← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 93

Sashe 86

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan gaisuwan da tambayar yadda take ita da Ummi su ka É—an yi zantukan soyayyarsu na kewar da su ka yi da juna. Sannan Mimi ta shigar masa da maganar Manaja nan ta ke Aji ya fara faÉ—a ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba,Mimi ta jawo Ummi da ke barci ta rumgumeta a sanyaye ta ce" Kayi hakuri Baban Ummi."
Haka kawai ta ke faɗa amman ya ma ƙi sauraranta sai faman faɗa yake yi yana faɗin" Ba fa mganar hakuri ba ne Fatima renin wayan ne na ga ya yi yawa. Me ya sa sai ke? Ke kaɗai ce ma'ikaciya mace a wannan wajen na ku? Haba sai ace ke dole fuskarki ce za ta riƙa yawo a akwatin Talabijin ɗin kowani gida? Haba ba ta yuyuwa kina matata ina son ki, in na kalle ki kina burgeki sha'awan ki na kamani, amman ace abun hauahi da baƙin ciki ni a matsayina na wanda Ubangiji ya yarje min ba ni da ikon kallon ki ni kaɗai na yaba, da wanda ya dace da wanda bai dace ba, kowa kallon fuskarki yake yi ya na yabawa. Wallahi Tallahi ko aikin nan da kika ga na barki kina yi ba a son raina ba ne Fatima , ina da kishi kishin da ni kaɗai na ke son na yi ta kallon ki ina yabawa. Amman ya zan yi? Yanzu ina hanaki wannan aiki sai ace ni mugu ne ba ni da adalci na ganki da aikin ki na aure ki kuma na rabaki da shi Ƴan'uwanki su zageni ke ma a ranki ko ba ki furta ba sai kin ce ni mugu ne ba ni da adalci."

Cikin Mamakin kalamansa Mimi ta ce"Ni? Me ya sa zan kira mijina da suna mugu? Ka isa ne shi ya sa ka hanani saboda kai É—in mijina ne kuma shugabana, yan'uwana kuma ba su da abun cewa tunda ba suke aure na ba, na su sai dai shawara ne ko jin ta baki"
Aji ya ciji leben bakinsa na ƙasa kafin yacce"Ina son na hanaki, amman kuma gwara na yi miki adalci kema ki yi min,in na dawo za mu sake yin mgana"
Ta san cewa akwai mgana tunda ya ce sai ya dawo za su ƙarisa mgana, tun kafin ma ya ce bai amince ba mganganunsa sun nuna in da ya dosa yasa ta faɗa mana Manaja Megidanta bai amince ba sannan ta ba da Shawaran tun da a shekaran a ɗauki sabbin ma'aikata me zai hana su jaraba wata sabuwar fuska! Nan da nan ko a ka karɓi shawaranta a ka fara shirye shiryen kaddamar da shirn tare da zaɓo cikin sabbin ma'aikatan da a ka ɗauka domin cire wacce ta fi chanchanta a ciki.

Ko da suka yi waya da Rukky ta yi mata zencen itama sai da ta ce"Ke ma Mimi da son jan ma kanki faɗa kike yi, wannan mijin naki mai shigen kishi ne zai amince? Aikin ma ai ba ason ranshi kike yi ba, da kin sani tun da Manaja ya tuntuɓeki kin datse abun da ba ta kawo ku da gabar haka ba."
Mimi ta ce"Haka ne Rukky, ai na ce su nemi wata sabuwar fuskar mijina bai amince ba."
Ruƙayya tace shike nan kuwa sai ki zauna lafiya.

Saboda maganar na ranshi sati biyu tsakani ya dawo gida, amman sai da ya zaunar da ita yana gaya mata ba dole sai an riƙa ganin fuskarta ba akwai ma'aikata da dama da suke aiki ta bayan fage fa ba'a son su ba, me zai hana itama a maida ta wannan bangaren? Mimi ta ce"Ba ni da zaɓin bangaren da zan yi aiki, zaɓi na kenan bangaren da na fi ƙwarewa broadcating, Kuma ni ban isa in ce ga in da za su ijiyeni ba sai dai in zan ijiye aikin gabaɗaya na dawo gida na zauna tunda haka kake so."
Jin haka yasa bai ƙara mgana ba tunda ya ga idanuwanta sun ciko, ya san tana son aikinta kuma yanzu ya ce ta bari kamar bai yi mata adalci ba, ita ba wata sana'a take yi ba sannan shi kuma ba mazaunin gari ba sannan In har Inna ta ji labari sai ya raina kanshi shiyasa ya danne ma zuciyarsa bai ƙara mgana kan aikinta ba har ya gama kwanakin shi ya koma Abuja.

Ya koma ba Daɗewa Mimi ta samu wayar Mommy ta ce tana neman ta a Abuja, a she ba ita kaɗai ba gabaɗaya yayan nata har da Dr tunda shi ne babba, kiran ya ba su mamaki amman su a tunanun ko maganar gidane, kuma dukkansu ta ƙi ce musu komai a waya ta dai ce su nemi izini wajen mazajensu weekend ɗin da zai shiga tana son ganin su gabaɗaya, Aji ma da ta gaya masa sai da ya ce" Topha! Allah ya sa lafiya."
Mimi ta ce"Ina tunanin ba lafiya, dukkan mu fa ta kira har Dr, ni ba ka ce min ka je wancan satin ba? Ko ka fahinci wani abu ne? Aji ya ce"A'a lafiya lau take ba wata matsala, mun daÉ—e muna hira da ita, ba na jin ko akwai wani abu na damuwa sai dai in wata mganar ce ta dabam, ki kwantar da hankali hairan in sha Allahu."
Da haka ya samu ta natsu amman ita duk ta damu, Abun da ya ƙara ba ta mamaki da ta je gida gaida Hajiya nan ta ke gaya mata ta saka Daddy ya nema musu jirgi gaɓadayansu har da shi za su tafi Murja na neman su. Sai Mimi ta saka a ranta ƙila kan mganar gida ne tunda ba'a raba gidan ba har yansu su sun ce sun barshi Mommy ta zauna har karshen rayuwanrta ne.

Daga gidan Hajiya gidan Inna ta biya ta na gaya mata za su tafi Abuja tare da Hajiya da Daddy, Inna ma kanta sai da ta ce"Lafiya kuwa? Ko wani abun ne ya faru?
Mimi ta ce"Lafiya ƙalau Inna za mu je dai mu gaishe ta ne."
Haka ta faÉ—a ma Inna, saboda itama ba ta san dalilin kiran ba.
Nan ta kai har mangariba saboda Aji baya nan ya sa ta koma da wuri kuma a motar ta ta zo, washegari kafin ta je aiki sai da ta kai Ummi asibiti ta kwana kuka ashe kunnenta ke ciwo a ka bata mgani. Daga asibitin ne ta wuce wajen aiki amman ba ta daɗe ba ta koma gida saboda Ummi, amman Alhamdulillah mganin da a ka bata ta ɗiga mata sau uku shike nan ta samu sauƙi ta cigaba da walwalanta irin na su na yara.

Tun ranar Jumma'a Khadi da Madiha suna Abuja, su Mimi kuma jirgin safe suka bi, wajen sha ɗaya suna falon gidansu a Abuja, abun da ya ƙara ninka mamakinsu ganin har da Inna zainaba suka iske a gidan kenan mganar babba ce, a yinin dai ba'a yi wata nagana ba an haɗu ana ta hira kowa sai mamakin kiɓan Ummi yake yi khadi ta dauketa ta na nishi lokaci ɗaya tana faɗin"Ka ga min burtuka, ke ubanki ɗan firit uwar taki kuma ba kiɓa ba, to ina kika ɗauko wannan jikin?
Hajiya na dariya ta ce"Ƙibar yara ce, taba fara girma za ta ragu, sannan ita kanta Binta haka Murja ta yo goyonta sai da ta fara girma sannan ta fara raguwa."
Mommy na wajen ta ce kwarai haka ta yo goyon Mimi da wannan kibar kamar kazar turawa jiki suɓu suɓu kamar Ummi, Dr ya ce to ga in da ta yi gado nan wajen uwarta ana ta dariya har Madiha ta na saka baki ta ce Yarinyar na burgeta ta na son ganin yaro da kibarsa sannan da ƙarsashinsa har ɗaukanta ta yi, Allah ya haɗa jininta da na Ummi duk ba ta damu da ɗaukan yara ba, nata ma a hannun masu aiki suka yi wayau

Har dare Mommy ba ta ce musu komai ba, Sun dai ga sun shige ciki ita da Daddy da Hajiya sun jima suna mgana sannan ya fito, shi a ranar ya koma daman ba kwana ya ce zai yi ba. Hankalinsu ya kwanta ganin Mommy lafiyanta ƙalau ta na ta zirga zirganta suna da tabbacin ba ita ce wani abu ya same ta ba. Har Asma'u sun ma mgana ta ce itama ba ta sani ba, sannan sun yi ma Inna Zainaba mgana ta kalli Khadi da ita ce ta tsarete da tambayan abunda ya sa Mommy tace ta na son ganinsu."
Inna Zainaba ta ce"Ban sani ba,ko jira ita uwar taku ai tunda ta kira ku za ku ji abin da ke faruwa." Sai suka yi shuru ba su kara mgana ba ko Dr da yake namiji bai damu ba. Harkan gabansa kawai yake yi sai su ne duk suka damu barin ma Khadi da Madiha.
Madiha ba ta hakura bq sai da ta je har É—akin Mommy a daran ta ga ta na waya amman ta na ganinta sai ta ce"Zan kira, yanzu zan yi mgana da yaran nawa."
Daga nan ta juya tana kallon Madiha cikin Mirmishi kafin ta ce" Madiha Kabir Dabo,."
Haka ta kira sunanta sai itama ta yi mirmishi kafin ta ce" Barrister me ke faruwa ne? Kin kiramu kuma kin ƙi ce mana komai? Kin san gobe zan koma ga Dr ma ya na da Tiyata jibi ya ce."
Sai Mommy ta dafa kafaÉ—anta kafin ta ce"Ina sane da abin da nake yi, mu je É—akin da Hajiya ta sauka sai mu yi mganar gabaÉ—aya.
Chapter 86 · 0% Book details