← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 93

Sashe 9

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Shima kuka ta saka masa tana faɗin ita ba za ta koma ba. Saboda ai shi Ajin ya san tafiyarta kuma da kanshi ya ce ta tafin, kuma har yanzu bai zo kuma bai kirata ba kenan shima ya gaji da auran nata.  Jin haka yasa bakin Dr  ya mutu amman shima ya ce a cikin ranakun weekend in ya samu lokaci zai zo Gomben.
Shima ya kira Daddy sun yi mgana  ya ɗan dai yi masa bayanin Mimi za ta koma matuƙar Mijinta ya zo biko a ka zauna a ka ji inda suke da ɓaraka a yi gyara amman matukar bai tako ba shi ba zai maida masa Mimi ba tunda ba ƴar sadaka ba ce. Ta nan kuma Dr ya ga gaskiyan Daddy ko ya ya ne a nuna masa Mimin tana da daraja, amman matarka ta biyo dare ta dawo gida amman baka kira ba, sannan ba ka zo ba, sannan ba ma tunanin ko wani abu ya faru da ita bayan fitar ta ba, shima ta wannan bangaren ya ga wawancin mijin na Mimi a haka kuma a fuska kamar mai hankali da Tunani.

  Ita Hajiya sai fakewa take yi da ƙannensa suna kiran ta wayarta ba ta ɗauka Daddy ya ce ƙannensa dabam shi dabam, ba ƙannensa ke auranta ba shi ya ke auranta kenen bai ma san darajanta ba kenan.
Kan kuma maganar kwaso kaya ne domin Maman ta zo a daran ta ce gobe da safe za su je tare da Turai su kwaso kata kayanta da umarnin babanta.
Hajiya ba haka ta so ba, ta so a dakata ba ta san vaggawa amman Daddy ya ce sai an kwaso saboda shi kaÉ—ai ya bar ma kansa Sanin dalilin shi na cewa a kwaso kayan da gaggawa.

  Washegari misalin ƙarfe 10:20am na safiya ranar jumma'a Mama ta isa gidan Wanzamai, ita ta fara yo gaba Hajiya Turai za ta zo da mai motan ɗaukan kaya, Inna Meri na ayyukanta a tsakar gida Mama ta shigo ta gane ta sai ta karɓe ta hannu bibbiyu ta shigarta da ita har cikin ɗakinta ta saka Walida ta kawo mata ruwa, Inna Meri kunya duk ya kamata a tunanin ta ko Maman ba ta san Mimi ta koma gida ba ne, Tana shirin ce mata ai Bintar na gidan Hajiya sai kawai ta ji Mama tana faɗin" Key ɗin ɗakin Mimi nake so don Allah."
Sai Inna Meri ta kasa magana saboda jikinta ya yi sanyi amman sai ta yi yaƙe kawai ta tashi sda kanta ta shiga ciki ta ɗauko daman ita da kanta ta rufe ɗakin ta riƙe key ɗin a hannunta. saboda jatsari ne barin ɗakin a buɗe tunda akwai kayan kudi a ciki.

  Ba tare da ta tambayi ba'asin abin da Mama za ta yi a ɗakin ba ta damka mata makullayen ɗakunan, Ita kuma har ta amsa ta fita daga ɗakin ba ta ƙara cewa komai ba, Ta buɗe dakin ta shiga ciki Inna Meri ba ta taba tunanin za'a kwashe kayan Binta ba ne duk daman ko yau sai da Magajiya ta zo Kofar ɗakin ta ta tsaya ta na faɗin suna bukatar ɗaki domin Matar Saddiqu za ta dawo nan ne cikin gaggawa.
Walida ta same Inna zqune kawai ta yi tagumi, Hibba ta je gidansu Jiya ba ta dawo ba sai ta kwana a can, Junior kuma ya ƙi zaman nan sai gidan Bintu saboda su Husaini.

  "Inna ko dai an zo ɗaukan kayan sawan Anty Mimi ne?

  Walida ta faɗa tana zama kusa da Inna Meri, ita kuma sai ta girgiza kanta kafin ta ce"Ban sani ba, makullin ɗakin kawai ta tambaya."
Ita kanta Walida duk jikinta ya yi sanyi, Uban gayyar kuma tun ranar da suka zo da Nasir ba wanda ya ƙara ganin shi Baba Ɗanjuma har ya yi tunanin su je gidan Sanata Hamza shi da abokinsa Mallam Hashimu su ba da hakuri Inna ta hana ta ce shi wai mai auren bai damu ba sai su ne za su damu kansu? Ai abin da ya nuna ya nuna ma duniya shima hakan ya zaɓa. Cewa ma ta yi in dai ya je ita ba da yawunta ba, Shi ya sa sai ya dakata shi kuma gogan in an neme sa sai ya ce kar kowa ya saka baki yana tutiniyan duk in da Ma Mimin ta je a cewarsa za ta dawo ne ma. Har su Yaya Amina sun so su  zuwa har gidan Hajiya su Samu Mimi su ba ta haƙuri Inna Meri na ji ta ce kar wacce ta taka ta je, ba hurumin su ba ne.

  Su dai suna zaune sai gani suka yi wata mata ta shigo Hajiya Turai, Mama ita ta leƙo ɗakin Inna ta ce a gaya ma matan gidan Maza za su shigo su fita da kaya shike nan ta faru ta kare. Daman Zuwan Mama kayan Sawan Mimi ta gama haɗa mata duka a cikin akwatinta da duka kayan kwalliyarta da takalmanta, Inna ko iya fita ba ta yi sai Walida ne ta je ta gayama magajiya Maza za su shigo ɗaukan kaya. Tana jin haka ta san Dalili a ranta ta ce abin dai ya tabbata kenan Daman itama duk ita da gayama yaƴanta har Maaeesha dake gidan Zuwaira ta je ta kai mata labari sai ta ji daɗi ko banza za ta zama tauraruwa a wannan gidan.
Kuma ta ji daÉ—i da za ta koma É—akin Mimi Saboda ya fi jin kayan gyara sannan ya fi kyau komai na fantin É—akin da abubuwa Uniqui ne masu tsada da yarari.

Walida hankalinta ya ta shi ganin da gaske fa tunda ana ta fita kaya. Sai ta Lallaɓa ta saci wayar Inna Meri ta Kira Bintu ta sanar da ita abunda ke faruwa sai ta ce ga ta nan zuwa ta kuma ƙara kiran Hibba ita sai ta ce ta na kan hanya tunda sun yi waya da Mu'aazzanm tun asuba ya ce ya ta so.
Da Bintu da Hibba a kofar gida suka haɗu suka shigo gidan lokacin har gqdon Mimi an kwance an fita da shi Kujeru ne su kaƙi fita a na tunanin a haura da su ta garu kamar yadda dama suka shigo gidan tun farko.

  Ɗakin Inna suka faɗa cikin wani yanayi Bintu ke faɗin" Inna ke kika ce su zo su kwashe kaya? Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba sai Walida ne ta maida musu abin da ya faru, Bintu ta ɗauko wayarta daga aljihun rigarta ta lalubo lambar Yayan na su ta kira shi amman wayarsa tana kashe ne so take yi ta sanar da shi abin da ke faruwa ƙila in ya ji ya zo ya dakatar da su.
Hibba faÉ—i take yi" Inna domin Allah ki dakatar da su mana.".
Inna Meri ta miƙe tana faɗin" Saboda wani Dalili Hibbatu? Ba ni da wannan hujjar."
saboda ma kar su dameta fita ta yi ta zuba ruwa a buta ta zagaya ta kama ruwa tana fitowa ta É—auro alwala ta zo ta shige ciki ta shimfiÉ—a sallaya ta kabbarta salla.
Ganin ba mafita ya sa Bintu ta ja hannun Hibba suka fita lokaci É—aya tana faÉ—in" Mu je mu yi musu mgana. Wlh makiyan gidan nan dariya suke yi mana."
Sun shiga É—akin sun iske Mama da Turai suna maida wasu kayan Kitchen É—in a cikin kwalayensu bayan sun gaishe su sai kuma suka kasa mgana har sai da Mama ta ce"Lafiya ko?
Bintu ta marairace kafin ta ce"Don Allah Mama ku yi hakuri da kwashe kayan nan, shi fa Yaya Mansoor bai ce ya saki Anty Mimi ba." Mama ta yi yar dariya tana kallon ƙanwarta Kafin ta ce" N ma yar aikace, umarnin Babanta ne ya ce Lalle lalle yau mu zo mu kwaso mata kayanta."
Turai ta ce"To tunda har ya ce ba ya sonta zaman me za ta yi da shi?
Mama ta ce" Babu kam, abin da yake so ne ta yi masa tunda ta ce za ta tafin ya ce gwara ta tafin."

  Da sauri Hibba ta ce"Sharrin sheɗan ne, sannan faɗan ma'aurata ne, in da an ɗan dakata za su iya sulhunta kansu."
Mama ta sake yin yar dariya kafin ta ce" To wannan kuma ban sani ba, amman ni dai yanzu Umarnin Babanta na ke aiwatarwa."
Duk iya ƙokarinsu amman su Mama ba su saurare shi ba. Daga karshe ma suna mgana sai suka yi musu kunnen uwar shegu.
Dole su ka fita jiki duk a sanyaye sannan sun koma suna ta kiran Mimi ba su sameta ba, abin da suka lura shi ne kamar ta rufe su ne ba za su ƙara samun ta a waya ba.
Suna ji suna gani aka kwashe kayan Mimi gabaÉ—aya tas kayan abinci kaÉ—ai suka bar musu a kitchen da za su tafi suka ba su makullin É—akin ba su ko ga Inna Meri ba ta na cikin dakinta.

  Makota ko sun cika ƙofar gida ana maida mgana, wanda ma bai sani ba duk ya san abin da ke faruwa Magajiya na tsakar gidan tana dariyan zuci burinta ya cika.
Mariya ba ta cika zama a nan ba ita ce gidan Zuwaira ko gidan Auwalu, Saboda anan ba za ta sake ta riƙa yin taɗe taɗe yadda ta ga dama ba sannan magajiya na takura mata kuma ba sa shiri da matar Saddiqu.
Sai ga ɗakin da Mimi ta yi rayuwa fayau ba komai a ciki haka su Hibba suka koma ɗakin inna suka yi jugum jugun abin haushi ma ba'a ɗade ba sai ga Saddiqu ya shigo Shashen shi da wani abokinsa ba sallama ba komai suka shige ɗakin suna dubawa baƙin ciki ya sa sai Bintu da ta yi kwallah ta ce ma Hibba bari ta je ta dawo ta fice daga gidan gabaɗaya tana jin magajiya na shewa ita da Gaje daman ai murna za su yi.
Daga nan Binta mashin ta hau zuwa gidan Yaya Amina domin ta sanar da ita halin da ake ciki ya kamata su san matakin da za su ɗauka kafin su zama abun dariya a cikin gida da maƙota.

******
Chapter 9 · 0% Book details