← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 93

Sashe 52

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*

Sallah da kwana uku mai gyaran jiki ta fara zuwa gida yi ma Mimi, kuma gashi in an fara ba'a san ana yawaita zirga zirga in da ma Allah ya taimake ta a satin sau uku take da karanta labarai, sai ta samu natsuwa amman duk ranar da za ta fita dogon hijabi da safa fuskarta ne kaɗai a waje kuma kowa ya ganta sai ya yi maganar ta ƙara kyau da fari har da su Aisha Farida iyayen gulma waɗanda Rukky daman ta gaya musu mijin Mimi yana nan yana danƙara mata wani katon gida, sai bakin su ya mutu daman can suna ta faman yawo da mganar ita ko Mimi har yanzu  tana nan a wannan gida kamar a kurki?

   Tun da ba wanda ya san abin da ya faru ya sa daga Rukky sai na jiki jiki. Ba wanda Mimi ta yi maganar da shi, sai dai ma na faɗan cewa za ta koma sabon gida. An shirya daman za'a yi waliman sauka a gidan Aji kuma daman ya ce za'a yi Saukan Qur'ani a gidan kafin ta tare,  daga shi har ita ba su da sukuni ita tana ta fama da shirye shirye. Shi ma kanshi baya samun zama tun salla ba su ƙara haɗuwa ba sai dai su yi mgana ta waya. Tuni har ta karɓo ɗinkunan da ta ba da ɗinki. Maganar kayan gida kuma daga waje Mommy wannan karon ta yi mata Oder bayan sun yi mgana da Daddy, Cikin Satin nan ma kayan za su iso. Sai turarukan wuta na jiki da na ɗaki, duk da ta lna da su amman ta siya wasu ta ƙara domin wannan karon ba auran wasa za ta je yi ba, auran ne da gaske take kuma fatan har Abada ya zama mutuwa ce za ta raɓa.

  Gyaran jikin sati ɗaya a ka yi mata. An yi mata dilka da halawa, masha Allah Mimi ta yi wani irin kyau, fatar ta ta yi wani irin silɓi da tsantsi. Ta ɗan dakata da zuwa wajen aiki tunda ta samu izinin Manaja da cewa za su tare a sabon gida akwai shirye shiryen da za su yi. Sai ya ba ta sati ɗaya shi ya sa suka samu lokacin zuwa kunshi da gyaran kai ita da Rukky. Wacce ba ta da zence sai na Nasir, Mimi ta gaji ta ce"Wai kuma kike ta yaɓon Nasir. Bayan kin gama zaginsa da cewa ɗan renin wayau ne." Sai Rukky ta harare ta kafin ta ce"Ba na son sharri, lokacin kafin mu fara mu'amala ne na san shi sosai."
Mimi ta kalleta a karkace kafin ta ce" Ikon Allah! To Allah ya tabbatar mana da alheri."
Rukky ta amsa da Amin tana murgaÉ—a baki, Tunda Nasir dai ya yaÉ—a manufarsa kuma ta amsa masa.

  Gyaran kai Mimi ta fara yi sannan sai washegari tun safe suka tafi kunshi, ba da motar ta ta je ba ga shi kuma sun yi dare dole Aji ta kira ya zo ya ɗauke su. Tare da Nasir suka zo ita dai Rukky a hannanye a ka yi mata. Ba su bi su Mimi a daidaita Nasir ya tara zai raka Rukky gida, sai da suka hau kan titi ne Mimi ta kalli Aji lokaci ɗaya tana faɗin" Abun mamaki, Nasir wai aure zai ƙara?
Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce"Ikon Allah me? Ai ba abun kunya ba ne, ko kawar ta ki ta fi karfinsa ne.?
Mimi ta kama baki kafin ta ce"Ni ban ce ba, kawai dai ina mamaki ne.Duka duka fa na ga Yayansa biyu ne, kuma zai ƙara aure sai na ga kamar ya yi sauri da ya ƙara aure."
A kaikace Aji ya kalli Mimi kamar zai yi mgana sai kuma ya fasa. Sai ya kauda mganar da cewa" Yau masu aiki fenti suka yi , zuwa gobe za su ƙarisa."
Mimi ta jinjina kai kafin ta ce" Aikin ya yi sauri gaskiya. Daman Gobe za'a kawo kaya, Mommy ta min mganar in da za'a ijiye kayan, na ce daman zan maka mgana in an gama gidan sai a je a gyara a sauke kayan a can kada ya zama wahala biyu."

  Aji ya yi shuru kafin ya ce" A'a sai an gama daman na saka Baba ya samo waɗanda za su yi sauka ina so kafin a fara komai sai an gama saukan Qur'anin da na ce miki." Cikin gamsuwa Mimi ta ce"To ba matsala, Allah ya nuna mana."
Sun ƙarisa gida kenan Aji ya kalli Mimi kafin ya ce" Ina Atm ɗina? gabana na ta faɗuwa na san gabaɗaya kin gama kwashe min tattalin arziƙina."
Mimi na dariya ta buɗe karamar jakarta ta ɗauko ta mika masa ya karɓa lokaci ɗaya ita kuma tana faɗin" Na gode Mijina, Allah ya ƙara arziki da wadata."
Ya amsa da Amin yana yi mata wani kallon ƙasa ƙasa kafin ya ce"Dole ki yi min addu'a mana tunda kin gama ƙwaçe min ƴan kudaɗe na."

  Yana dariya tana taya shi, sun ɗan jima a Motar suna Hira kafin ya rakata har kofar falon Hajiya sai da ta shiga gida sannan ya koma ya shiga motarsa ya bar gidan ita kam Mimi wani abu ne ke ba ta mamaki duk irin rawan kafa nan na matasan zamanin nan Aj ba shi da shi, ko dai ba shi da lafiya ne? In ya zo fa daga rike mata hannu in ya yi abu mai nisa ne ya rumgumeta, ita ce ma take sumbatarsa wani lokacin, ba ya wuce gona da iri sannan yana da kiyayewa har tunanin Ko dai ba shi da lafiya ne duk ta yi shi, bayan ya koma gida ya kirata sai da ta yi masa mganar da cewa.

  "Wai ba ka ga lalli na ba ne, ko ka ce ya yi kyau? Sannan na yi gyaran jiki kowa ya ganni sai ya yaba amman ban da kai."
Kai tsaye ya ce"Kin nuna min ne?
Baki ta buÉ—e kamar ya na kallonta kafin tace"Au ba ka gani ba,?
Kai tsayen ya sake cewa" Ni ban gani ba."
Sai Mimi ta kasa mgana ganin zai yi wasa da hankalinta cikin raÉ—a ta ce" In dai ko ba ka gani ba, ko dai ko dai.?
"Ko dai mene ne?
Sai ta kasa mgana ta koma tana dariya ya fahimci maganarta bai san lokacin da ya yi sariya mai sauti ba, kafin ya ce "Yaro yaro ne. Yaro man kaza, Uhmm"
Haka kawai yace bai ƙara yi mata wani mgana ba suka cigaba da hiransu ita ba ta san yadda yake iya surving ɗin rayuwarsa in har ya zo su ka haɗu ba, ko muryanta wanka ta ke saka shi in ko ya je ya ganta in ya dawo sai  y yi wanka dauriya yake yi ba ya so ya wuce gona da iri, kuma shi yana da kiyayewa ba ya son ya watsar da darajan auransa a kan titi shi ya sa ba ya rawan kafa wajen taɓa jikinta shi ya sa take tunanin ko ba shi da lafiya ne? Lalle ko zai nuna mata kwanjinsa da lafiyansa ƙila har sai ta fara cewa ita ta gaji.

  Kamar yadda ya faɗa washegari ma'aikata suka karisa fenti, sannan a daran masu sauka suka fara, wani malami ne mai almajirai shi ya wakilta babban Almajiransa da yara goma suka kwana a gidan suka kuma sauke Qur'ani zuwa wayewar gari tare da sauran addu'o'i, zuwa safe kuma a ka sallame su da abun sadaka.Mansoor ya yi mgana da Inna kan gyaran gidan tunda an gama aiki sai Inna Meri ta kira ƴan'uwansa mata su Yaya Amina daman Hibba tana nab  ba su koma ba,Mu'azzam hutun sallarsa na Sati uuɗu ne sai bayan tarewar Mimi za su koma, su suka hadu har da Walida da Mariya da matar Auwalu da ya ce itama ta je ta kama musu suka je gidan suka share suka goge amman fa kowa ya san wannan gidan ya kai makura wajen haɗuwa,  har yamma suna can sai gabda mangariba suka gama gyarawa suka koma gida suna zuzuta ma Inna kyan gidan da tsaruwarsa.
Chapter 52 · 0% Book details