Sashe 31
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
  Baba Ɗanjuma cikin mamaki yake kallon Magajiya da wani irin bacin rai a fuskarsa da cikin zuciyarsa abib da ya faru yau ya sa ya kasa mgana, Allah ya sa ya iya gyaran targaɗe ko karaya shi ya samu ya ja ma Inna Meri hannunta, abin da ya ba shi tsoro shi ne ganin hawaye a idanuwan Inna daganan sao jikinsa ya ƙara yin sanyi ya rasa matakin da zai ɗauka tunda ga ita makiran sai kuka take yi tana dafe cikinta a cewarta a ciki Walida ta dake ta. Yau hatta su Baba Sani sun kasa yin wani sharhi kamar yaadda suka saba har Baba Ɗanlami yau dai sau ɗaya ya ce Magajiya ta yi shuru Saddiqun ya dawo a je asibitin a gani Allah ya sa ba wata nabbar matsala ba ne.
 Za ta ƙara mgana Baba Ɗanjuma ya daka mata tsawa ya ce ta yi ma mutane shuru ana cikin haka sai ga Mariya ta shigo tare da Yaya Zuwaira kusan lokaci ɗaya da Auwalu, Dalilin da ya sa a kasan Mansoor ashe tun ɗazu yana tsaye daga bayansu, ba su yake jira ba wanda ya ke son gani bai shigo ba so ya ke yi ya fara cin ubansa tukunna sannan ya ɗauka dai ya ci darajan mai daraja wlh da sai ya saka an kulle shi na tsawon wata ɗaya sakamakon abin dda ya aikata.
 Baba Ɗanjuma da ya gansa sai da ya ji Kunya, kansa ya sunkuyar kasa ma ya kasa mgana Zuwaira da Mariya suka nufi magajiya suna taya ta rike Aisha da take kara narkewa kamar ranta zai fita , ita ko Magajiya faɗi kawai ta ke yi ina Saddiqun ne shima ya je ya yi zaman shi, Bintu kuma wajen walida ta nufa ta duka tana lallashinta Harira kuma ta ƙarisa kusa da Inma ta riƙo ta tana faɗin" Ki tashi daga kasan nan Innar Mu'azzam, ki koma cikin ɗaki."
Amman Inna ta kasa tashi. Hawaye take yi amman tana saka hannunta guda ɗaya ta na gogewa, Mansoor ji ya yi kamar ya mutu saboda Baƙin cikin dake cin ransa Inna suka saka kuka lalle nema. Shi fa kafin ya fara aiwatar da komai sai ya fara cin uban Saddiqu wlh, Auwalu ma lamarin bai yi mishi daɗi ba haka ya duka yana ba ma Inna da Walida haƙuri, Baba Sani ya juya ya na kallon Mansoor dake tsaye har lokacin hannunsa goye a bayansa yana cije leɓensa na ƙasa Ya ce"Kai kuma tsayuwar me kake yi, ka zo ka lallashi ita Merin ta koma ɗaki lamarin bai yi daɗi ba sai hakuri."
"Akwai wanda na ke jira ne."
 Amsar da Mansor ya bashi kenan a kausashe kafin kuma ya kalli Walida kukan ta ma ɓata masa rai ya ke tsawa ya daka mata kafin ya ce"Ki yi min shuru anan wajen," haka ya faɗa yana kokarin saisaita fushinsa a lokacin ji yake yi kamar ya mutu sai wajen ya yi shuru har mai kukan ƙaryan ta natsu Bintu ya kallah daga baya yana faɗin"Bintu kama Inna ku koma ɗaki."
Yana gama faÉ—in haka dai dai da shigowar Saddiqu da sauri yana faÉ—in" Magajiya ki kamota ga mai adaidaitan na samo."
Gadan gadan kawai ya nufo bangaren shi kuma Mansoor daman shi yake jira Kawai sai suka haɗe. Ya saka hannu ya ture Saddiqu sai da ya kusa faɗuwa kasa ya dago cikin mamaki domin ya ga waye ya yi masa haka kawai Mansoor ya daddage iya karfinsa ya tsinke Saddiqu da lafiyayyan marin da sai da ya ga hasken taurari, bai gama dawowa hayyacinsa ba ya ƙara masa wani, da sai da ya faɗi kasa ya bi shi ya saka hannu ya damƙo ƙwalan rigan shi ya ɗago shi sannan ya ƙara masa wani marin mai shiga jiki sannan lokaci ɗaya ya ture shi da ƙarfin da sai da ya faɗi kasa. Kowa sai ya buɗe baki yana kallon ikon Allah Baba Ɗanjuma kuwa saboda jin daɗi da karfi ya ce"Na gode maka mansoor, kayi masa dukan tsiya."
  Harira ma ta ji daɗin hukuncin Gaje dai ba wanda ya gane yanayin ta, Baba Sani da Baba Danlami sai faman subhanallahi suke faɗi kawai domin Saddiqu ya maru lokaci ɗaya har shacin hannu ya bayyana a dama da haunin fuskarsa sannan jini na bin hancinsa kenan haɓo ya yi. Zuwaira ta kira sunan Mansoor cikin tsawa tana faɗin kada ya kara taɓa mata kaninta Auwalu na gefe ya ce"Wlh ya yi min dai dai gwara ya kara masa tunda ba shi da mutumci."
Bintu ko kamar an sakata a Ajannah har Walida mai kuka ta ji daɗi, yau kam Inna na zaune amman ba ta hana ba. Lalle tura ta kai vango magajiya kuma tsaabar ruɗewa ba ta san ma ta saki mai ciki ba tana mamakin wai Agola ne ya kama ɗanta da duka ita kuma Maeesha ba ta san ma ta tsaya da kafafunta ba jikinta ba inda bai rawa ganin Mijin nata da take taƙama da shi a gabanta ya maru, to ita fa? Tuni ta manta da an dake ta a ciki ta mike ga jikinta tana wani fiƙi fiƙi da idanuwa.
 Saddiqu kuma cikin ɓorin kunya ya lakato jinin dake saman hancinsa ya gani. Sai kawai ya taso yana faɗun" Ni ka mara. Wallahi sai na rama." Ya nufi Mansoor gadan gadan sai Auwalu ya riƙe shi amman yana fizge fizge kamar zai iya wani abun, Mansoor ya kalle shi cikin fushi kafin ya nuna shi da yatsa lokaci ɗaya yana faɗin" Mari na farko na Junior ne, mari na biyu na Walida ne mari na uku saboda Inna ne. Kai har ka isa uwar tamu kake son ka kashe mana?. Wallahi ka ci darajan Baba da yau sai ka raina kanka banza kawai sakarai wanda ba namiji ba."
Ya gama faÉ—a lokaci É—aya har yana hambari sa shi da kafafunsa shi kuma Saddiqu tana hakilon nanza.
  Juyawa mansoor ya yi ya isa ga Inna ya saka hannu ya ta da ta tsaye lokaci ɗaya yana faɗin" Ki yi hakuri Inna komai yau ya zo karshe." Bintu ya kallah kafin ya ce"Ɗauko ma Inna hijabi ta saka, ke ma ki shirya Walida ta ɗauko mayafinta mu je mota ki riko hannun Junior."
Ya faɗa Lokaci ɗaya yana rumgume Inna ta gefren kafaɗanshi da sauri ko Bintu ta shiga ɗaki ta ɗauko masa hijabin Inna ya taimaka ya saka mata, Inna hawayenta sun ƙi tsayawa abin da ya faru yau ya ba ta tsoro matuka da mamaki. Walida ma ta sako hijabinta ita da Bintu, Inna Mero kuma Mansoor ya saka mata takalmi da kansa sannan ya Juya yana kallon Baba lokaci ɗaya yana faɗin" Baba ka yi hakuri amman Inna ba za ta cigaba da zama a gidan nan ba tunda har oamarin ya kai ga duka bamu san abib da zai faru a gaba ba kuma, kada ka ji a ranka kamar ka gaza kawai dai ba zan iya hakurin na barta ba ne gwara ta bar gidan sai waɗanda basu san zamanta a gidan su haɗa da ɗakinta suyi ta zama zauna."
Baba ÆŠanjuma ya jinjina kai kafin ya ce"Bakomai Mansoor, nima a yau ina goyan bayan ka, Mahaifiyarka ce kana da Ikon kare martabanta tunda ni na kasa, ku je duk inda ta koma ni a matsayina na mijinta zan bita ko'ina ne."
 Sai a lokacin Magajiya ta samu bakin mgana sai ga ta, ta yi wani tsalle ta sha gaban Mansoor da Inna Meri lokaci ɗaya tana faɗin"Ina za ka?. Wallahi baka isa ka dokar min ɗa kuma ka juya ka yi tafiyarka kamar ba abin da ya faru ba. Ba ka isa ba domin ban taɓa ganin inda Agola ya daki ɗan ma su gida ba, Ko ka ɗauke ta daga baya kenan bayan kun gama zama kun gama more komai, nan gidan dai shi ya yi muku komai dangin uban naka me suka tsinana maka? tunda ka shigo rayuwarmu kai da mahaifiyarka kuka rugumin gidana a da ina zaune da gani sai ƴa'yana da mijina amman zuwan wannan matan da zuwan wannan Agolan gidan nan komai ya sauya. Yanzu Danjuma ya fi fifita Agola sama da ƴayansa, in ba lalacewa ba a gaban idon ka a ɗaki ɗanka amman ka kasa mgana sai ma munawa da ka yi abin da aka yi dai dai ne to ni wallahi ban yarda ba sai an bi ma ɗana haƙƙinsa"