Sashe 35
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai Daddy ya saki fuska yana faɗin" Alhamdulillah Allah ya sa na ji daɗin haka, ka burgeni yadda ka amshi laifukan ka sannan ka ce za ka gyara sannan na amince zan baka damar yin bikon matarka saboda dalilai guda biyu na farko ka yi laifi kuma ka amsa laifin ka, ka ba da hakuri sannan ka yi niyar gyara na biyu kuma na ji labarin ka je Abuja da kano ba ka samu ganinta ba hakam ma ya saka ni yarda da mganarka ta farko. Tabbas da farko da ta dawo gida da Koke koken cewa ita a raba auran ku in da ban yi zurfin tunani da duka rayuka sun ɓaci amman sai na bata lokaci kamar yadda ka ce itama ta sauka daga fushinta na tabbata a yanzu ba za ta so rabuwar auran ku ba sai dai daman an tauna aya ne domin tsakuwa ta ji tsoro. Sannan ina son na yi maka nasiha shi riƙo ba shi da amfani mu kasance ma su afuwa tunda Allah ma muma yi masa laifi, yana yafe mana kuma shi ya ce mu kasance masu afuwa, sannan shi kan shi Yaya Kabiru kafin rasuwarsa wallahi ya yi nadama kan abin da ya aikata maka kuma Hajiya da Brr. sun je sun yi mgana da kai sun kuma nema masa afuwarka sannan kafin rasuwarsa shi ya ce duk abin da Mimi take so a yi mata dalilin da ya saka aka yi auran ku bisa duk Sharaɗɗun da ka saka ka ga ba wanda ma ya maida kansa, To me ya sa kai ba za ka yi hakuri ka manta baya ba? Sai ka bar abu na shekaru ya hana ka sukuni da zaman lafiya? Shi kan shi Yayan ina yake yau ? Ai ba shi a duniya ya ma manta shi ya taɓa rayuwar duniya, ni ma ƙila ban sani ba nan kusa ne, wataƙila kaima nan kusa ne duk ba mu san gawan fari ba, sai fatan Allah yasa mu dace sannan ka sani Allah ya yi ma masu Afuwa wani babban tanadi, Ina ba ka shawaran ka manta baya don Allah domin samar ma kan ka da zuciyarka salama."
Gabaɗaya jikin Mansoor ya yi sanyi mganganun sun shiga zuciyarsa sosai daman kuma shi tuni ya saki wannan abun Sai ya ji kamar ana rage masa nauyin zuciya cikin jinjina kai ya ce"In sha Allahu komai ya wuce. na gode Alhaji Allah ya ƙara girma." Sai Daddy ya ji daɗi har ya nuna a saman fuskarsa ya kalli Aji Lokaci ɗaya yana faɗin" Na ji daɗin yadda ka saurare ni, da duka amincewata Mimi za ta koma ɗakinta, zan kirata da kaina na ce ta dawo amman sai ka same ta ku tattauna wannan kuma tsakanin ku ne ba zan shiga ba."
Aji ya rankwafar da kai yana godiya Daddy yace"Ba laifi. Na gode kwarai Allah ya yi ma rayuwa albarka Allah kuma ya kaÉ—e fitina a tsakanin ku."
Aji ya amsa da Amin Amin kafin ya zura hannu a cikin aljihun rigarsa ya zaro kuɗi bai san ko nawa ba ne ya ijiye a gaban Daddy sannan ya miƙe yana yi masa sallama Daddy duk da yana da rufin asirin sa amman ya girmama wannan alherin ya miƙe Lokaci ɗaya y na ɗaukan kuɗin kafin ya ce"Har da ɗawainiya? To yau dai zan ce na ci kuɗin ƙwallo kenan."
Mirmishi kawai mansoor ya yi ba tare da ya yi mgana ba Har haraban gidan Daddy ya rako shi, suka kara yin sallama shi ya koma cikin gidan shi kuma sai ya hau mashin É—insa ya bar gidan, yana tafe iska na kaÉ—a shi yana jinsa kamar ya na shawagi a sararin samaniya, sannan nauyin da ke zuciyarsa ya ji ya yaye, wani irin nishaÉ—i da farinciki ke shigar sa bai sani ba, Yana tafe yana Faman mirmishi shi kaÉ—ai.
Daddy kuma yana komawa cikin gida Mama daman na falo tana jiran shi ya na shigowa ta miƙe tana faɗin" Har ya tafi? Shi kuma bai ba ma tambayarta wani muhimmamci ba ya ce" E."
Ya faÉ—a lokaci É—aya ya na zama kan É—aya daga cikin kujerun falon gefensa ta koma ta zauna tana faÉ—in" Allah sa dai ba ka ba shi fuska ba"
Kai tsaye ya kalleta kafin ya ce" wani fuskan kuma ? Na saurari bayaninsa na nuna masa Kuskuransa kuma ya karɓa ya ce zai gyara na kuma bashi izinin in Mimi ta dawo ya je su zauna su daidai ta."
Mama ta yi wani iri wanda har sai da rashin jin daÉ—in ya bayyana saman fuskarta.
Cikin mamakinta Alhaji Hamza ya kalleta kafin ya ce"Sai na ga kamar ba ki ji daÉ—in jin hakan ba ko?
Da sauri ta ce"Ba wai ban ji daɗi ba gani na yi yarinyar nan ita ta ce ta na so daga farko amman yanzu kuma ta ce ba ta so, kana ganin a tsaya sauraran shi ba ɓata lokaci ba ne? Sannan sam ba su dace da juna ba ji irin gidan da ya kai Mimi domin Allah fa."
Mirmishi ya yi domin shi ya gama gano in da ta dosa amman gudun ka ɗora ma mutun zargi ya sa yac e" To ba ki san tsakanin mata da miji sai Allah ba kenan? Itama a lokacin ɓacin rai ne amman tana son mijinta kuma ba za ta so rabuwarsu ba, mganar gida kuma ai ta san ra'ayin sa tun farko kuma ta ce ta ji ta gani, ba hurumun ba ne yanzu mu san abin da suka yanke ni dai na ce ya same ta su yi mgana abin d suka tattauna namu na saka albarka ne."
"Amman ba dai wanman gidan na su za ta koma ba ko?
Mama ta faÉ—a cikin yanayin damuwa a muryanta kai tsaye ya ce"Ban sani ba,ko ma can ne ko wani gidan ne can tsakanin su dai."
Sai Mama ta sauke ajiyar zuciya ba tare da ta yi mgana ba sai Daddy ne ya kalleta na wani ookaci kafin ya ce"Na san damuwarki kan Jaheed ne."
Da Sauri ta juya gare shi tana faÉ—in"Yallabai Yaron mu na son Mimi har yau ya kasa ba ma wata mace dama, bayan dawowan nan nata baka gq murnan da ya yi ba."
Dariyansu na manya ya yi kafin ya ce"Shi ma dai sakarai ne, mace da mijinta bai sake ta ba ne yake murna a kanta? Ke ce kuma ba ki ga ya masa gaskiya ba gwara tun da wuri ya hakura da Mimi in da ace tana son shi da ta zaɓe shi amman tunda ba ta iya zaɓarsa a baya ba yanzu ma ba za ta zaɓe shi ba, ki zauna ki gaya masa gaskiya Mimi ta haramta gare shi gwara tun lokaci bai ƙure masa ba ya nemi wata domin ba zan barshi ya tsallake shekaran nan bai yi aure ba."
Yana gama faɗin haka ya mike ya shige ciki ya barta zaune da tagumi, har Allah ta na jin haushin Hajiya domin ita taƙi ba ma Jaheed goyon baya in da tana so da Mimin ba ta isa ta yi gaddama ba, amman an na ce an ce sai abin da take so ga ta nan ga abin da ta ke so ɗin nan ya na wahalar da ita. Ranta ba daɗi itama ta bar falon zuwa ɗaakinta tana tunanin kiran ƙanwarta Hajiya Turai su tattauna mganar.
*******
*MIMI*
Lokacin da Daddy ya samu wayar Madiha wajen kwana uku da zuwan Aji wajensa ya na ta kiran wayar Mimi ba ya samu sai ya kira ta Madihan tunda suna tare, bayan sun gaisa ya ce ta haÉ—a shi da Mimi sai ta ce tana na É—akinta in sun fito zuwa masallaci da yammah zata sanar da ita akan ta kira shi.
Wannan saƙon Madiha ta gaya ma Mimi sai ita kuma ta kunna wayarta ta nemi Daddy a waya suka yi mgana ba tare da wani dogon mgana ba ya ce" An gaya miki mijin ki nata zuwa neman ki baya samun ki?
Sai ta amsa masa bai ba ta samar mgana ba ya cigaba da faɗin" To daga ƙarshe dai ya zo ya same ni mun tattauna ya karɓi laifukansa ya ce zai gyara na ba shi damar ya same ki ku yi mgana kin ji ko?
Gaddama ba halinta ba ne ya sa ta ce masa in sha Allahu sannan ya ƙara da cewa"Yaushe za ku dawo?
Kai tsaye tace" Bansa ni ba amman ina tunanin cikin satin nan." Sai ya ba ta umarnin in ta dawo ta nemi mijinta su yi mgana har ya kara da cewa" kada ki damu na yi mgana da shi na fahimci fushin zuciya ne amman shima ya na sonki kuma ya faÉ—amin ma da bakin shi, kawai dai ki yi amfani da wannan damar ki sauyashi zuwa yadda kike son ya dawo kin ji ko?
Cikin girmamawa ta amsa masa sannan su ka yi sallama sai ga ta rumgume da waya a kirjinta tana hamdala karfinta zuwanta umra akan Aji ne ta roƙi rabil samawati ya sausauta zuciyar bawansa Mansoor ya sanya masa salama da Aminci da natsuwa ya daidai ta masa rayuwarsa sannan ya Haɗe kansu shi da ita su zauna Lafiya su gina rayuwa mai kyau tare da zuru'a ɗayyiba, in da alheri a komawarta in kuma babu alheri ya cire mata son shi salin alim a cikin zuciyarta.
Itama dai tuni duk wani fushi da take yi ta ji komai ya yaye mata ta ji ta yafe masa duk da cin zarafin iyayenta da ya yi in ta tuna ranta na ɓaci, sannan kuma sintirin da ya riƙa yi a kanta ya tabbatar mata da cewa tana da wata ƴar daraja a wajensa