← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 93

Sashe 57

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani ƙaramin Karfe ya ba ta ya ce ta ɗaga amman abun mamaki yana sakar mata kawai sai karfen ya bi ta zai danne ta da sauri Aji ya riƙe karfin ya maida shi mazauninsa ita kuma Mimi ta kai ƙasa da sauri ya saka hannu ya ɗagota yana kallonta itama shi take kallo cikin haƙi tana faɗin" Na shige su, daman haka abun yake da nauyi?
Mirmishi ya yi lokaci É—aya, yana faÉ—in" To daman mana? Kin É—auka cin abinci ne ko aikin gidan tibin da kike zuwa ki zauna kawai ana É—ora miki camera?
Ya faɗa lokaci ɗaya yana laƙuce mata hanci, Mimi sai numfashi take saki ta tsorata. Da sauri ta ce"Ba wani mai ßaukin ɗauka?
Aji ya yi shuru kafin ya kai bakinsa saitin kunnenta yana faɗin" Akwai mana, gani ai ni ina da sauƙin ɗauka"
Kallonsa ta yi kafin ta balla masa harara lokaci ɗaya tana faɗin" Ba wani sauƙi, duk kanwar ja ce"
Ido ya zaro kafin ya ce"Au ni fa daman tausaya miki nake yi, amman tunda kika ce haka za ki gane baki da wayau yau. Sunan Hajiya da Mommy duk yau ba zai saka na ƙyale ki ba."

Tana jin haka ta yi saurin faÉ—in" Daga wasa? Ya fara bin ta in da ta matsa yana faÉ—in" Ni kuma ga shi ban san wasa ba."
Tana dariya ta ce"Haba Nawan. Haba mana ka ga fa ba mu ko ƙarya ba,"
Shi kuma ya ce za mu yi duk wannan daga baya. Ta kwasa da gudu za ta bar ɗakin ya tare ta cak ya ɗaga ta sama da nshi da komai ya ɗauketa yana faɗin" Duk anan karfina na yau zai ƙare."
Ta fara yawo da kafafunta tana faÉ—in"Wayyo Hajiya, Mommy Inna ku zo ku taimake ni."
Ya na tafiya da ita zuwa, ɗakinsu na barci yana fwaɗin" Su kaɗai? Ba ki kira Dr da Daddy ba, ki kuma ƙara Volume ba su ji ki ba."
Tana ganin sun shiga bedroom ɗin su shike nan ta saduda ta miƙa wuya kuma kamar mugunta, sai da ta fara masa kuka sannan ya ƙyaleta shima dai ya ce saboda yana da tausayi ne amman yadda ta haɗa sa da wancan karfen haka zai yi mata.
Sai bayan sun natsa sun yi wanka sannan suka yi zaman ƙaryawa. A lokacim Mimi ta yi masa mganar tana son zuwa ta ɗauko Hajiya ta zo ta ga gidansu, sai ya ce ta bari an juma sai su je su ɗaukota Inna ma yana son kawo ta itama ta ga gida ta saka albarka.

Bayan La'asar suka sake wanka suka fita gari. Gidan Inna suka fara zuwa suka gaishe ta, ita kaÉ—ai a gida suna gidan Walida ta dawo. Sun É—an jima kamar awa É—aya sannan suka tafi gidan Hajiya, ba su daÉ—e ba suka É—aukota Baaba Uwani daman ita ta je ta ga gidan lokacin tarewan. Sun kawo Hajiya ta ga gida ta yi ta saka albarka har tana faÉ—in" Kai Mansoor ya mganar mu ne! Na fa ga ya maka na ji na gani ka zo mu daidaita ba zan bar ma Binta wannan gidan ba ya yi mata girma."
Mimi na dariya ta ce"Hajiya na tare gaba na tare baya, ba ki da muhalli a wannan gidan"
Shi kuma Aji ya ce"Kada ki damu Hajiya ke ma ai sai na gina miki wani gidan wanda ya ninka wannan kyau da tsaruwa."
Hajiya ta ce"Shike nan kuwa an raba gardama."
Haka suka zauna suna ta hira xuciyan hajiya kamar farar takarda saboda jin daɗin ganin Mimi na zaune lafiya da mijinta. Hana ta tafiya suka yi har dare sai da Mimi ta gama dinner suka ci sannan suka maida ta gida a tare Ranar litini Mimi ta fara fita aiki da motar ta in yana da morning traning wani lokacin ma ya na riganta fita, ko kuma su fita a tare, megadin su wani matashi ne daga can anguwan Arawa Auwalu ya samo shi, an san gidan su ba shi da matsala shi ya sa in Mimi ta yi abinci Aji ya ce ta riƙa zuba masa amman fa bai amince ta riƙa fita da kanta tana ba shi ba sai dai ta ijiye in ya dawo ya ɗauka ya kai masa.

Kashedi iri iri Mimi ta sha shi da za ta koma wajen aiki.Kada ta riƙa mgana da maza ba ya son ta je ana haskata a gidan Tibi tana dariya kada ta manta ita matar aure ce, matar ma matar Aji. Ta san halin shi da mugun kishinsa na bala'i aikin ma ba domin Inna ta yi mgana ba da tuni ya rabata da shi, ita kuma saboda tana son aikinta ya sa take tsaka tsantaan. Tuni faman ta daina saka mayafi in za ta je wajen aiki sai dai hijabi, in kuma za ta saka mayafi sai in suna tare irin za su fita gidan Hajiya ko gidan Inna, shima sai ta masa yar shagwaɓa ta ce daga mota fa sai gida wane ne zai ganta ballantana ya ce wani abu, to in ta ce haka sai ya barta amman bayan haka sun zame mata kaya na ajiya kawai.

Kimanin sati uku da tarewarsu. Ya ɗauko Inna ta zo itama ta ga gida ta yi ta saka albarka Baba Danjuma ya zo tare da su Baba Sani da suka ji zai zo su ka ce suma za su zo, Mimi kuma ta yi ta hidima da su sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Aji ya ɗauke su a mota ya maida su gida iyakarsa kuma daga Kofar gida shi tunda Inna ta bar gidan bai ƙara taka kafa cikin gidan ba Magajiyar ne baya son gani daman Inna ke kaawo shi kuma yanzu ba ta a gidan ba shi da abun ɗauka a gidan kuma, ya ɗauka sai ya shekara bai taka kafarsa a cikin gidan ba amman dalilin Magajiya ba ta da lafiya zazzabi da ulcer suka kwantar da ita har a gadon asibiti Inna Meri ta kira shi ta faɗa masa ya bar Mimi su je dubiya tare da su Bintu ya ce a'a, ta bari in zai je sai su tafi tare daman kuma Bintu ba ta matsa ma kanta ba sau ɗaya ta je ta duba ta gwara ma su Yaya Amina sun je sau biyu Inna kuma kullum sai ta je kuma ta yi abincin ta tafi da shi wazai hana ta? Ko an hana ta ba za ta ji ba shi ya sa yayan nata suka saka mata na mujiya.

Kwanan ta uku a asibitin a ka sallamo ta, Kuma duk Aji ne ya yi hidima asibitin Ƴaƴanta nata da take ganin ba kamar su ba su da shi gwara ma kowa ma da Saddiqu duk ya wani susuce. Lagos ɗin ma tunda ya dawo bai koma ba, matan kuma daman duk a wahale suke Manssor din dai da Mu'azzam su ne nauyin gidan nan, Washegarin ranar da aka sallami Magajiya da daddare ya ɗauko Mimi suka zo gaisheta shima ko asibitin bai je ba amman dai ya tura ma Auwalu 20k, Sun iske har su Zuwaira a gidan da Saddiqu da matarsa, Mimi daman ta yo abincin ta zo da shi bai hana ta ba saboda ba zai iya hanata aikin alheri ba. Amman in da ba ta ce za ta zo da abincin ba, ba zai taɓa matsa mata ba, a hanya ta kuma saka shi ya siya kayan marmari ta ce ai ba za su je hannu rabbana ba.

Ai ko duk sai suka yi tsuru tsuru sai ga Magajiya na amsa gaisuwan Aji da Mimi cikin rawan baki. Baba baya nan lokacin shi ya sa ba su wani daɗe ba. Mimi ta tura kyakyawan kulan abincin da ta zo da shi tare da ledan kayan marmarin gaban Magajiya, Saddiqu daman suna shigowa ya fice ko kallo bai ishi Aji ba. Tun bayan abin da ya faru ko ƙara ganinsa bai yi ba sai yau.
Sai ga Zuwaira na godiya Magajiya ma na kwance tana faɗin" Na gode Allah ya jiƙan mahaifa." Mimi ta amsa da Amin Amin dama tun shigowarsu sun gaisa da su Zuwaira. Har Maeesha na ce mata hala aiki ne ya hana ta zuwa asibiti sai ta amsa mata da cewa wallahi, har yarinyar sai da ta ɗauka kafin su tafi, ta fahimci Maeeshan na so ta kara shige mata ne tunda har ƙofar gida suka rako su ita da zuwaira.

Suna shirin tafiya sai ga su Baba Ɗanjuma da ƴan'uwasa Baba Ɗanlami ya ce ya kamata Mimi ta shiga ta gaida su Gaje ai Baba Baba Ɗanjuma ne kaɗai uban mijinta ba. Shi ya sa Mimin ta shiga gidan ta gaida su Gaje sun kuma ji daɗi kwarai duk da ba ta wani daɗe ba,.Suna hanyar komawa gida yaron Gwaggo Yalwa ya kira wayar Aji ya na gaya masa jikin Gwaggon ya ta shi kwana biyu, a tunanin Mansoor Inna ma ba ta sani ba saboda bai ji ta yi masa mganar ba sai kawai suka biya daga nan wajen Inna ya gaya mata halin da ake ciki sai ta ce daman ta kwana biyu ba ta je ba ya kamata ta shirya ta je ta duba ta, Aji dai ya ce ba zai samu halin zuwa ba amman ya na tunanin in ya samu sarari sai su tafi tare da Mimi tun da ba ta taɓa zuwa ba.
Chapter 57 · 0% Book details