Sashe 76
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Mommy ba ta zo ba amman suna mgana ta waya, Mama da Anty har Daddy ya zo gida dubata shi ya ce a bar mata Baaba Uwani ta zauna da ita Hajiya ta ce itama me ta ke yi a gidan? Mansoor kuma ya ce har Hajiyan don Allah su zauna tunda Walida ba ta da lokaci yanzu. Yadikko ma ta zo ita da iyalanta su Anty Amina da su Bintu ma duk sun zo. Su jummai da su Zuwaira har Maeesha da matar Auwalu.
Magajiya da su gaje sun zo duba ta, kuma taji daɗi kwarai yadda suka nuna mata kulawa shima kanshi gogan rawan jiki kawai yake yi, Nasir da su Makama duk sun zo dubata Rukayyan kusan kullum tana gidan. Zaman Hajiya da Baaba Uwani ya daidai ta Mimi da Aji, tunda dole ta bar musu ɗakin ta koma ɗakin Aji tana kwana kuma suna gidan ai ba za ta masa horon da ta saba a gabansu sai ta ke nuna komai lafiya sai sun shiga ɗakin ta yi masa gum Ranar dai ya gaji cikin dare ya miƙe ya kunna hasken ɗakin ya ta da Mimi, ta tashi tana sosa idanuwanta cikin sanyin ta ta ce"Me ya faru?
Gurfana ya yi daga saman gadon a gabanta ya ba ta kanshi lokaci ɗaya yana daɗin"Gani ki yi min duk abin da kike ganin za ki wuce, na gaji Fatima kina horani wlh na tuba ba zan ƙara ba."
Ya faɗa kamar zai yi kuka idanuwansa sun kala yana bukatar matarsa amman sama da wata ɗaya Mimi na masa kisan munmuƙe.
Kallonsa ta yi kafin ta kauda kai tana kokarin komawa ta kwanta da sauri ya rikota ya jawota jikinsa ya kamkameta ya na Faɗin"Kin ce kin yafe min amman ki duba abin da kike yi min? Ba ki yi min mgana ba na ganin dariyan ki. Ni fa bayan ganin ki a tare da ni ina bukatar ganin ki cikin farincikin ba na jin daɗin ganin ki haka don Allahi ki yi hakuri mu koma kamar baya."
Mimi kwallah suka cika mata ido cikin rawan murya ta ce"Me zan maka? Na kasa manta maganganunka ne Aji, da bakin ka kace tabbaci gare ka a kaina ba zargi ba ne. Ni wai na ke cin amanarka? Ni wai haba don Allah ban yi lalacewa tun ban da aure ba sai da na yi aure zan lalace? Me ya sa ba ka za kamin uziri ba? Ni ba ka yarda da ni ba? Kai ne fa ka taɓa sanina a ƴa mace amma har kake so ka saka zargi a zaman aure mu Saboda ina sonka ina kiyayema duka dokokinka komai ka ce in yi shi nake yi saboda mu zauna lafiya amman duk ban tsira ba, ka ce wai kana da tabbacin ina cin amanarka.. Aji ni ce fa Mimin ka ni? Abunda ya fi min baƙin ciki shi ne yadda ba ka yarda da ni ba, sannan kana mijina wanda ya fi kowa sanina ka kasa iya shaidata to waye zai yi shaida ta?.
 Tana mgana ta na kuka saboda abun in ta tuna sukan ranta yake yi, Aji gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi haka ya kara kamkame Mimi shima kamar zai yi kuka yana faɗin" Wlh sharrin sheɗan ne da kuma sonki, ina sonki Fatima shi ya sa nake kishin ki."
Cikin kuka ta ce"In kana kishi na sai ka bari ka kasa yarda da ni? Haba don Allah shekara nawa muna tare? Ka rika sarrafa zucyarka sannan ka rage kishin ka, ka tuna sanda ka ɗauke ranga ranga zuwa asibiti ka manta likitan namiji ne ya dubani a lokacin ba ka damu ba saboda lafiyata kake nema, To haka za ka rika hakuri da rayuwa dole zan fita wasu za su ganni kai ma za ka fita za ka ga wasu abunda kawai za ka saka a ranka shine ka yarda da ni, ko bayan ba idanuwanka ni mai tsare maka amana ne amman wlh abunda ka yi min yasa min bakinciki a zuciyata sannan kuma yasa na rage ganin ka yadda nake ganin kaa cikin Idanuwana."
Haka ta faɗa tana kuka, Aji ya ruɗé yana faɗin"Don Allah kada ki daina sona Fatima, in kika gujeni wa zai so ni? Zan gyara halina zan riƙa sarrafa zuciyata da kishina amman kada abunda ya faru ya sa ki ji kin tsaneni."
Mimi ba mgana sai kuka shi kuma ya na ta ban hakuri kamar zai mata kuka. Tabbas ya yi nadama kuma ba zai yarda ya ƙara aikata abin da ya aikata ba.
Itama tana son mijinta duk da wasu hallayan na shi ba su da kyau.Sai dai ai daman É—an adam tara yake bai cika goma ba, a komai ba za ka ce ka samu abu É—ari bisa É—ari ba. Ko 50% ka samu sai ka yi hakuri da shi, tunda har ya Ffhimci bai kyauta ba ta na da tabbacin gaba ba zai kara yarda ya aikata abin da ya aikata a baya ba.
 Sai ta rumgumeshi cikin shesshekan kuka ta ce" Shi mgana zarar bunu ce, kuma wata mganar ta fi kaifin takobo kaifi, in ka caka ma mutum zata huda cikinsa har ta fita ta waje, ka daina barin ranka na ɓaci kana faɗin mganganu mara kyau a kan abin da ka ke so, wata rana za ka cutar da ni cutar da bazan iya yafe maka ba."
"In sha Allahu ba zan kara ba."
Da haka ta yafe masa ta kuma yi alkwarin manta abin da ya faru amman ta ce ba yanzu ba sai a hankali za ta iya manta abin da ya faru.
Shike nan ma'auranta suka shirya, amman duk da haka Mimi ba ta sakin jiki da Aji, in ta tuna kalamansa a kanta sai gwiwanta ta yi sanyi shi dai ko da yaushe ban hakuri ne.
Satin Hajiya biyu suka koma gida tunda Jikin na Mimi ya yi kwari, ta na yin amai amman ba sosai ba.
Kasala ne dai da jiwa shima ba sosai ba. Sai zazzabin dare shima ya yi sauki sai dai ta yi fari fayau ta kuma rame.
Sama da wata ɗaya sannan Mimi ta koma aiki. Gogan ya yi sanyi yanzu yana gani za ta saka mayafi ta fita sai dai ya kauda kai tunda ya yi alƙwarin yarda da matarsa kafin kishin sa a gaba, itama kuma tana yi domin ta ga ko da gasken ya daina abunda yake yi.
Da gangan take saka abaya ta sha rolling ta wuce, baya mgana amman dai ya kan ce" Abaya tana nuna sufar jiki ko za ki saka hijabi ne Mimi?
Sai ta kalle shi ta ce"Sai in saka É—in in kana tunanin har yanzu ba ka yarda da ni ba."
Da ta ce haka sai ya ce Allah ya ba ta hakuri, In sheɗan ya saka masa wani tunani sai ya yi saurin yin ta'awizi ya kuma tuna cewa ba yadda zai hana Mimu fita to saboda haka sai ya yi hakuri da wasu abubuwam
 Mimi kuma sai harabasa take yi ta ga ko zai kara yin wani abun amman sai ta ga da gasken ya gyara halinsa. Kuma har a lokacin ba ta gaya masa Alaqar Jaheed da Rukayya ba har manya sun shiga mgana abu ne daman me za'a jira? Har an saka rana wattani shida amman dole Rukky za ta bar aiki da karamci Jaheed ya ce a can zai nema mata aiki. Sai dai Mimi ta ba ma Aji mintin saka ranar Rukayya da Jaheed
Baki sake y ace"Mimi abokin nawa fa?.
Kai tsaye ta ce"Ya tsaya wasa. Ga É—an gaske nan ya zo ya É—auka."
Nasir kam da kanta Rukayya ta gaya masa, Ya damu tunda shi a tunaninsa ta na jiransa ya daidaita da iyayensa ne.
Jin ga wanda za ta aura ya sa Nasir ya ce"Ni miye laifina da zai huce a kaina ya kwace min dudurwa."
Aji ya yi masa rantsuwan Mimi ba ta faɗa masa. Kuma saboda ta kure shi har gidan ta sake gayyato Jaheed, tare da Rukayya ba tare da ta gaya masa ba domin ta ƙara jaraba nadamarsa.
 Ko da ya dawo ya gansu bai nuna mata wani abu ko a fuska ba, sun yi masabaha da Jaheed har ya bashi hakuri kan abunda ya faru a baya shi kuma ya ce komai ya wuce shima ya na mai bashi hakuri.
Rukayya sai a lokacin ma ta san an samu rashin fahimta ba ta yi mamaki ba, ita kawar Mimi ce ta san kishin Aji a kanta.
Ita kam har ya na zolayanta da cewa ta yaudare su ta ce su ne suka yaudare ta.
Sai yamma suka tafi, Aji bai yi ma Mimi mgana sai da daddare bayan sun kwanta ya kalleta yana faɗin"Fatima, wai ke nan har gobe ba ki yarda da nadama ba! Ba ki amince da na ce bazan ƙara ba?
Sai ta yi shuru ba ta yi mgana Mirmishi ya yi ya na rumgumeta lokaci ɗaya yana Faɗin"Abin da nake so ki gane har abada ba zan daina kishin ki ba Fatima, ina sonki ba na so kuma ki kasance abun burgewa a idanuwan wasu mazan, gwajin ki a kaina ba shi zai saka ki gane nadamata ba, in na ce zan bar abu to kokari na ke yi na yi yaƙi da
zuciyata a kan haka, na fahimci yarda shi ne kan gaba akan kishi shi ya sa na aminta da ke, ina son ki kuma ba zan daina kishin ki ba kema ina rokon ki aminta da ni kin san ina sonki ina kishin ki. Don Allah ki kiyayewar motsawar zuciyata Mimi"
Ƙara shigewa jikinsa ta yi lokaci ɗaya tana faɗin" In sha Allahu Merapyaar.."
Ya na mirmishi ya ce"Sunan Indiya kuma a ka saka min?