ya na zaune da ita,.Sai bayan ya je sallar asuba ne ya dawo ya kira Inna ya faɗa mata hankali tashe ta ce gata nan zuwa, likitan da ya karɓe su ya kira shi ya yi masa bayani Mimi ta daina cin kifi domin cikin ta ba ya son shi, ta na daina cin wani abun da cikinta ba ya so. Allah ya sa abun ya zo da sauƙi Inna Meri ta zo ta yini da ita a ranar sai Hajiya da Mansoor ɗin ya je ya gaya mata, kwananta viyu a ka sallameta ta koma gida duka yan'uwanta sun kirata a waya kuma kowa ya san ta na da ciki Khadi har da mata tsiyan cewa Oho su Mimi da ciki an kusa zama uwa.
Chapter 75 · 0% Book details