Sashe 41
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Haka ya fara faɗa lokaci ɗaya yana ƙara daƙune fuskarsa kamar wanda aka faɗa masa wani mummunan saƙo, Mimi ta kalli Rukky itama ta kalleta a ranta dai sai da ta ce mai hali baya fasa halinsa amman a fili sai ta haɗe rai itama ta juyar da fuska tana faɗin" Wa ya gaya maka na dawo? sannan me yasa ka zo ba Sanarwa?
Ta faɗa tana wani masa jijjigan jiki lokaci ɗaya tana taɓo hannayen Rukky wacce ta dukar da kanta ta ƙasa ta kasa ɗagowa saboda Aji ya yi mata ƙwarjini ba ta ɗauka za ta kasa haɗa ido da Ajin in suka haɗu gaba da gaba ba.
"Alhaji ne ya gaya min kin dawo. Sannan domin zan zo wajen matata ai ba na bukatar ɗan saƙo."
 Haka ya ce mata yana kallonta cikin ƙara nazarinta da sauri ta kallesa kafin ta ce" Wani Alhajin? Kafin ya samu damar magana ta zaro ido tana faɗin" Wai Daddy ne Alhaji? Ba za ka iya kiransa da sunan Daddy ba kenan?
Ta faɗa cikin masa wani kallon kasa ƙasa, cikin mamakinta ya ce"Daddy kuma? To ai kinsan ni a gidan da aka haifeni da in da na taso, Inna da Baba muke cewa, in kin ji mun ce Alhaji alamamun girmamawa ne."
Ita kanta ba ta san ta masa wannan kallon ba sai da ta ga ya yi mirmishi wanda tun zuwansa wajen bai yi ba sannan ya ce"To na bari, Daddy ba shike ban ba?
Sai ta gyaÉ—a masa kai, kawai sai ya gyara tsayuwa a ransa ya na faÉ—in"Rigimammiya kawai."
Rukky ce ta ga kamar Har Mimin ta manta da ita. Sai ta matsa gefe tana faÉ—in" Mimi zan tafi, yamma ta yi"
Ta gama faÉ—a lokaci É—aya tana duba agogon fatan dake tsitsiyan hannunta na hagu sai a lokacin Mimi ta tuna da ita domin har ga Allah in tana gaban Aji mantawa take yi da kowa da komai ciki har da ita kanta ma.
"Aji ga ƙawata Rukkaya, Rukky ga Aji ku gaisa."
 Mimi ta faɗa cikin Mirmishi tana kallon su duka, Aji ya yi shuru yi ya yi ma kamar bai ji ba sai can ya ce"OH na ganta."
Daga haka ya juyar da kansa yana kallon wani ɓarayin Rukky ta watsa ma Mimi wani kallo ita kuma tana faman roƙonta da hannu a kan ta gaishe shi abin da ba su sani ba duk yana kallonsu ta gefen Ido, abin da ya bashi mamaki ita yanzu ƙawar Fatima Jira take yi ya gaisheta? Amman yarinyar ba ta da hankali ya fara tunanin haka.
"ina yini"
 Haka Rukky ta faɗa Kamar ba ta so. To daman dole Mimi ta saka ta, sai da ya nishaɗu sannan ya juya yana kallonta lokaci ɗaya yana faɗin" Barka da ƴamma"
Sannan sai ya juya yana kallon Mimi kafin ya ce"Na É—auka tana jiran na gaisheta ne."
Sai Rukky ta ji kunya ya kamata da sauri ta ce"A'a na bari ku gama gaisawa ne."
"Gaisawa? da wa? Ba gaisuwa muke yi ba ko kin ji sanda ta gaishe ni?
Sai Rukky ta kasa mgana shi kuma sai ya cigaba da faɗin" Ko ita ƙawar taki ba ta isa ta zauna in gaisheta ba, koda nake auranta ba ta isa ba."
 Daga Rukky har Mimi kai suka jinjina, kafin Rukky ta ce"Ta cancanci ka gaisheta mana, ka fa ba ma ƙawata wahala."
Ta faɗa tana yar dariya mirmishin gefen baki ya yi kafin ya ce" Ita kaɗai? ba ta gaya miki nima ta ba ni wahala ba? Mun ba ma juna wahala shi ne gaskiyan magana."
Ya faɗa yana kallon Mimi ita kuma sai ta harareshi ta na tura masa baki har sai da ya yi yar dariya Rukky na tsaye tana kallon Ikon Allah a tunaninta Mimi ba za ta sakar masa fuska a zuwan farko amman kalli abin da take yi. Shi kuma agogon hannunsa ya duba kafin ya kalli Mimi ya na faɗin" Kina da mintina goma,ki sallami baƙuwar ki, ina son mgana dake."
Yadda ya yi maganar cikin ba da umarni ya sa Mimi ba ta ga damar masa musu ba sai ta ce ya shiga falo ya jira ta bari ta taka ma Rukky kamar zai ce rakiyar ba ta isa haka nan ba sai ya fasa bai shiga cikin gidan ba ya tsaya nan yana jiranta daga in da yake suka matsa gaba kaɗan yana gani Rukky na ta magana Mimi na marairaicewa kamar hakuri take ba ta shi fa baya raba ɗayan biyu duk abin da Mimi ta aikata ba tunaninta ba ne tunanin wannan ƙawar ta ta ce, kuma daman tana da fuska da yanayi na munafukai.
 Dole Mimi ta sallami Rukky ganin uban gayyar ya kasa ya tsare ta na fita daga get ɗin Mimi ta dawo wajensa tana faɗin" Ba ka ciki ba ?
Kai tsaye ya ce"Ke nake jira, sannan kada ki ƙara fitowa a haka ba ki saka babban mayafi ko hijabi ba."
Baki buÉ—e ta ce" A cikin gidan?
Kansa ya É—auke kafin ya ce"E na dai gaya miki."
Yanayin yadda ya haÉ—e rai ne ya sa dole ta yi shuru tana gaba yana Binta a baya har zuwa falon gidan Hajiya ta ce ya zauna sai ya samu kujera mai zaman mutum biyu ya zauna ita kuma ta ce tana zuwa.
Sai ta juya tana tafiya ya bi ta da kallo yana haɗiyan miyau har ta ɗauke ma ganinsa Ajiyar zuciya ya sauke dole ma ya ijiye duk makaman yaƙin sa matarsa yake bukata cikin lokaci.
 Ɗakin Hajiya ta fara shiga ta isketa tare da Baaba Uwani suna mgana ta gaya mata zuwan Aji sai ta koma ɗakinta domin ta gyara fuskarta, ita kuma Hajiya ta fito tare da Baaba Uwani ta gaishe shi ya amsa cikin yanayinsa sannan ta shiga kitchen ta kawo masa ruwa da lemu, Hajiya kuma har kasa ya sauka ya gaisheta ta na masa tsiyan ba ta ce in Binta ba ta son auran ita a zo a yi da ita ba kansa na ƙasa ya ce shikeman in ta ƙi komawa sai ya zo kawai su daidaita Hajiya na ta dariya bayan tambayan su Meri ya ce tana gaisheta kai tsaye Hajiya ta ce"Ai ka gaya mata na ce na yi fushi, tunda abun nan ya faru ban ganta ba sannan ba ta kirani ba." Mirmishi kawai ya yi ba tare da yayi wata magana ba, nan Hajiya ta bar shi ta shige ciki ta je ta na yi ma Binta tsiyar ta shanya shi, ita kuma har kaya ta sauya daga baya sai ta fasa domin zai ɗauka ta hakura ne tunda har da kwalliya sai ta maida wanda ta cire har da saka uban hijabi sanda ta dawo falon yana zaune ya gama shan ruwa kenan kujeran dake kallonsa ta zauna shi kuma ya na kallonta daman tun shigowarta. Cikin mamaki ya ce"Wannan hijabin fa? fita za ki yi ne?.
Kai tsaye ta ce"A'a ba kai ka ce na riƙa saka hijabi ko a cikin gida ba ne?
 Dariya ta ba shi har sai da ya dara sannan ya kaɗa kai kafin ya ce"Kin yi nesa da ni, ta ya ya za ki iya jin abin da zan faɗa? Ki matso nan domin ba zan ɗaga murya ba."
Ya faɗa yana nuna mata kujeren dake gefensa mai zaman mutmn uku ba musu ta miƙe ta koma nan ta zauna sai da suka ɗauki wani lokaci kowa na sake saƙe sannan Aji ya yunƙura kaɗan yana faɗin"Ina fatan hutun da kika yi ya ishe ki?.
Kallon bangane ba ta yi masa sai ya cigaba da faÉ—in" Na san ban kyauta ba. Mu manta abin da ya faru a baya Mimi ki dawo gare ni domin na nuna miki komai ya wuce."
Kai tsaye ta kalle shi domin ta ga da gaske yake yi sai kawai ta kauda kai kafin ta ce"Ni fa na É—auka takardan saki na ka kawo min."
"Subhanallah, ki daina wannan zencen ni ban aureki domin na sake ki ba"
"To ana dole ne? tun da ka ce ba ka sona? Sannan ba za ka iya daraja iyayena ka manta abin da ya faru saboda ni ba, ni ma kuma ban ga laifina domin na ce ba zan cigaba da zama da kai ba."
 Yadda take mganar da alamun abin na taso mata ne domin kamar za ta yi kuka, huci ya fitar daga bakinsa kafin ya ce" ɓacin rai ne ya sa duk na faɗi wasu mganganun, ki yi hakuri."
Mamakin yadda ya yi saurin laushi ta yi sai ta kalle shi shima ita yake kallon cikin irin kallon nan mai kassara oafiyan jikin ƴa mace, ita ta yi saurin kauda kanta kafin ta ce" Wasu mganganun? kamar su wanne kenan?
Bakinsa ya ciza leɓen kasa kafin ya ce"Na ƙaryata kaina Mimi, ke sai ki yarda cewa ba na son ki?
Ya faÉ—a cikin wani sauti ba ta son kallonsa Saboda kada ya ga rauninta kanta na gefe ta ce" Na yarda tunda da bakin ka ka faÉ—amin alfarman Hajiya da Mommy nake ci."
 Bai san ya aka yi ba shi dai kawai ya gansa zaune kusa da Mimi kafaɗanta na dukan Kafadansa haka itama taji mutum zaune gefenta kafin ta samu zarafin mgana ta ji kawai ya yi mata wani irin riƙo mai karfi lokaci ɗaya yana faɗin" Shike nan kuma sai ki yarda da duk abin da na ce? Ke ba ki san bacin rai ba? Raina ne ya ɓaci shi ya sa na faɗi haka."
Ya faÉ—a cikin sanyin murya ta É—ago tana kallonsa shima ita ya ke kallo,ta buÉ—e baki za ta yi mgana kawai ya saka hannunsa samman bakin yana faÉ—in" Shiii."
Sannan ya hura mata iskar hucin zafin ɓakinsa kusan suman zaune ta yi kafin ta dawo hayyacinta ya yi mata magana cikin raɗa raɗa kamar wanda ba ya so a ji.
"Ke ce ta farko, ke ce ta biyu ke ce har ta uku da ta huɗu. Sannan ke ce a baya da shekaranjiya yau da gobe har da jibi da gata, ke na zaɓa ke ma kinsan ba zan iya daina son ki ba Fatima."