Sashe 10
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duka kayan Mimi gidan Daddy a ka sauke su,. Sai dai kayan sawanta ne Mama ta aika mata da su gabadaya gidan Hajiya.
Washegari Asabar Mommy ta biyo jirgi ta zo Gombe, can gidan Daddy ta je ta same shi suka tattauna bai fito ya nuna mata manufar shi ba amman ya ce sai ya nuna ma yaron nan Mimi yar gata ce, in yana sonta zai kawo kansa ya kuma ce kar ma wanda ya takuramata da Maganar komawa tukunna a ƙyaleta sai ta kara samun natsuwa da hutu.
 Dole Momny ta bar mganar shi ya sa ma kwananta ɗaya ta juya, sun yi saɓani ba ta daɗe da tafiya Dr. sulaiman ya zo garin shima, Duka dai bayanan da Daddy ya yi ma Mommy shi ya yi mishi ya ce kuma su taimaka masa wajen dawoma da Mimi darajanta a idon mijinta su cire bakin su su bar shi da shi da Mimin gabaɗaya.
Shima É—in bai kwana ba a ranar ya bi jirgi ya koma kano amman ya je gidan Hajiya ya gaisheta sannan ya ga Mimi sun yi mgana shi dai ya ce ta kwantar da hankalinta komai zai wuce kamar bai faru ba.
Khadi kuma aiki ya hana ta zuwa amman Kwazzaba yasa sai da Mimi ta amsa wayarta.
 Har tambayan Mimi take yi wai daman ance baƙaƙen maza sun iya rashin mutumci tana so dai Mimi ta buɗe mata cikinta ita kuma sai taƙi, ce mata kawai ta yi i ta ta ce ta na so daga farko yanzu kuma ta ce ta haƙura ba dole sai an matsa mata anji dalilinta ba, itama tana da wayon ta san kowa na rufe siirin shi ita ba za ta bar na ta a buße ba, ko da ta zaɓi rabuwa da Aji har yau har gobe zuciyarta ba ta daina son shi ba. Kawai dai ta zaɓar ma kanta barin rayuwarsa ne saboda ƙimar iyayenta, Sannan kuma yana da hallaya masa kyau ɗin da ba za ta iya zama da shi ba, to wanda bai da kyakyawan zuciya ai zama da shi hadari ne. Mutumin da ba ya ganin ka da kai da Iyayenka a wata tsiya ai ba amfanin zama da shi.
 Madiha kam da suka yi waya ce mata ta yi" Zan yi supporting ɗin ki karo na farko Sisto, In bai sake ki ta arziƙi ba to za mu maka shi a Kotu alkali ya karɓan miki yancin ki, kin fi sa komai shi ne zai yi asaran rasaaki, ke kuma sai dai ki samubwanda ya ninka sa. daman abin da Abi ya guda kenan tun farko amman at last dai Hajiya da Mommy sun kasa ganewa ke ma wawanci ya rufe miki Ido, amman kar ki damu ba ki makara ba abin da kuma kika yi kin yi dai dai i support your Decession."
 Mimi dai ba ta ce mata komai ba. Daman ai madiha kowa yasan irin kalamanta kenan, ta kuma san za ta fi kowa jin daɗin abin da ya faru, amman ko da ita ba ta yarda ta furta mata wata mgana ba.
Ita yanzu wa za ta zauna ta faɗa ma tun auran su ko hannunta sai bisa kuskure Aji ya taɓa kamawa? Sai maganar ta kara girma sai daga baya ma ta fahinci kamar ba ya sha'awarta ne tunda ba ya sonta amman ko ita ta san tana da sura mai jan hankali maza. Wata zuciyar ta ce" Ba yana kishin ki ba? Sai kuma a zuciyarta ta ce kishin banza da wofi ba shi da amfani a wajenta yanzu.
 Jin daɗin ma tana Annual Leave ne, shi ya sa ba ta aikin komai a gida sai kwanciya da tunanin. Tuni ta daɗe da blooking ɗin duka lambobin yan gidansu Mansoor domin ba ta so ma ta ɗauka a roketa abin da ba za ta iya ba, Ko Rukky ba su yi waya ba ballantana tasan abinda ke faruwa ra bon ta da mgana da ita tun ta na Abuja, kila za ta yi tunanin ba ta dawo ba ne. ita kuma ba ta so ma ta sani saboda surutun Rukky ne ba ta so, daman itama tana daga cikin ƴan adawa da auran.
******
Bangaren Mu'azzam kuma tun da ya sauka garin yake lallashin Inna da ban baki da roƙon ta domin Allah ta shirya ta je gidan Hajiya ta ba ma Mimi hakuri ta dawo, haka duka yaran suka haɗe mata kai, ita kuma ta yi rantsuwan cewa ba in da za ta je suma kuma duk wanda ya je ba ta aike shi ba.
Abin a ya fi bata musu rai ma shi ne a ranar asabar da safe aka fara kwaso kayan Maeesha zuwa É—akin Mimi ba sanarwa ba komai maza na giftawa, bayan Inna Meri da kanta ta zo ta share É—akin ta goge.
Sannan ta fito da kayan abincin da aka bari a É—akin ta watsar nan kofar É—akin Inna Meri sai da Hibba da Walida suka kwashe suka shigo da su É—akin Innar.
 Ganin Inna ta cije, domin ita ɓacin ranta ɗaya, yadda shi uban gayyar bai ma san ana yi ba tunda washegarin ranar da ya yi tsiyar bai ƙara dawowa ba to sai ta ga ko an shiga mganar ba amfani zai iya maimaita abin da ya aikata tunda bai san darajan matar ba, Sannan ita da kanta ta kira Alhaji Kabiru babansa na Bauchi tana gayamasa abin da ke faruwa a tunaninta zai zo garin ya same shi ya yi mishi faɗa tunda ita dai daman ya renata ba ya jin mganarta.
Amman kawai sai ta ji ya ce"Haka aka yi kenan? Daman ai Gwaggon sa Yalwa ta faÉ—amin baya son yarinyar, kawai ya saketa sai ya zo gidana ya duba mata na aura masa ."
Haushi ya kama Inna to ko É—iyar Babansa ya aura zai iya yi mata abin da ya fika haka in dai wanna mai bakar zuciyar ne.
Daga nan ba ta kara neman su ba, Domin ta na da tabbacin suma ya fi ƙarfin su.
 Mu'azzam tare da su Yaya Amina suka yi shawara, shi yanzu su Nasir yake jira Ahmad ne yace a jira shi zai shigo garin tunda dukkansu sun ji labari, kuma cikinsu duk wamda ya kira Aji baya ɗaukan wayansa su sun ce za su yi masa ne bisa zaman tare da abokantaka bisa Amana, za su je su yi gamgami su samu Mimi su ba ta hakuri, Sai Mu'azzam yace kafin su je, su matan su shirya su je su gani.
Ba tare da Inna ta sani ba suka haÉ—u a gidan Bintu domin Hibba cewa ta yi Walida za ta rakata gida ta É—auko wasu kayan.
Inna bqta sani ba suka haɗu gabaɗayansu Har da Yaya Halima sai gidan Hajiya amman abin da ya ƙara ba su tsoro Hajiya da kanta ta ce musu Mimi ta kwanta kanta na ciwo kuma ba zai yuyu a tashe ta ba.
Zaman kusan awa huÉ—u suka yi tun la'asar anan ma suka yi sallar mangariba amman Mimi ba ta bari sun ganta ba. daga baya dai suka fahimci cewa Ita ce ba ta son su haÉ—u.
 Yaya Amina ce ta yi ma Hajiya mganar a yi hakuri abun bai kai haka ba don Allah Mimi ta dawo ɗakinta su suna sonta, Inna ma kunya ce da nauyi suka hana ta zuwa.
Amman sai Hajiya ta yi dariya kafin ta ce" Ayya ni kaina zan so hakan, amman kuma mganar ba ta hannuna tana wajen Binta da Babanta ne, abin da duk suka yanke shike nan."
Fahimtar da suka yi lamarin ya wuce tunaninsu haka suka dawo gidan Inna jiki ba daɗi suka iske wani ƙarin abun haushi ƴan'uwan Maeesha sun dawo da ita sun yi kaca kaca da shashen suna ta shewar su, Inna dai ba ta gaya musu ba ne amman Ko darajan gaisuwa ba ta samu ba.
Sai da suka dawo ne suka faɗa mata abin da ya faru da in da su ka je, Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"Sun yi min dai dai, ku kuma Allah ya ƙara sai da na ce kar ku je, wanda ya ɓata bai san hanyar gyara ba sai ku?
 Mu'azzam da ya zo ya ji labarin abin da ya faru sai jikinsa ya yi sanyi, yanzu haka Aji ya bar masa gida shi a Camp yake kwana in kuma ya je da niyyar su yi mgana sai ya ce suna da traning haka dai duk ya shanshantar da maganar Mimi, shi kuma Mansoor tunaninsa ya bi Mimi gidansu ya ba ta hakuri kamar ya sauko ne ya yi Arha, a tunaninsa auranta na hannunsa to zai tsaya ya ga iya gudun ruwanta shi bai ce ta tafi ba, ita ce ta zaɓi tafiya shi kuma ya goya ma zaɓinta baya, kuma ba ya son kowa ya shiga maganar kotun da ta ce za ta kaisa ya ke jira, ɗayan tunaninsa nasa kuma na gayamasa Mimi na son shi ba za ta iya rayuwa ba shi ba, tabbas duk in da ta je ma za ta dawo ko labarin an kwashe kaya bai samu ba balle ya dawo cikin hayyacinsa ya fahimci shirmen da ya tafka yana nan yana shirme da tunanin banza..