← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 93

Sashe 70

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Ta ɗauka a sanyaye suka gaisa ya ce ya jikinta ta ce masa ta ji sauƙi. Kai tsaye ya ce"Ina fatan ba matsala? Kai tsaye itama ta ce"Da Sauki dai, za mu yi mgana daga baya." Da ga haka suka yi sallama bayan ya ce ta kira Rukky tana ta neman wayarta itama a kashe.
Suna gama waya Rukkyn ta kira nan take gaya mata Bibi ta haihu aiki a ka yi mata ta samu mace suma asibiti, Mimi ta yi mata Allah ya raya sannan ta ce in ta shiga ma'aikata ta rubuta mata takarda sai ta ce mata eh za ta je. Daman Manaja ya san ba ta jin daɗi amman za ta je ta yi rubutun ta ba da, ko alama Mimi ba ta nuna ma Rukayya wani abu ba itama ba ta sani ba tunda Jahedd ya rike alƙwari bai faɗa ma kowa ba .

  Tana gama abunda za ta yi da wayar ta sannan ta kashe wayar ta maida ta chaji, ta na shirin komawa ta kwanta Inna Meri ta shigo cikin ɗakin sanye da hijabin da ta yi salla. Mimi na ganin ta da sauri ta duka ta na gaisheta Inna Meri ta zauna gefen gado lokaci ɗaya tana faɗin" Tashi ki zauna Binta ke da ba ki da lafiya? Sannu ya karfin jikin na ki? Ta amsa mata da sauƙi kanta na ƙasa, Inna Meri ta yi mata fatan Allah ya kawo afuwa, shuru na wani lokaci sannan Inna Meri ta gyara zama lokaci ɗaya tana kiran sunan Mimin.

"Fatima.."

Mimi ta ɗago tana kallon Inna Meri bayan itama ta daidaita zaman ta a nan gefen gadon na Walida ta amsa mata cikin ƙanƙantar da kai.

"Kin É—auke ni a matsayin uwa Ko Fatima?
Mimi ta gyaɗa kanta sannan Inna Meri ta cigaba da faɗin"Na kuma ga haka, tunda ki ka zo wajena ba tare da kin tafi ga Hajiya ko Mahaifiyarki ba  na ji daɗi da kika mutumtani Binta, ki faɗamin abin da ya faru kika zo gidan nan cikin wani yanayi kuma har kika kwana ban ga megidan ki ya zo bin bayan ki ba? Me ya faru? Ki faɗa min kada ki ɓoyemin komai domin Allah Fatima."

  Inna Meri ta ƙarishe faɗa tana kallonta Mimi kuma sai ta ji idanuwanta sun cika kwallah, ta kasa mgana jikinta har ya fara rawa Da sauri Inna ta matsa kusa da ita ta na mai dafa kafaɗanta kafin ta ce"Kada ki damu ni uwace, mai jin damuwar ƴaƴanta ta kuma taya su addu'a ko kuma in tana da hanyar mangancewa ta yi musu mganin damuwarsu, ki sanar da ni abin da ke faruwa nayi miki alƙwarin yi ma duk abin da ya faru adalci in sha Allahu."
Mimi sai kawai ta fashe da kuka har da shessheƙa Inna kuma na faman lallashinta da kalamai ma su sanyaya zuciya lokaci ɗaya tana bubbuga kafaɗan ta da hannayenta.

  Sai da Mimi ta samu natsuwa sannan ta iya warware ma Inna Meri abin da ya faru, wannan karon ba za ta iya rufa masa asiri tun da har ya saka zargi a zaman auran su, ta karishe da faɗin" Inna abu ɗaya ya fi min zafi yadda Mansoor ya kasa shaidata ya ce tabbaci gare shi ina cin amanarsa da ɗan'uwana, ya saka zargi a cikin ransa kinga kenan ya na so ya ɓata auran mu, sannan da bakinsa ya ce na fitar masa daga gida na koma in da na fito daga yawon iskancin nawa." Ta faɗa ta na kuka da karfi saboda yadda in ta tuna abun ta ke jin kamar bakin ciki zai kasheta.

  Inna Meri ranta ya yi mummunan ɓaci ba ta san lokacin da ta ja wani dogon salati ba" Innalillahi wa'inna alaihirraju'un na shiga uku ni Meri, a she Baban Inna dabba ne jaki ne kuma ni ban sani ba? Haka ta faɗa saboda ranta ya ɓaci ta rasa ma wani suna za ta kira Baban Inna da shi.
Cikin harzuƙa ta cigaba da faɗin"Sakarai ne ashe mara tunani ya na abu kamar jahili wanda bai je makaranta ba? Da kansa zai lalata auran shi? da kansa zai kalle ki ya ce ya na zargin ki? Ashe shi jaki ne ban sani ba.? Inna Meri ta ƙarishe faɗa itama baƙin cikin duniya ya ishe ta.
Me ya sa Mansoor ba shi da hankali ne ba ya tunani in zai aikata abu? Shi ya sa ta sha faÉ—a masa in dan an ciza a hura saboda gudun nadama wata rana.

Kafaɗan Mimi ta dafa lokaci ɗaya tana faɗin" Ki yi hakuri don Allah Binta ki daina kuka, na kuma gode ma Allah da kika yi tunanin zuwa wajena, ni kuma zan ɗauki matakin da ya dace kuma sai ya raina kansa zan saita masa tunani tunda na lira shi ɗin dabba ne mara hankali ai ko Mu'azzamu da yake ƙaninsa wlh ba zai yi abin da ya yi ba. Shashasha kawai ki yi kwanciyarki kada ki sake ki ɗaga wayarsa balle ki faɗa masa kina nan barsa zai zo da kafarsa tunda yana zargin ki kenan ba amfanin zaman ku tare sai ya zo ya sake ki ya auri wacce zai riƙa saka ta a riga yana yawo."

  Dole Mimi ta yi shuru ganin Inna Meri ta fita ɗaukan zafi amman ba ta bar ɗakin ba sai da ta tattabar da Mimin ta daina kuka ta kuma share hawayenta sannan ta koma ɗakin ta  sai faɗa take yi ita kaɗai wannan karon sai ta ci ma Baban Inna mutumci tunda ba shi da tunani. Walida ta gama gyaran gida sannan ta yi musu abin karyawa itama ta karya sannan ta yi wanka ta ta fi wajen koyon ɗinkinta, Mimi kuma sai da ta yi wanka sannan ta karya ta sha mgani ta kwanta Inna kuma na zaune a falo tana jiran ta ga idon mara mutumcin.

******

*MANSOOR*

Barcin kirki ma bai samu ba. Shi ya sa har ya na makara sallar asuba sai dai a gida ya yi ta shi, ga yunwa yana ji amman ya kasa ma kansa wani ƙokari har kuma da wayewar garin yana ta kiran wayar Mimi a kashe shi ya sa karfe bakwai ya bar gidan zuwa Camp sun yi morning traning bayan sun gama Daga nan ko gida bai je ba ya tafi gidan hajiya. Sai dai daga yanayin tarban da kuma zolayan Hajiya ya san Mimi ba ta zo ba domin Har Hajiya sai da ta ce"Yau kai kaɗai ka zo kenan? Ina ga ka zo dai mu sansanta ne shi ya sa ka baro ta a gida."
Daga nan ya san Mimi ba ta zo ba sai kawai ya fake da ya zo gaida Hajiya ne  ya ijiye mata kuɗi bai daɗe ba ya bar gida.

  Yana fitowa daga gidan ya kira Mommy a waya itama dai suna gaisawa ya ji ta ce" Ya wajen Mimi? Fatan duk kuna lafiya? Daga nan ya tsuke bakin shi suka gaisa ya katse wayarsa shine har Dr. Sulaiman ya kira shima ɗin dai ba wani bayani alamun dai Mimi ba ta je can ba, sai kawai ya saka ma ransa tana gidan su Rukayya daman ya san gidan sai ya kaɗa kan mota sai gidan su Rukayya, ya iske ba ta a gida sai ƙanwarsu karama ita ke gaya masa Anty Bibi ce ta haihun Mama na wajenta a sibiti Anty Baby kuma ta dawo amman ta shirya ta tafi wajen aiki. Sai a lokacin ya tuna ya ga kiran Makama jiya da daddare bai ɗauka ba kuma bai bi baya ba, kenan haihuwar matarsa yake son gaya masa.

  Daga gidansu Ruƙayya ma'aikatansu na Karamchi Tv ya wuce, Rukky na can ma bangaren su Mimi ne suna mgana da Manaja, a ka ce tana da baƙo a waje ta yi mamakin ganin Aji,sai da gabanta ya faɗi ta ɗauka wani abun ne ya faru da ƙawar ta ta.
Cikin ruɗewa ta ƙarisa gabansa cikin ruɗewa take faɗin" Me ya samu Mimin? Ko dai jikin ne ya tashi, na shiga uku ni Ruƙayya"
Haka ta faɗa tana dafe ƙirjinta  Cikin mamaki Aji ya kalleta kafin ya ce"Ban gane ba. Daman ba ta da lafiya ne?
"Ba ka sani ba?
Itama Rukky ta maida masa martanin tambayansa cikin mamaki.

  Sai ya ji kunya ta kamashi cikin wani yanayi yacce"Rukayya me ya faru? Don Allah ki gaya min ina Mimin ta je jiya?
Rukayya cikin mamaki ta ce"Jiya ta zo wajen aiki ba ta da lafiya na kira wayarka baka É—auka ban Sai na kira Jaheed ya zo ya kaimu asibiti a ka yi mata allurai da karin ruwa bayan an sallamo ta, za mu kai ta gida na samu waya cewa Bibi na asibiti. Sai na bar Jaheed ya kai ta gida ni kuma na wuce asibiti, ban gane duk ba ka san abin da ya faru ba?
Yana kallon Rukayya cikin wani yanayi ya ce" Ina Fatiman take yanzu?
Rukky fa ta fara tunanin akwai wani abu cikin karin mamaki ta ce" Ah ikon Allah kai zan tambaya ba tana gidanka ba l? Mun yi waya da ita da safen nan har ta ce min na zo cike mata takarda, za ta zauna a gida na kwana biyu sai ta ƙara warwarewa."
Aji ya yi shuru kawai kamar ruwa ya ci sa, innalillahi kawai ya ke maimaita a cikin ransa. Me ya aikata? wani irin shirme ya tafka? Me ya yi ma kansa ne?
Kawai sai ya juya zai shiga mota da sauri Rukayya ta ce"Mimin ba ta kwana a gida ba ne?Sai kawai ya kaÉ—a kai kafin yace" Kada ki damu ba matsala."
Daga haka ya koma mota ya kunna ya bar haraban ma'aikatan.
Chapter 70 · 0% Book details