Sashe 50
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ta kyale shi gajiya ne a jikinta saboda ta wahala yau ga azumi ga aiki, amman ɗazun nan ba ta ma jin yunwar. Sai yanzu da ta kwanta gajiyan ya taso mata, har ta fara barci ta ji karan wayanta tana dubawa ta ga Aji ne da sauri ta ɗaga kiran na shi tana tambayansa ya ya koma gida? Ya amsa mata a dakune lokacin fa ya gama cin abincin da ta yi masa ne farar shinkafa da miyar naman rago da cowslow, sai zoɓo da kunu, daman bai ci komai ba amman kishi ya hana shi ya nemi wani abu da ba ta kawo masa ba haka zai kwana kuma ya tashi da azumi. Haka dai su ka yi wayar yana ta wani cin mgani ta na dai bashi hakuri. Shi bai ce ya haƙura ba shi kuma bai ce bai haƙura ba, Karshe ma barci ne ya kama idanuwanta ya sa ta yi masa sallama tace za ta kwanta, da asuba ma wayarsa ne ya tashe ta ya ce ta tashi ta yi Sahur ita kuma sai da za ta tafi wajen aiki ta kira shi yana barci sai bayan ta je wajen aiki ya kira ta daga jin muryansa ma ta san yana barci ne sai suka gaisa sama samma sannan suka yi sallama har a lokacin dai bai gama Hucewa ba sai bayan wajen kwana huɗu sannan ya warware ya daina fushi fushi. Amman da ta ce ta ƙara gayyatansa shan ruwa cewaa ya yi ba zai zo ba kada ya ƙara zuwa ya ga ta gayyato saurayinta.
Sai ta riƙe baki kafin ta ce"Ba ka hakura ba kenan? Kuma ni ai ba ni na gayyace sa ba."
Banza ya yi mata. Sanda suke mganar ya kaita ne kasuwa ta amso ɗinkunan hijabanta a ranar ta ba shi Atm ɗin sa ya kalleta kafin ya ce"Kin gama komai? Domin kika sake na karɓa in ma da wani abin sai dai ki siya da kuɗin ki"
Tana jin haka ta yi saurin maida shi jaka tana na faÉ—in" Ban cire na gyaran jiki ba."
Taɓe baki ya yi bai yi mgana ba, da ta ga kamar ya ƙara shaƙa sai ta ce"Ka zo gobe don Allah zan jira ka."
"Ba zan zo ba."
Haka ya ce kuma yanayin mganarsa ya sa ta san da gaske yake yi sai ta kyale shi.
Da ta gaya ma Rukky itama sai da ta ce Jaheed bai kyauta ba amman ta ba shi hakuri to sai ya nuna kamar ya hakura sai kuma ya nuna kamar bai haƙura ba.
Ko da ya kai ta gida ma bai shiga ba ya yi tafiyarsa. Wajem sati fa ya na mata wannan halin sai ta yi masa mai gabaÉ—aya ranar da aka kai azumi goma ta shirya masa abun shan ruwa ta kira shi ta ce ya zo ya ce ba zai zo ya ga abin haushi ba ,sai kawai ta ce zan zo to na kawo maka"
Da sauri ya ce"Ba ki da hankali ne? Ki tsaya gani nan zuwa wlh kada ki ce za ki taho."
Daman ta shirya masa ne, ta san in ya ji ta ce za ta so sai ta shi hankalisa tunda daman ko ranar sai da ya ƙara mata fadan zuwan da ta yi, ko Minti talatin ba'a yi ba sai ga shi ya zo amman ya ce ba zai shiga ciki ba sai dai ta kawo masa ya tafii da shi, ita kuma sai ta shagwaɓe masa tana faɗin" Mu shiga ciki mana, ba sai ka ga abin da ka ce ina maka rowa ba?
Ya kasa mata musu saboda ta rike hannunsa sannan ta ma masa fari dole ya bita cikin falon ya zauna ta haɗo masa kayan shan ruwa tun yana basarwa har ya saki jiki, Ita kuma tana cire mayafi ya ganta cikin wata riga mai roba ta kama ta. Kirjinta rabi duk a waje ssannan ba ta saka ɗankwali ba ta ɗaure gashinta kawai, Aji na cin abinci ya na kallonta ƙasa ƙasa, Sai bayan sun gama ta kwashe abin da suka yi amfani da shi sannan ta dawo gabansa ta juya masa dakyau sannan ta kashe masa ido ɗaya tana faɗin" Ga gama kallon ne?
Haka ta faÉ—a tana masa dariya sai kawai ya kalleta cikin wani yanayi kafin ya ce"KaÉ—an na kalla."
Baki ta rufe tana dariya, ba ta san lokacin da ya ta so ba jinta kawai ta yi a jikinsa ya rumgumeta kamkam, itama sai ta lafe a kirjinsa tana shaƙan kamshin turarensa mai saka ta natsuwa. Rungumeta kawai ya yi sai ita ce ma da ya ɗago ta sumbaci bakinsa sai ya kalleta sai ta ji kunya ta juya baya sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce"Daran ranar ba ɗaga kafa wallahi."
Haka ya faɗa sannan ya koma ya sha mur kamar ba shi ya faɗa ba da zai tafi ya ba ma Hajiya 5k, baba Uwani 3k, ita dai ya ce ko sisi ba zai ba ta ba, da ta ce tukwaicin girki fa? Sai ya ce to ai ladanta na wajen Allah Tun da ta ciyar da mijinta sannan shi ba shi da kuɗi ta gama talauta shi ma gaɓadaya shi ya yi mganar sai ya bar ta da dariya.
Tun daga ranar ta samu ya huce, yabq zuwa a sati sau biyu su yi BuÉ—e baki, gefe daya tana ta shiryen shiryen tarewa gini kuma yana ta nisa sun yi mgana da Mommy dole kayan gida komai sabo za'a siya ita Mommy ta yi mgana da Daddy ya ce ba laifi in an gama gidan sai aje aka ga abib da ya kamata a siya, ita dai bangaren Mimi kayan É—akinta da a ka kwaso daga gidan Wanzamai ta ce a bar mata sai ta saka shi a wani falo tun da ya ce falo biyu ne nata sai bedroom uku sai shi falo É—aya Bedroom guda biyu, ga sallah na matsowa kuÉ—in da ya tara Mimi duk ta yi kasa da su, Hibba ya ba ma kwangilan kayan sallah na Inna da Walida Junoir, sai Mariya da Baba da magajiya, Bintu ma ya yi mata kala É—aya.
Inna kala uku, Magajiya biyu, Baba ma shadda da yadi guda biyu su Baba Sani Kuma Mu'azzam ya yi musu har da su mariya suma ya kara musu da kala É—aya É—aya. Magajiya sai dai ta ga Baba ya shigo da kaya Hatta Mariya kala uku ne Mu'azzam kuma ya haÉ—o musu da kuÉ—in dinki.
Gaje da Harira ma ya yi musu Atamfofi kala daya daya, suna ta godiya Magajiya ta kasa mgana domin kaf a cikin ƴayanta ba wanda ya ke mata kayan sallah sai Mu'azzam da Mansoor, Auwalu na fama da kanshi Saddiqu kuma bai garin ina ya ga ta zama bashi kaɗai ya ishe shi, Dole kanwar ñaki zuru'an Innan dai sume suke taimakon su tunda ga sutura har bangaran abinci tunda in sun ci su ne, in kuma sun sha suma sune.
Mariya sai murna take yi tana da kala huɗu, tunda saurayinta ya yi mata ɗaya sannan su ka haɗa kudi su biyar za su yanka sa Nasir Makama, Ahmad Mu'azzam da Aji domin su raba a tsakaninsu, Aji kuma ya ce zai ƙara da shiga tantan saboda Can gidan da su Baba Sani.
Ana sallah saura kwana huÉ—u Hibba da Mu'azzam suka sauka a garin, da kaya niki niki na kayan fulawa duk ta siyo komai anan za su yi cincin da sauran cimar fulawa, Matan su Yaya Amina kuÉ—i yan'uwa suka ba su, Bintu dai an mata kaya ita da yayanta, Ana jibi sallah suka yanka san su, naman duka gidan Inna aka kawo sannan ga kaji Mu'azzam ya siya guda goma. Biyar nan gidan Inna uku Magajiya biyu Baba Sani da Baba Danjuma. Shi kuma Aji naman tantan na 50k ya shiga aka raba na Magajiya kashi Biyu su Baba Sani kashi É—aya, sai ga shi karon darko Magajiya da aka kawo mata nama da kaji ta buÉ—e baki ta ce Allah ya yi albarka sannan Auwalu ma ya kawo musu Nama tunda a kwangilan aikin gidan Aji Alhamdulillah, ya na samu kuma haka ya gaya ma Magajiyar. Shuru kawai ta yi ta kasa magana ko Jummai ma da ta kira Mu'azzam dubu goma ya tura mata, Saddiqu kuma sai kiran babu, domin ya ce Maeesha ta matsa masa sai da ya tura mata wasu kudaÉ—e biyar ba'a samu ta hannunsa ba, in da ace ma dasu aka dogara da an mutu ba'a ci ba.
Ana gobe sallah gabaÉ—ayansu sun haÉ—u a gidan Aji da ake gini har an saka get da Kofifin cikin gida yanzu POP suke yi da plasta sannan masu saka tayil da Interlock na cikin gida na aikinsu Ahmad ya ce"Lalle Aji ka tara kuÉ—i."
Aji ya ce"Duk sun ƙare, Mimi kaɗan ya rage ba ta maidani talaka ba."
Nasir ya ce"Ta cancanta ne."
Suna gidan har aka sha ruwa lokacin da Ma'aikatan su ka ta shi akwai wanda ke kwana a gidan saboda barayi. Dag nnan gidan Makama suka wuce nan suka shirya shan ruwa suna gidan Rukky ta zo kawo mata ɗinkunanta kawai sai ta gan su cikin mamaki ta kama baki tana faɗin" Yallaɓai na Mimi ashe kana nan?
Aji na Mirmishi ya ce"Nan fa gidan abokina ne, za ki iya ganina ko wani lokaci."
Nan fa aka gaggaisa, ta shiga ciki Nasir ya ce"Yayar matar ta ka akwai girman kai."
Makama ya ce" Da alamu dai kana ciki da ita domin ina ganin ka, kana satan kallon ta.".