Sashe 82
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dakuna fuska ya yi kafin ya ce"To shi ne me? Jegon dai ba a haihu a taru a yi suna aci abinci ba ne? Ina ce shike nan an gama jegon.?
Ta na dariya ta ce"A'a sai na yi kwana arba"in ina jego a na kula da ni tare da mai sunan Inna, akwai dokoki ciki har da zama a É—aki mai É—umi."
Sai ta faɗa ya ji zafin ɗakin tunda ba fanka sannan an kashe Ac. Har gumi ya fara ma bai sani ba abun sai ya ba shi mamaki har sai da yace Topha, ya na koƙarin sake mgana ne Inna Zainaba ta yi sallama a Kofar ɗakin suka amsa mata sai ta shigo
Kai tsaye ta kalli Aji ta ce"To Baban Maryam mu kwana lafiya ko?
Kallonta ya yi cikin mamaki bai yi mgana ba,a gabansa ta kalli Mimi ta na faÉ—in"Za ki kara shiga ruwan É—umi kafin ki kwanta.".
Sai ta gyaɗa mata sai kuma ta ƙara cewa"Ga Kunin ki nan a fulas anjuma ki ƙara sha, Sannan wankan towel ɗin nan zuwa sati zai tsaya, ganye za'a samo min na daki jikin ki da shi."
Mimi ta zaro Ido haka ma Aji da bai bar ɗakin ba. Inna Zainaba ko a jikinta ta shige toilet domin haɗa ma Mimi ruwan dumi ba ta ciki da iskacin yaran zamani na fahimci Mijin nan na Mimi ɗan gadara ne, ta gama masa kara in ta masa lamunin ganin matarsa da ƴarsa minti goma ne za ta riƙa shigowa tana ganin abin da ke faruwa.
Aji ya kalli Mimi kafin ya samu damar magana ta masa alama da hannu alamun ya yi shuru sannan ta ce ya fita amman bai fita ba sai da ya dawo ya sumbaci yarsa da matarsa sannan ya fice yana faÉ—in"Sai da safe Ummu Maryam."
Amman har ya gama cin abinci ya na mamaki shi fa ya ɗauka wani ɗaki mai kula da Mimi za ta kwana shi kuma ya kwana tare da matarsa amman kuma sai yake jin wani karatu na dabam, da ya koma ɗaki ya saka kayan barci ya kwanta ya kira Mu'azzam ya na masa ƙorafi Mu'azzam na danne dariyan sa ya ce"Ai hakuri za ka yi Yaya sai in Anty Mami ta yi kwana arba'in sannan komai zai dawo dai dai.".
Aji ya ce" Haka ta ce, wai daman da gaske take yi? Ni kaÉ—ai zan rika kwana kamar wani mara gata, addini ne ya ce a yi haka ne?
Mu'azzam ya ce A'a nan take Aji ya yi tsaki kafin ya ce"To saboda wata al'ada sai a ware ni, ana gama taron suna zan ce kowa ya tafi a barni zan iya kula da matata da Æ´a ta." Mu'azzam na ta danne dariyansa amman ya san tunda yayansa ya faÉ—a zai aikata shi ya sa da asuba yakira Inna da shawaran Hibba saboda ta ce gwara a kwabe sa tun yanzu kada ya aikata ya bar mutane da jin kunya.
Inna na jin abin da Baban inna yake shirin aikatawa ta yi yar dariya kafin ta ce"Bar ni da shi, shi ya sa ya ce ba za ta je gida ba saboda ya yi wannan diɓar albarkar ko? To zan ce bayan suna ta koma gaban Hajiya sai naga karyan tsiya fitinannen yaro kawai sai kace a kansa a ka fara haihuwa."
Mu'azzam na jin haka da sauri ya ce"Kada ki yi haka Inna ki dai yi masa mganar don Allah kada ya yi wata mgana ya bar ƙanwar mamanta da kika ce tana wajen ta ta zauna ta kula da ita kin ji ko Inna? In ta koma gidan Hajiya an ƙwari yayana tunda shi baya ra'ayin ta koma can in kika matsa masa kamar an shiga haƙƙin sa ne."
Da waÉ—anan kalaman ya lallashi Inna Meri ta bar mganar cewa bayan suna Binta ta koma gida, amman da safiyar ta je can gidan duba Binta da takwaranta ta iske tuni sun sha wakan har sun karya ta samu Mimi na cin ferfesun kayan ciki ta iske su Mama a gidan su suka taho mata da shi.
Ta iske suna ta maganar yau da safe an samu ruwan nono har yarinyar ta samu ta sha, amman sai barci ta ke yi Mama ta ce" Daga gani rigiman dare za ta riƙa yi."
Inna Meri ta ce"Shima ai haka ya yi, na fi wata takwas da haihuwa Baban Inna bai daina kukan dare ba."
Ana ta dai raha ana dariya. Baya gidan tun safe ya fita zuwa Camp, dawowarsa kenan ya shigo yana gaishesu sai ya ga Inna bai ma san ta zo ba.
Daga nesa ya kalli Mimi ta kalleshi suka yi ma juna mirmishi, Sai a ka bar shi da tambayan Inna Zainaba yana faÉ—in" Ba wata matsala ko inna? Ko akwai wani abu da kuke bukata?
Cikin mirmishi ta ce"Ba ma bukatar komai, ai komai ai akwai shi sai godiya Allah ya ƙara buɗi na alheri."
Ya amsa da Amin kansa a kasa sannan ya miƙe ya fita sai Inna Zainaba ta ce Mimi ta ɗauki yarinya ta je su gaisa jikinta na rawa ta mike ta sunkunci yar amman sai da Inna Zainaba ta saka ta ta saka mayafi da takalmi daman kafar nan da safa tun da ta haihu ko'ina na jikinta ya na rufe Inna Zainaba jegon mutanen da take yi mata..
Aji har ya fara ƙorafin mutum da matarsa an barshi da kallo daga nesa sai ga Mimi farinciki yasa sai da ya rumgumeta yana sauke ajiyar zuciya. Ba ta daɗe ba tunda tasan halin Inna Zainaba amman sai da ta ɗauko masa abun ƙaryawansa ta jera mai sanan cafet a cikin Bedroom sannan ta koma ɗaki har magiya ya yi mata ta tsaya ya gama ƙaryawa tace a'a in ta daɗe za ta yi mata faɗa, daman bayan fitan ta sai da Mama ta ce" Yaran zamani jikinsu na rawa za'a je wajen miji."
Inna Zainaba ta ce"Su ko tausayin kansu ba sa ji."
Inna na gefe ba ta ce komai ba, ta san halin Baban Inna bai son kara ba.
Sai da ya yi wanka ya sauya kaya sannan yace Inna Meri ta fito ya kaita gida, Itama daman tana son mgana da shi, ta yi musu sallama akan anjuma Walida za ta kawo garin kuni, a hanya ne ta yi masa mganar ya rika kawaici sannan kada ta ji ya yi mganar bayan suna a watse in an barshi da matar da yarinyar zai iya kula da su ne? Ya na jin haka yasan Mu'azzam ne ya kai mgana wajen Inna bai ce komai ba, illah tura baki kafin ya ce" To Inna mutun da matarsa sai a hana shi ganinta."
Inna ta yi masa wani kallo kafin ta ce" Ka dai ji abin da na gaya maka, in ka ce ba za ka yi kawaici ba wlh zan ce a maida Binta gaban Hajiya sai bayan wata biyu sai ta dawo " Yana jin haka da sauri yavce"Allah ya baki hakuri Inna, In sha Allahu ba zan ƙara mgana ba"
Amma bayan ya sauke Inna, bai shigan ba ya juya a hanya ya kira Mu'azzam yana ce masa"Kai ba'a sirri da kai ko? Ban ƙara gaya maka wata mgana."
Tunda yaji haka ya san kan mganar yana koƙarin mgana yayan nashi ya katse kiran sannan ya kira shi daga baya bai ɗaga ba sai kawai ya ƙyaleshi za su daidaita daga baya.
A cikin satin da Mimi ta haihu kafin suna ko da yaushe gida cike da baƙi. Ba yan'uwanta ba na megidan ba, Khadi tun ana saura kwana biyu suna ta iso Madiha ma ta ce sai ranar suna za ta zo har da ƴan'uwan Mommy daga kano. Jawahir ma ana gobe suna ta iso ita da yara Rukky dai tana lagos ba za ta samu zuwa ba, amman har abokan aikinta mata sun zo mata barka sannan za su zo suna, mazan ma har gida suka zo su ka yi mata barka. Daman hutun haihuwanta sai bayan ta haihu zai fara aiki wattani uku kafin ta koma, kullum sai Magajiya da Gaje sun leka in da wani aiki su kama sannan Yaya Amina da Yaya Halima suna zuwa Bintu da ma Maeesha gwarama su Yaya Junmai suna fashin rana amman suma kan sun yi kokari Inna Zainaba sai yabawa take yi, ga uban gayyar kafin ma a bukace wani abun ya kawo shi.
Inna Zainaaba tana waya da Æ´ar'uwata lokacin da Mommy ta ce"Ina fatan ba wata matsala ko?
Inna Zainaba ta ce"Wlh babu Murja, Mimi ta yi dacen miji da danginsa masu karamci da mutunci komai da kika sani wlh sai dai ma mu yi kyautarsa. Mimi da Maryama ba abunda suka nema suka rasa waÉ—anan mutanen akwai karamci da kirki "
Mommy ta ji daɗi kwarai hakama khadi ta dinga faɗa, domin kayan Mimi da na jaririya duk safe Magajiya da Bintu ke zuwa su wanke sannan su dafa ruwan zafi su yi ma jaririyar wanka Mimi kuma Inna Zainaba ta yi mata. Bintu kuma da Maeesha suke gyara gidan su turarashi da kamshi.Su Yaya Amina kuma su zo su yi girkin rana da dare su Mama suna zaune suna hira ba abin da suke yi, duka yayyen Angon karni ne da ƙañensa ke yin komai yaddiko ma da ta zo sai da ta yaba musu, sannan Inna ma ta kan leko da safe, garin kuni haka ta yo shi da yawa ana damama Mimi har ruwan nono ga shi ya samu sosai.
Hajiya ma ta na gida labari ya zo mata Sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce" Meri basakkawata ce mai kirki, sanna yayanta sun samu tarbiya daga bangarenta, babu nadama ga haÉ—a zuru'a da ita."