Sashe 16
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Cikin girmamawa suka gaisa da Hajiya, Ita kuma ta amsa masa cikin sakewa kamar wani abu ma bai faru ba. Har ta na masa irin zolayan da ta saba yi masa, tunda har ga Allah ba ta san da zuwan sa ba tunda Binta ba ta kira ta ba.
Kallon sa ta yi kansa na duke lokaci É—aya tana faÉ—in" Ka makara da zuwa biko, Binta ba ta na nan shekaran jiya can ta tafi can Abuja wajen Murja. Hala ba ku yi waya ba ne?
Kansa na kass a cikin zuciyarsa ya maimaita" Abuja?
Lalle ne ma Mimi ta maida shi wani sakarai ya ga alama akwai kasawa ma ya ce ma Hajiya sun yi magana a waya shi ya sa kawai sai ya ce mata ya kira wayar ta bai same ta ba.
Hajiya ta muskuta kafin ta ce"Ai ko ba ta nan, amman tunda biko ka zo kuma ta karfe ta gudu, me zai hana ni mu daidaita? Ta fada cikin Sigar zolaya yar dariya ya yi yana shafa kansa kafin ya ce" Haka za'a yi Hajiya."
Shuru na wani lokaci, Hajiya ce ma take É—an Jansa da hira tana tambayan shi aiki da mutanen gida.
Ya amsa mata da duk suna lafiya kai tsaye ta ce" Ka gaida min da Meri dakyau dakyau."
Ya amsa da In sha Allahu, ko ruwan da aka kawo masa bai sha ba ya yi ma Hajiya Sallama da cewa zai koma.
"To ko za ka ƙarisa gidan Babanta Hamza ne. Daman yana neman ka."
Hajiya ta ce tana kallonsa lokacin da ya miƙe shi kuma ba ya son wata doguwar mgana sai kawai yace mata Toh, amman shi ya san ba zai je ba wato ya kai kansa kenan tunda daman ana jiran shi.
Kuɗi ya ijiye ma Hajiya a nan ƙasa ta saka hannu ta ɗauka tana faɗin" Ai shike nan kana bikon dani tunda ka fara toshi, Na gode kwarai Allah ya ƙara ma rayuwa albarka."
Ya amsa mata da Amin Amin sannan ya yi mata sallama ya bar falon ta bi shi da kallo, Binta ta cika taurin kai sai da ta hana ta tafiyar nan amman ta haɗa ta da ubanta ya ce a ƙyaleta ta je ta gaida mahaifyarta ga shi megidanta ya zo ba ta nan, Baaba Uwani Hajiya ta kira ta Umarce ta da ta Dauko mata Wayarta a cikin ɗakinta.
Bayan ta kawo mata sai ta ce ta kira mata Binta tunda Baaba Uwani ta iya karatun Hausa ita ta nemo lambar Mimi ta kira ta sqnnan ta miƙa ma Hajiya tana ɗauka ta fara faɗin" Hajiya ta, kin yi kewata ne?
Hajiya ta ce" Kin san cewa yanzu mijin ki ya bar gidan nan yana neman ki?
Sai Mimi ta gyara kwanciyarta kafin ta ce" Wa? Aji? Ban sani ba saboda bai kirani ba."
Ta yi ma Hajiya ƙarya. Sai ita kuma Hajiyar ta ce"To ya zo, na sanar da shi bakya nan amman na ce ya karisa wajen babanki ke kuma sai ki yi kokari ki dawo a daidaita ki koma gidan Mijin ki."
Ba gaddama ta amsa ma Hajiya saboda ko ta ce za ta yi gaddama Hajiya ba za ta gane in da ta dosa ba ne.
Bayan sun gama waya da Hajiya ita kaɗai take ta Mirmishi, Kaɗan ya gani yanzu ma aka fara wasan ba ɗaɗewa ko sai ga kiran shi ya sake shigo mata wannan karon ba ta kashe ba barin shi ta yi har sai da ta katse, wani kiran ya ƙara shigowa ya katse har sau uku bayan mintina kaɗan sai ga saƙon sa.
"Kin raina ni ko Mimi? Kina jin daÉ—in kin yi wasa da hankalina ko? to ya yi miki kyau amman ina so ki sani ki sauke wannan abin da da ki ka É—auka na tunanin za ki wahalar da Aji ko ki yi ramako a kaina, Never zuwan ma da kika na yi saboda inna da Baba sun matsa sai na zo na dawo dake gida, in kin ga dama daga nan Abujan ki ci gaba kin ji ko."
Daga ganin yanayin saƙon ta san ranshi ne ya ɓaci, tana yar dariya bayan ta karanta wato zai fake da Baba da Inna shi a dole kada a hango ya gaza, a lokacin ba ta yi tunanin maida masa da martani ba sai bayan kamar awa ɗaya tun da barin ɗakin ta yi zuwa falo in da Asma'u ke kallo Mommy kuma tana ɗakin ta tana faman duba takardu sai wajen goma saura ta Daawo ɗakinta ta yi wanka ta kuma yi shirin kwanciya sai da ta kwanta sannan ta jawo wayarta ta tura masa saƙo.
"To shike nan zan ci gaba kamar yadda ka ce."
A lokacin da saƙonta ya shigo kamar tasan yana kwance ne yana kisima hukuncin da zai yanke Mata in ta bari suka haɗu, tsabar ma takaici ko abinci bai ci a daran kuma in ya je gidan Inna ba bashi za ta yi ba domin tun bayan barin Mimi gidan inna ta daina masa tayin abincin ko ya ce zai ci sai ta ce ya kare ko da ga shi nan ko yana gani shi ya sa yake rufa ma kansa a siri ko ya gani bai nuna yana bukata. Barcin sa rabi da rabi ne a baya ne da yasan Mimi na ƙarƙashinsa ya ke samun Ishasshen barci amman tunda ya fahimci kamar ta yi masa nisa ya daina samun barci cikin natsuwa. Shi fa a ransa sai da ya ga laifin Hajiya ta ya ya za a su bar matar aure tana yawo ba tare da sanin Mijinta ba shi fa tafiyarta Abuja ta fi masa raɗadi fiye da yadda take yi masa wannan renin wayau.
Da farko ya yi alkwarin ba zai ƙara kiran ta ba amman ba shi da mafita saboda ya kasa sukuni ko da bai kirata ba yana bibiye da dukkkan wani motsinta. Haka kawai saboda ita zai hau facebook da WhaApps ya duba ta, a Facebook duka Account ɗin ta guda biyu na Fatima Kabir Dabo(Mimin karamchi) da kuma na wanda ta buɗe a ɓoye na MIAJ, duk ya san dasu kuma yana vibiyanta amman ba ta taɓa sani ba, to abubuwa da dama ma ba ta sani ba wani abun gwara ka bar shi a rufe saboda Sanin shi a lokacin ba shi da wani amfani.
Yini yake duba ta sai ya ga ba ta saka komai ba kamar ma tun bayan auransu motsin Account É—inta ya dakata.
Sannan ya duba bangaren hidan tibin da take aiki, daman tun kwanaki ya ga ma kallata gidan Tibin suna ta cigiyarta sai suka ba da sanarwan ta na nan lafiya ta ɗauki hutu ne ma'ana Anaual leave ɗin ta, ƙaramin tsaki ya ja shi fa ya tsani aikin nan domin shi bai ga wani amfanin shi a Al'umma ba, Kuma zai bude data yana ganin tarin Groups da aka saka shi yawanci duk na ƙwallo ne tunda babu wani Team na nan Gombe da ba'a saka shi a ciki ba, akwai wani ma da tunda aka saka shi an tara saƙo sama da dubu bai taɓa buɗewa ba, kuma ko a Private ka yi masa mgana in ka ci sa'a ya buɗe ya karanta ba zai maida maka amsa ba sai dai in ta kama ya kira ka. Saboda gani yake ɓata lokaci ne ya tsayawa yana typing.
Shi ya sa duk yadda su Nasir suke caccakan sa a group ɗin su na Brother's bai ko shiga ba, Ko mu'azzam ba ya chart da shi sai dai in ya ga ya yi masa mgana ya sauka ya kira shi, yawanci ma shima yasan hali yafi tura mishi hotuna ko wani abu mai muhimmanci,group ɗin su na jami'a ko tuni ya fice,an sake maida shi ya sake fita har sau uku, daga nan suka ƙyaleshi.
Har ta goup ɗin su na Gombe United kowa na da amfani ban da shi hatta Coach na su yana mgana da sauran bayanai amman shi sai dai a waya ko ya je Camp ɗin ya tara su yi magana shi ya zauna ne wai ya ga yana rubutu ya ke ganin shi a ɓata lokaci ko kuma wai ya kunna voice note shi fa har mamakin ma su yi masa vioce yake yi, wani mai tsawon ma shi ai ba shi da wannan lokacin, wani lokaci yana buɗewa yake kashewa ba ya da lokacin saurara shi ya sa ga wanda yasan tayuwar Aji gwara ya kira shi a waya amman domin ya yi magana ta chart kamar ya zama aikin banza ne