← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 93

Sashe 59

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mimi wlh tallahi lokacin da Hajiya da Momny suka zo min da mganar auran ki kaɗan ya rage ban suma saboda daɗi ba na kwana farinciki da godiyar ubangiji na yi ta sadaka sannan bayan azumin Kaffara na yi azumi bakwai wanda na yi alƙwari tsakanina da ubangiji a kan duk ranar da na same ki zan yi wannan azumin. Na saka miki waɗannan sharuɗdan ne saboda ina tunanin zan iya rama kwatakwatancin zafin da na ji a zuciyata saboda rashin ki, Mimi saboda ke nake son shiga bangaren Inna in na ganki sai naji damuwata ta yaye, in na zo ban ganki ba sai na ji ni cikin kunci, ina tsokanarki Ssboda na ga fushin ki saboda kina yi mini kyau sannan ina so ki rika biyemin muna mgana a tsakanim mu, Mimi in na saka ki kuka ji na ke yi kamar zan mutu yadda na tsani kukan Inna haka ma tsani na ji kina kuka, lokacin da kika fara sakarmin fuska muka fara zama na fi kowa farinciki in da za ki tona zuciyata a Lokacin kamar farar takarda, ba a son raina na gayya miki mganganu ba Fatima har ga Allah zuciyata ne na ƙasa iya sarrafata ta manta baya shi ya sa na kasa ba ta haɗin kai ko dama kan abib da take so. Sai na yi yunkurin mu gyara zaman su sai wata zuciyar ta hana ni, sheɗan ya yi tasiri a kaina na so na yi ma kaina saken da zan ta nadama har na koma ga Allah.

Har ga Allah ban ɗauka za ki tafi ba na ɗauka kamar yadda na ke sonki kina min son da ba za ki iya bari na ba bayan tafiyata ranar ban yi barci ba na yi ta nadaman abunda na aikata, a lokacin da baki nan na shiga tashin hankali kawai ina daurewa ne ina cikin zullumin da tunanin kada na rasaki a karo na biyu , ko ba ki zo min da wasu sharuɗɗan ba da addu'an iyaye da abokai na suka na gane gaskiya riko ba shi da amfani gwara na bar komai ya wuce domin nima na zauna lafiya cikin rayuwa mai kyau kamar kowa, abin da ya sa na gaya miki haka ina so yau ki sani tun bayan rabuwar mu da shekaru goma har yau har gobe matsayin ki bai taɓa sauyawa ba, I love u so much, ke ce mahaɗin farincikin rayuwata Fatima"

Kafin ya gama magana Mimi har ta fara shessheƙan kuka. Saboda mganganun sun shige ta, ƙara wani kamkame shi ta yi kamar za ta maida shi ciki ta ƙara fashe masa da kuka lokaci ɗaya tana faɗin" Shi shi ne ka yi ta ba ni wahala haba mana."
Haka ta ke faɗa ta na dukan sa a kirji shi kuma ya na jinta amman bai hanata ba haka ya ƙara rumgumeta kamar zai maida ta ciki lokaci ɗaya yana faɗin"Na sani, na sani amman yanzu komai ya wuce."
Kuka mimi ta riƙa yi kafin cikin kukan ta ce"ka sa na kasa kallon wani ɗa namiji da sunan so, na kasa ganin kowa sai kai. Kowa ni yake kallo an ce naƙi aure kai na ke jira ba ni da tabbas a kaina kowa sei yace ka daina sona ni kuma ina da yakinin kana sona har gobe, aji ina barci da hotonka a saman kirjina, ina kuka a kan hoton ka saboda ina tunanin ka yi min nisa!. Me ya sa ka bani wahala!.? Ka bar ni ina zaman jiran ka shekaru sama da goma bayan kuma ma same ka ka yi ta ba ni wahala, me ya sa ka min haka? Kasan yadda n ke kwana kuka saboda kai? Ta faɗa tana kara fashewa da kuka lokaci ɗaya ta na dukansa da hannunta sai da ya bari ta yi har ta gaji sannan ya kamata ya sake rumgumeta ya haɗe bakinsu wake ɗaya na tsawon lokaci ɗaya sannan ya sake ta, ta lna haki ta ce"Da na rasa ka da bansan wani hali zan shiga ba, ina sonka, da ban same ka ba da na shi."
Bai barta ta ƙarisa ba ya ƙara haɗe bakinsu waje ɗaya bayan ya maida ta kasa shi kuma ya zama yana samanta daga nan sai zencen ya sha bamban Mimi ta kamkame Aji tana sakin masa kukan farinciki shima ji ya yi kamar ya yi mata kukan saboda yanayin da yake ciki, ji ya ke yi kamar ya buɗe zuciyansa ya saka ta a ciki domin ta fahimci soyayyarta ta wahalar da shi.

A Wannan daren masoyan sun raya shi ne wajen fallasa ma juna abin da ke cikin zukatan su, da safe Aji ya ɗauko hoton Mimi da ya ɗauka a ibadan a cikin wayarsa tabbas ko ya je, itama nan ta nuna masa Ajiyayun hotunansa na wayarta da kuma ma ajiyan sirrinshi in da hotunansa suke da ta saka a ka yi mata babban frame har da tsohuwarta wayar da tsoffin tasa tasan da suka riƙa yi ma juna a shekarun baya. Ya yi mamakin ganin har a lokacin ta na nan a jiye da duk abin da ya dangance sa.
Ranar kasa fita ya yi itama haka sai kawai ta zama ranar tuna old momory ɗin su. Su yi dariya su ji haushin juna sannan su kuma koma su ƙamkame juna kowa na faɗin da ya rasa ɗan'uwansa bai san halin da zai shiga ba, tunda kowa ya san ba ma ɗan'uwansa wahala barin ma Aji sai ya yi alkwarin ba ta dukkan wani farinciki a zamantakewar su itama haka ta yi masa alkwarin ba shi dukkan wani jin ɗaɗin rayuwar aure. Amman ya faɗa mata ta kiyaye masa kanta da auransa yana da kishi, in ta kiyaye sai su zauna lafiya har abada ba mai jin kansu sai dai in sun samu matsala su zauna su sulhunta kansu a tare.

Sun fara gudanar da kyakyawan rayuwa mai cike da abun sha'awa in Rukky ta zo gidan Mimi ta yi ta ba ta sha'awa tana tunanin Allah ya sa itama Nasir ya nuna mata so haka. Da gaske ne ta na son shi har ya shiga gida, Mimi ta fahimci mijinta mai son a yi masa biyayya ne sannan a bi ra'ayinsa sannan in ya ce abu to a yi masa cikin gaggawa sai ta zama mai danne bukatunsa a kan nata, sai a ka zauna lafiya tunda ya zama shugaba kuma wakilinta komai in za ta yi sai ta tambaye sa, ko shawaransa mota ma da za ta sauya sun yi magana sai ya ce ya so shi ya sauya mata mota amma ba yanzu ba. Ba zai tsaida ta ba in tana bukatar canjin yanzu ne shike nan jin abin da ya ce ne ya sa ta fasa siyan motan saboda ta girmama maganarsa kuma ya ji daÉ—in haka. Target É—in shi na gaba Inna ta je ta sauke farali bayan nan komai wani irin buri ne zai cika shi daga baya, burin kai Mimi duk in da take so a faÉ—in duniya sannan ya yi mata komai take bukatan anan duniya domin shi take so ta kuma zauna da shi duk tsanani da wahala.

Duk in da ya ce kada ta tsallaka ba ta tsallakawa, ko gidan Hajiya in ya ce ba za ta je ba ko ba ta so ba ta nuna damuwa shi ya sa da kansa in ya ga dama zai ce ta je in ta tashi aiki, ko gidan Inna ne in bai yi ra'ayi ba sai ya ce daga wajen aiki ta koma gida, cikin lokaci Mimi ta sauya ta fara Kiba da Kumatu ta nacin mai kyau ta sha mai kyau ta kuma kwanta a waje mai kyau sannan hankalinta ya na kwance, duk wanda ya ganta ko ya yi waya da ita zai san ba ta da wata matsala.

Sau ɗaya ta taɓa shiga kasuwa ta yi cefane da kuɗin ta da ta dawo Aji ya yi mata faɗa kai tsaye yac e"Ni ban kasa a gidana ba Fatima, me ya sa za ki nemi ki kashemin Kokarina a kan ki? Ki bari duk ranar da na ce ba ni da shi ina bukatar taimakon ki sai ki taimakamin amman by now hqkkin ki na kaina naira biyar ban yarda ki kara kashe ma kanki da gidana a cikin kudin ki batare da kin gaya min ba."
Da sauri ta ce masa ya yi hakuri ba za ta ƙara ba tun daga ranar ba ta ƙara ba in abu ne ya kare shi za ta gayamawa ya je ya siyo.
Kitso ko da kunshi duk bayan sati uku wata makociyar Bintu ke zuwa tana yi mata ya biya ta. Maganar ma siya ma walida waya da ta zo wajenta ta ce ta ƙara tuna masa da ta yi masa mgana bai ce komai ba sai ta yi tunanin bari ta siya ma Walidan wayan amman da ta nemi izininsa sai ya ce a'a, sai dai ta masa kuka da cewa tunda haka ya ɗauka shike nan amman ita walida ƙanwarta ce ganin haka ne ya sa ya ce ba haka ba ne waya shi ya yi alƙwari amman ba zai hana ta ta siya mata wani abun ba.
Chapter 59 · 0% Book details