Sashe 85
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maeesha ma ta kawo mata gumba mai kyau ta na sha da madara. Mariya na ta nurna ganin Walida duk da tana da ƙawaye amman ai Walida ta dabam ce kuma ƴar'uwanta ce.
An je jere ana saura biyu daurin aure angon Mariya ya yi gidansa ɗan daidai an danka mata shi da kaya ko wata yar gatan sai haka gado biyu ga tibinta ga firiza ga gas ga Tv stand ga center table ga cafet ga labulayan masu kyau da zannuwan gado kitchen ma koma ya ji ga kayan garanta an yi daidai gwargwardo har dake dake ma yan'uwan Magajiya sun yo sannan su Gaje ma sun ƙara mata. Inna ce uwar Amarya da su Gaje da su ake shawara.
Aji sai ana gobe ɗaurin aure ya dawo daga Abuja ya yi kiba ya ƙara haske. Murnansa ya ga Inna da matarsa da Ummi ai ko shima ya yi mamakin girman Ummi yana dariya ya ce yar lukuta.
Ranar a gida Mimi ta kwana ana sabunta amarci sai can rana ya kawota gidan wanzamai inda ake sha'anin bikin,Inna ta bashi tsarabanta ya karɓa da godiya a ranar ma da yamma jallabiyan ya saka haka kuma ya ga Mu'azzam ma ya saka naahi, sai suka kalli juna suna mirmishi suma suna ta shiryen shiryen wajen daurin aure a masallacim kusa da su ne amman sun saka an share kofar gida an gyara shi saboda mutane. Har saddiqu da shi ake komai ya ga ba sarki sai Allah ya saduda. Yaya Mansoor sama Yaya Mu'azzam domin ya fahinci in ya yi tawaye ba riba hakama Magajiya ta faɗa masa.
Gida cike da baki ana ta hada hada
Matan sun yi ankon Atamfa na biki,sannan ko walima ba'a yi ba sai ranar lahadi a gidan Amarya.
Mariya a gidan Bintu za su yi zaman su tunda kusa ne sai ya kasance su Mimi duk suna can har da su Nafisa da Bibi matar Ahmad dai sun koma kaduna.
Har da Yan'uwansu Hibba duka da su ake sha'anin ƙannen mahaifansu Yaya Amina kuwa, daman duk wani sha'ani da su keyin shi kuma duk saboda Inna Meri ne a ka zo a ka yi ma Magajiya karan.
Ana jibi bikin nan suka kawo lefe akwati shidda kuma da kayansu ma sha Allah daidai karfin talaka mai nema.
Ranar asabar aka tashi da shagalin biki sha daya na safe aka É—aura auren Mariya da angon ta Aminu, Baba ÆŠanlami me waliyin Amarya anan wajen ya ce ya wakilta Aji ya yi ma Mariya wallici shi ya ba da auranta ga waliyan Aliyu sannan bayan É—aurin auran ana rawan jikin gaisawa da shi wanda bai ma san shi ba an gaya masa sunan shi.
Ango da tawagansa sun sha fararen kaya suma su Mu'azzan kowa da kalan kayanshi amman sun saka babban riga har da Saddiqu da ya saka ta bikin shi, Baba ma sabuwa Mu'azzam ya ɗinka masa da Sabon takalmi a cikin gida kuwa ana ta hada hada an dafa ahinkafa da alala sannan an yi waina Amarya da ƙaawayenta sun yi firaidi rice din shinkafa da Alala sai nama da Mimi ta bada kuɗi aka siya kilo uku saboda baki Walida yan jami'an an sha kwallya tunda sun yi makeup, nan aka bar wasu ƙawayen su Mimi suka tafi da Amarya can gidan ana ta hotuna duk rashin son hoton Aji su Yaya Amina suka rike shi sai da ya shiga amman ya na rike da Ummi a kafaɗansa ɗayan hannun kuma ya na rike da Junior da damam ɗan gidanshi ne.
Ammi dai tana wajen uwarta Mu'azzam dai daman ba shi da wani nane ma yara.
GabaÉ—aya ahalin gidan Wanzamai a ka haÉ—u a ka yi family picture su Gaje da Harira da yayansu maza da mata da su Baba ÆŠanlami Inna meri da Magajiya da Baba Danjuma da su Aji da yayansu da matansu gabaÉ—aya a ka dauki joton kowa ya gansu sai ya ji sun ba shi sha'awa babu abunda yafi haÉ—in kai daÉ—i.
Bayan La'asar Mansoor da Auwalu suka dauki amarya zuwa ɗakinta daga umarmin Baba Ɗanjuma, tare da Inna su ka je da wata ƙanwar Magajiya sauran daga baya su ka zo bayan ango ya kawo motoci, Mariya na ta kuka domin yayyenta sun mata faɗa ta zauna lafiya kowaani aure da ta gani yanzu na da shi kalubalen gwara ma ta zauna lafiya, Walida ne da sauran ƙawaye suka kwana a gidan sauran kuma suka koma gidajemsu suka kwana su Hibba dai a gidan Inna daman suke kwana Mimi kuma Aji ba barinta daman zai yi ba.
Sai washegari suka koma kai kayan da ake ba ma dangin ango bayan sun É—auki Mariya zuwa gidan iyayen mijin, su Mimi da su Yaya Amina sai Inna da su Gaje,an gama komai cikin girma da arziki sun mika amanarta ga dangin mijinta suka baro ta acan tana kuka.
Wasu suka sauka gidan Magajiya wasu kuma gidan Inna irin su Mimi da sai dare Mansoor ya zo suka koma gida.
Wasahegari litini Mimi ta tafi aiki shi kuma sai ya leka Camp É—in su na Gombe United su ka gaggaisa da su Kb suna ta cewa sun yi kewarsa ya ga pele sosai daman yake da kokari shima auransa ya kusa sun zauna da Caach suna ta hira kan sabon horon da yake samu anan Abuja sai can rana ya baro wajen ya isa ma'aikatansu Mimi ya É—aukota suka dawo gida.
Ranar talata ya bi jirgi ya koma Abuja Mu'azzam kuma washegari shima suka koma kano, amman ba su tafi sai da suka sallami Safiya da kuÉ—in mota za ta koma
An yi cincin da dublan na Amarya an yi kuma na rabo an dibar ma su Mu'azzam sai Mansoor da Mimi ta haɗa masa cikin kayan snkas din ta yi masa , har da dambun kaza da miya ta yi masa saboda ya gaya mata wancan tafiyan ba karamin wahala ya yi ba, shiyasa wannan karon ta shirya ma tafiyar nashi sannan sun yi mgana da Mommy ta ce za tariƙa ba ma direba abinci da lambar wayarsa sai ya riƙa kai masa can Camp ɗin su.
Amman kuma ta san halin Aji ba lalle ya amince ba amman duk da haka sai ta ce za ta gaya masa, ta na ko yi masa mgana ya ce a'a ba ya son ya saka Mommy wahala da É—awaniya.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3020*
Duk da yace ba ya son saka Mommy ɗawaniya amman duk weekend Asma'u kan yi abinci a saka direba ya kai masa har Camp ɗin su fitowa kawai ya ke yi ya karɓa. Daman abinci ya fi ba shi wahala saboda Camp ɗin Abuja ba ɗaya yake da Camp ɗinsu na Gombe karami ba wannan babban waje ne da ya tattara manyan yan wasan kwallo na ƙasa gabaɗaya duk wanda ka gani a cikin wannan kungiyar fitattace ne sannan ya kwarewarsa ce ta kaisa.
Shi ya sa ko yanayin traning ɗin su ba ɗaya ba ne, duk da akwai manyan ƴan wasa da ƙasa ta jima da sheda fuskarsa dama duniya gabaɗaya wasu yanzu suke cin zarafin su wasu kuma suna cin zarafin nasu har kuma wa'adin da za su yi ritaya ya cimma musu shi ya sa a ka ɗauki ire iren su Aji masu ƙokari domin maye gurbin su. A baya ba shi da burin zama a wani gari face jiharsa saboda Inna da kuma yanzu ya zama uba kuma mai mata, ko a yanzu da ya samu sauyin wajen aiki bai ji ko a ranshi wata rana zamansu gabaɗaya zai dawo Abuja ba, ya saka a ranshi duk matakin da zai taka a rayuwa jihar Gomb uwace a gare shi ba da Mama.
Ya kan yi sama da wata a Abuja wani lokacin ma sai ya raba wani watan ya ke zuwa Gombe ya ga Mimi da Ummi da Inna tare da sauran ƴan'uwansa sannan in ya dawo in ya daɗe ne kwana huɗu zai koma Shi ya sa sai zaman kaɗaicin ya yi ma Mimi yawa sai ta ke roƙon shi bayan ta tashi daga wajen aiki ko ta biya gidan Hajiya ko wajen Inna to shima ɗin ba kullum ba ranar da bai ga dama ba sai ya ce ta koma gidanta ta zauna in ta ce ba kowa sai yace ga Ummi nan, kada ta damu ita uwace yanzu kuma yanzu suka fara gina rayuwarsu a kwai lukatan da za su yi nesa da juna ba domin suna so ba, sai domin neman halas da kuma inganta zamantakewarsu ta nan gaba, ta maaa uzuri sanin halin shi ya na da Kulafacin gida amman tunda ta ga Aji ya hakura da zaman Gombe ya koma Abuja ta san ya ƙarbi canji da Ubangiji ya yi masa da hannaye bibbiyu.
Wani lokacin sai su yini ba su yi mgana ba, ya fi kiranta da asuba ko can wajen sha biyun dare lukatan da ya ke samun sukuni kenan itama sanin ba shi da lokaci ba ta takura masa da kira sai in har tana da mgana da shi mai muhimmanci da ta shafeta ko ta shafi Ummi ko inna, sai ta kira shi in ya zo ya ga kiranta zai kirata daga baya. Hakan ce ta faru yau ma tunda tun kwanaki a wajen aiki sun yi mgana da Manaja kan wani sabon shiri da Ma'aikatansu za ta ƙirkira shirin kuma na mata ne, mai suna matsalolin mu Ayau shirin da zai riƙa gayyato mata dabam dabam domin jin irin matsaloli da challages ɗin da suka fuskanta a rayuwa kuma ana so ita ta kasance presenter ta shirin gabaɗaya ba, ba ta amsa ba sanin halin mijinta ta ce sai sun yi mgana da shi, to ba ta samu sun yi mgana ba saboda karancin lokaci, yau ɗin ma ba su yi mgana a daran ba ta kira shi wayarsa a kashe sai da Asuba ya kirata ya ce sun shiga Meeting ne shi ya sa ya kashe wayarsa sannan ba gama da wuri ba shiyasa bai kirata ba a tunaninshi ta yi barci kada ya tashe ta ita da Ummi.