Sashe 2
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Mimi ta girgiza kanta kafin ta ce"Bai sakeni ba, amman zai sake ni dolen sa Hajiya."
Sai lamarin ya fara ba ma Hajiya tsoro amman ba ta sake mgana ba, ganin irin kukan da Mimi take yi yasa ba ta sake jan ta da wata mgana ba sai ta rumgumeta tana lallashinta cikin taushin murya take faÉ—in" Shike nan ya isa daina kuka ya isa Binta ya isa."
Take faɗa tana bubbuga bayan ta, Mimi tun tana kuka har ta koma sauke numfashi cikin dashewar murya, Hajiya ta lallaɓata ta koma kan gado ta kwanta ta rufa mata bargo kanta ta shafa kafin ta ce" Ki daina kuka. Da safe sai mu tatttauna kin ji ko?
Sai Mimi ta gyaÉ—a mata kai lokaci É—aya tana jin yar salama tana da tabbacin cewa Hajiya za ta mara mata baya.
 Dukkansu daga Mimi har Hajiya ba wanda ya samu cikakken barci, Mimi damuwa da bakinciki ne suka hana ta kwanciya, Ita kuma Hajiya tunani da kuma damuwa suka hana ta samun barci da wuri. Ta yanke shawaran da safe za ta kira Hamza domin ya zo ya ji abin da ke faruwa ita a tunanin ta matsala ce tsakanin Binta da mijinta kuma shi aure yana da tsari da doka domin ta ce ta hqƙura ba za a barta a zura mata ido ba ya zama dole a yi binciken abin da ke faruwa.
******
 Yadda Hajiya da Mimi suka yi kwanan damuwa da rashin barci. Haka Inna Meri ta kwana salla tana kai ma Allah kukanta Hibba da Walida ma sun kusa raba dare ba su yi barci ba, gwara ma Walida ta samu barci daga baya amman Hibba ta kasa saboda duk farkawan da ta yi sai ta leko Inna a falo sai ta ganta tana sallah tausayin Inna Meri ya gama cika mata zuciya.
Domin hannu ta ɗaga sama tana hawaye lokaci ɗaya take faɗin" Ya Allah ga bawan ka nan Mansoor ka fi ni sanin abin da ke cikin zuciyarsa Ubangiji ka saka mishi salama da yafiya a cikin ransa, ka saussauta masa wannan baƙar zuciya dake damunsa, ka ba shi zuciyar yafiya da afuwa, Ya Allah ni ba zan iya ba ka dafamin ka shiryamin rayuwar wannan yaron."
 Tana yi tana kuka, Hibba sai dai kawai ta koma ta kwanta har tana sharan kwalla, a daran ta kira wayar Mu'azzam ba ta samu ba. Sai da asuba sannan ya kira ta akan mganar tafiyar ta, sai kuma Hibba ta sanar da shi wani labari mara daɗin ji.
Cikin tashin hankali ya ce" Subhanallah! Yanzu ina ita Anty Mamin?
Hibba ta ce" Ta tafi gidan Hajiya tun a daran Jiyan." Da sauri ya ce" Me ya sa kuka barta ta tafi? Inna kuma ba ta hana ta tafiya ba?
Hibba cikin sanyin murya ta ce" Inna ba ta hana ta ba, ni ce na hanata tafiya amman ta rantse sai ta tafi." Mu'azzam ya dafe kansa daga can bangaren kafin ya ce" Yanzu ina shi Yaya Mansoor É—in?
Hibba ta ce" Wlh ban sani ba, tun jiyan ya fita ya bar gidan."
 Mu'azzam ya saki huci kafin yac e" Kin gane bari na neme shi a waya, Ina Inna take ?
Hibba ta ce"Inna na tsakar gida,.Duk ta damu jiya kwana ta yi ba ta yi barci ba gaskiya abin da ɗan uwanka ya yi bai kyauta ba kuma ina tsoron haƙƙin Mimi da Inna ya kama shi."
Mu'azzam ya jinjina kai kafin ya ce"Bari na neme sa a waya." Daga haka ya katse wayar cikin tashin hankali ya fara neman lambar Mansoor din amman wayar ta na kashe ne.
Gabaɗaya sai ya rasa mafita. Sai ya sake kiran wayar Hibba ya ce ta ba ma Inna wayar, lokacin da aka kai mata ta karɓa suka gaisa sama sama.
"Inna na ji abin da ya faru yanzu Hibba ke faÉ—amin, Inna me ya sa ba ki hana ta tafiya ba? Da sai a zauna a sulhuta mganar a nan gida ba sai ta je da mganar gidan su ba."
 Inna Meri ta yi mirmishin taakaici kafin ta ce"A a Mu'azzamu in na yi haka kamar na danne ma yarinyar nan haƙƙinta ne, gwara da ta tafi gidansu danginta su nema mata haƙƙinta, in na ce ta zauna ai ba zan iya taƙwasa Mansoor ba, ya fi karfina, tun da kuma har ya furta baya sonta to ko ƴata ce iyakar abin da zan yi mata kenan."
Duk yadda Mu'azzam ya so ya fahimtar da Inna amma ta dake kan magana É—aya wallahi ba za ta saka baki ba, Mansoor sai ya saki Mimi ita kuma da ya saka ta jin kunya ba za ta yi masa baki ba, ta yafe masa amman wallahi tallahi ta cire hannun ta a kan rayuwarsa za ta kira can kwami ta sanar da su halin da ake ciki ta yi iya nata ba za ta iya ba su zo su saka hannu suma tunda É—an sune.
 Dole ta saka Mu'azzam ya ce ma Hibba ta zauna zai shigo garin jibi jumma'a domin ya ga halin da ake ciki, amman zai dai cigaba da neman layin Mansoor ɗin ya ga ko zai same shi.
Jikinsa a sanyaye ya shirya ya tafi wajen aiki, amman yana tunanin me ya sa Yayan na shi ya aikata abin da ya aikata? Yana masa tsoron kar haƙƙin Mimi da na Inna ya kama shi kamar yadda Hibba ta faɗa. Har ya je office ɗinsa wayar Mansoor tana kashe ne ya rasa kuma hanyar da zai same shi su yi mgana.
 Gama wayar Inna da Mu'azzam ba daɗewa, Inna na kofar ɗakin ta, ƙokarin dama kunu take yi. Ta ji tashin hayaniya daga Bangaren Magajiya ta ji muryan Baba Sani da na Baba Danlami, amman mganar da ta ja hankalinta har ta dakata da abin da take yi ta saurara shivne muryan Baba Ɗanjuma da ta ji cikin fushi yana faɗin" Ba ruwan ku a wannan mganar. Ɗaki dai nawa ne, kuma ni ba ma Mansoor ɗakin nan da Kaina na ce ya zauna da matarsa har sai shi da kanshi ne ya gaji ya ce zai tashi. Saboda haka kai Sani da Ɗanlami baku da iko kan abin da yake mallakina tunda ina raye ban mutu ba."
Tunda Inna ta ji wannan kalaman jikinta ya fara rawa shike nan ta faru ta ƙare, abin da ta daɗe tana gudu sai da Baban Inna ya ja ai ya kyauta.
 Cikin wannan halin ta dama kunun saura kaɗan ma ta saki tukunyar ruwan zafin a kafarta saboda damuwa. Tunda sai tashin maganganu take ji daga bangaren Magajiya, Ta dama koko kenan ta ɗora ruwan zafi sai ga Magajiya ta faɗo shashen Inna Merin cikin hargowa tana faɗin" Malama ki faɗa ma ɗanki ya tashi ya bar ma masu gida waje, tunda dai ko bayan Ɗanjuma ya faɗi ya mutu ba shi da gadon ko filoti a cikin gidan nan."
Take faÉ—a tana kallon Inna Meri cikin reni, sannan ta rike kugunta alamun yau da bala'i ta shigo
 Kallonta kawai Inna Meri ta yi amman ba ta yi mgana ba, Baba Danjuma ne ya shigo ya na kwalama ta kira cikin tsawa" Magajiya ba na ce ki bar mganar nan ba ne?
Baba Sani da Baba Ɗanlami su ka shigo har suna haɗa baki wajen faɗin" Me ya sa za ta bar maganar? Ai gwara ta faɗa mata domin ta ji yadda ta bar agolan ɗan ta ya kame a gidan nan gwara a sake fahimtar da ita ba shi da gadon ko taku a cikin gidan nan."
Abun mamaki har da Saddiqun shima yana bayansu amman bai yi mgana ba, Inna Meri ta kai kununta É—aki. Sannan ta sake fitowa hayaniyar har ya fito da Walida da Hibba.
Baba ÆŠanjuma ke nufar Inna Meri yana faÉ—in" Meri kar ki tankasu yi shigewarki É—aki domin Allah."
Inna Meri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce" A'a kyale su gaskiya su ke faÉ—a, nan ai ba gidan uban shi ba ne ni kaina ban ga dalilin zaman shi ba."
 Ta faɗa lokaci ɗaya tana haɗiye wani abu da ya taso mata daga ƙasan zuciyarta.
Baba Ɗanjuma ya kalleta cikin mamaki amman ya kasa mgana Baba Sani ya ce" Kwarai ashe kema kin san gaskiya. Na rasa me yaron nan yake so a duniyar nan, yana da gidan shi amman nan dai haƙƙin wasu marayun ne ya tsole masa ido."
Saddiqu na daga baya ya ce"To ni in baya son gidan ne ya ba ni na zauna, in kuma ba haka ba ya tashi ya ba ma magada wajen su." Baba Ɗanlami ya ce"Ahto in ya na son zama a gidan gado sai a koma ƙauye a zauna a gidan tsoho ba"
Hibba ta kalli Walida itama ta kalleta domin dai kalaman sun yi girma.
Magajiya haka take ta masifa tana faÉ—an maganganu tana zagin Inna Meri a fakaice sannan kuma Baba ÆŠanjuma ya kasa tsawarta masu daman ko a baya Magajiya ba ta jin mganarsa ballantana su Baba Sanin. Ana cikin haka sai ga Bintu ta shigo gidan ita da su yara har da Junior.
 Ta iske an tasa uwarta gaba ana gaggaya mata mganganu. Daman kuma tun da asuba Walida ta saci wayar Inna ta tura mata saƙon abin da ya faru, shi ne tun safe ta zo gidan amman ta iske ana ta cin ma Inna mutumci har magajiya na faɗin tana takama ɗanta na da arziƙi zaman me ya ke a gidan da ba shi da gado? Ina kuɗin?
Baba Sani ya ce ko akwai kuÉ—in zuciyarsa ta mutu mganganu dai marasa daÉ—i.
Inna Meri ta kasa mgana Baba Danjuma kuma na daka musu tsawa amman ba wanda ya saurareshi Sai abin da suka manta ba su faÉ—a ba.