Sashe 68
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
 Mimi ta ƙwala sunan shi cikin karfi da karkarwa ba in da jikinta ba ya rawa, Idanuwanta har sun fara zubar kwallah ta nuna kanta Lokaci ɗaya tana faɗin"Me ka ke nufi? Kana nufin kana zargina ne da Jaheed?
Kai tsaye ya ce"Ba zargi ba ne tabbaci ne, saboda ga shi nan tare kuka dawo kuma Saboda ba ku da kunya a gaban idanuwana yake taɓaki ai dai kwaji kunyar aikata son ranku a gaban idanuwana amman da yake damman an ce mara kunya ya aikata duk abin da ya ke so. Ya yi miki kyau."
Ya karishe faÉ—a cikin fusata Jaheed ya buÉ—e baki zai yi mgana Mimi ta hana shi. Kukan bakinciki take yi da har gobe Aji bai yarda da ita ba, da zai yi tunanin za ta iya cin amnarsa da wani namijin?
Ko ya yi nadaman kalamansa saboda Idanuwansa ya rufe yasa ya ce ta juya su koma in da suka fito, ba musu ta juya za ta fita Jaheed ya ce"A'a Mimi ki tsaya na yi masa bayani."
A Fusace ta ce" Sai ka tsaya ko ba ka ji abin da yace ba ne? Tunda ya na zargina babu amfani zama da wanda ba zai iya shedar ka ko a bayan idonka ba."
Daga haka ta fice Jaheed da Aji suka kalli juna kafin Jaheed kaɗa kai yana faɗin" Ina jin tsoron wannan kishin naka kada ya lalata muku aure, ya kamata in rai ya ɓaci hankali ya nemosa, sannan ka sani in an ciza a hura saboda kada rashin hurawar ya taho da nadama."
Ya na gama faÉ—in haka ya juya ya bi bayan Mimi da sassarfa, Aji sai ya tsaya yana kallon in da suka bi a cikin zuciyarsa yana faÉ—in"Sai kuma ta bi shii É—in suka fita?
Bai ƙara dawowa hayyacinsa ba sai da ya ji ƙaran buɗw get yana leƙawa ta window ya ga motar Jaheed ta fice daga gidan.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3016*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Sheɗan ya shiga hasko masa su cikin yanayin da bai kamata ba, kenan ta zaɓe shi a kan shi,?
Sun koma su cigaba da abin da suke yi kenan? Wani irin tururi ya ji yana fitowa daga cikin zuciyarsa har ya na jin hucin zafin a cikin fatar jikinsa, bakinsa ya saki iskar na fita yana ta kuma sakin hucin da sauri sauri ga sanyin A.C ga na fanka amman gumi na ke tsattsatso masa kamar wanda a ka watsa ma ruwa. Bai san lokacin da ya dungule hannanunsa guda ɗaya ya daki bangon ɗakin da shi ba.
 Ya ji radaɗin har a tsakar kansa daga. Har sai da ya yarfe hannu nasa saboda azaba. Cije baki ya yi kafin ya kalli hannun nasa ganin ya sale har ya fara jini kan kujera ya koma ya zauna ya na ƙokarin daidaita numfashinsa da ke fita da zafi sannan a kai a kai kamar wanda ya yi gudun tsere, yana nan a zaune nan ba abin da sheɗen bai saka masa ba har tunani ya yi daman raba musu jiki Mimi take yi shi da wannan tsohon saurayin nata? Ya kasa tuna waye Fatima a wajensa? Ya kasa tuna matsayinta a ransa ya kasa tuna shi ya karɓi ƴan matancinta, ya kasa yi mata kyakyawan sheda saboda kishinsa na banza da wofi ya saka zargi a cikin auransa.
 Duk da haka ya kasa samun natsuwa. Har waya ya ɗauka zai sake kiranta amman ya fasa ya kuma kasa fita ko'ina ya na gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, tunaninsa bai hasaso masa me zai faru ba, a tunanin shi duk in da ta je za ta dawo, in tana kunya ba za ta bari wani ya san abin da ta aikata ba.
Yana gidan a zaune a saman kujera a cikin falon yana kallon ƙofar falon, motsi kaɗan zai ji zai ta shi ya leƙa ta window amman Har mangariba ba Mimi ba dalilinta sai ya fara tunanin ina ta bi shi suka tafi? Gidan Hajiya? An ya za ta je can kuwa?
 A lokacin idanuwansa sun rufe ya kasa sarrafa zuciyarsa har sai da ya ga an yi isha'i tara ta kusa na dare sannan nadama ya fara shigarsa ya fara tambayar kansa da me na aikata kenan?
Cikin Rawam jiki ya É—auki waya ya kirata amman sai ya samu wayarta ta na kashe, kansa ya dafe da ke sara masa a karon farko ya furta" Hasbunallahi wa'imal wakel."
Ya aikata kuskure babba. Zafin zuciya da kishi sun saka Mimi ta zaɓi wani namiji sama da shi, hankalinsa ya dawo jikinsa ya na tuna kalaman da ya je fa mata, Ya san Mimi mai tarbiyace duk abin da ya ke tuhumanta a kasan ranshi yasan ba za ta aikata ba amman sheɗan ne da bakar zuciyarsa suka kaisa suka baro sa.
Tunanin kiran Hajiya ya yi, amman kuma sai ya fasa saboda kunya me zai gaya mata in Har Mimi ta je ta faɗa mata mganganun da ya yi a kanta? Kansa ya dafe ya na faɗin"Aji me ya sa ka yi haka? Sai yau ya fara jin haushin kansa da haushin wannan zuciyar tasa, sannan ya fara tunanin kishinsa zai saka wata rana ya aikata wani abun da zai dawo yana kuka da idanuwanshi saboda nadama. Ko abinci ya kasa ci, ruwa ma bai iya saka ma cikinsa ba, barci kuma sai dai ɓarawo amman kusan raba dare ya yi a falo idonsa biyu wayar Mimi kuma ya kira bai san adadi ba har ya gaji ya tura mata saƙo.
_Don Allah Mimi ki yi hakuri ki faÉ—a min in da kike sai na zo mu yi mgana. Ki tausayamin sharrin sheÉ—an ne_
 Tunaninsa Allah ya sa ba gidan Hajiya ta je ba. Sannan Fatansa ya sa ko kila gidan kawarta Rukayya ta je, amman in har ta je gidan Daddy ta faɗa masa, to shi fa ba shi da bakin kuma da zai iya kare kansa wannan karon.
*****
MIMI.
Bangaren Mimi kuwa tana zaune a bangaren mai zaman banza a motar Jaheed amman ban da kuka babu abin da take yi, kuka sosai mai Sauti fuskarta ta yi chaɓa chaɓa da hawaye har da majina Jaheed na bata hakuri amman kamar yana ma ƙara zuga ta ne.
"Mimi don Allah ki daina kuka, kin ga fa halin da kike ciki, ba ki da lafiya na ce miki mu koma ki ba shi hakuri mu yi masa bayanin abin da ya faru."
 Mimi ta dago fuskarta duk hawaye cikin Kuka ta ce"Ba ya bukatar wani bayani Jaheed da kunnen ka ka ji ya ce ba zargi ya ke yi ba, tabbaci gare shi a kan ina cin mmanarsa tare da kai, abin da ya fi min baƙin ciki ace yau mijin da kake so kuma ka ke aure shi ne ba zai iya shedar ka ba. Yau ni Aji ke kira da lalattaciya ina lalacewa da wani namijin Alhalin nasan ina da aure wannan abun ya fi komai baƙan tamin rai."
 Tana gama faɗin haka sai ta ƙara rushewa da kuka Jaheed ya girgiza kansa cikin damuwa kafin ya ce" Gaskiya bai kyauta ba, bai kamata ya yi haka ba."
Daga haka sai ya yi shuru saboda shi ya ma rasa abun faÉ—amSuna tafe Mimi na cigaba da kuka Rukayya ta kira wayar Jaheed bai É—auka ba saboda kukan Mimi sai ya maida wayar a silent.
Kuka take yi ta manta ma da in da take sai dai kawai ta ga Jaheed na hon a bakin get ɗin gidan Hajiya sannan ta dawo cikin hayyacinta. Da sauri ta kalli Jaheed hankalinta a tashe lokaci ɗaya tana faɗin" A'a mu juya Jaheed ba zan je ma Hajiya cikin wannan yanayin ba."
"To ina za ki je?
Ta yi shuru kafin ta ce" Mu je gidan su, wajen mahaifiyarsa."
 Jaheed ya kalli Mimi kafin ya ce"Me ya sa sai can? Kai tsaye Mimi ta ce"Ba na so wani acikin dangina ya san abin da ya faru, kowani aure ya na da nashi ƙalubalen Jaheed. Gwara na je wajen mahaifiyarsa a kan na je ma Hajiya ina koke koke."
Sai ya jinjina kai alamun gamsuwa har Megadi ya leko ganin motar Jaheed ya buɗe get amman sai ya ga ya juya kawai ya mike bai shiga gidan ba cikin mamaki ya bi motar da kallo kafin ya koma ya rufe get ɗin bai lura ma da Mimi da ke gaban mota ba a tunaninsa ƙila wani uzirin ne ya sa bai shiga gidan ba.