Sashe 6
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Hankalin Aji sai ya fara tashi da sauri ya ce"Saki? wa aka saka kuma?
Ya faÉ—a yana kallon fuskokinsu, Baba ÆŠanlami da Baba Sani suka kalli juna kafin Su haÉ—a baki wajen faÉ—in" Toh ba ka son a sani ne? To ai Meri ce da safenan ta ce ka rabu da matarka tana ma gidansu tun jiya."
Aji ya zaro ido lokaci É—aya yana jin wani abu kamar zafi zafi na ratsa sassan jikinsa cikin mamaki ya ce"Mun rabu? tana gidansu?
Sai kawai ya juya ya shiga gidan da sauri kamar zai kifa Nasir ya bi bayan shi. Domin in ya fahimta Mimi dai tun a jiya nan ta koma gidansu.
 A tsakar gida suka ci karo da Magajiya tana Aikinta tana wake waƙenta cikin gara'a, abin da ya ba ta mamaki ganin yadda Mansoor ya wuce kamar zai ta shi sama, Duk da ba kasafai take amsa irin gaisuwar sa ba, ta san bai taɓa shigowa gidan nan ya ganta zaune bai mata irin ta shi gaisuwan ba ko da ba za ta amsa ba, amman sai ta ga yau ya wuce fuu kamar Iska sai Nasir ne ya bari da gaisheta ta amsa a ranta tana tunanin me ke faruwa?
Wata zuciyar ta ce"Me ko ya faru, abin da ya faru da safe ne uwar ta kira duka Æ´aÆ´anta ta sanar da su, sun zo sun cika gida, yau ko sai dai a yi fito na fito."
Tuna haka yasa ta ja tsaki kawai ta cigaba da aikinta.
 Ɗakin Inna cike da ƴayanta da jikokinta suna ta faman maida yadda aka yi tun bayan zuwan su Yaya Amiman, Inna Meri alwala ta yi ta koma cikin ɗakinta kawai ta zauna ta rasa mafita. Domin ta gama yarda Baban Inna baya son farincikinta sannan Babban Burinsa ya ga ya ɓata mata rai ya saka ta a cikin wani hali, ina amfani wannan jin kunyar da ya jawo mata, kamar daga sama ta ji muryaansa a cikin falonta cikin kaushi yana faɗin" Ina Mimin take?
Sai falon ya yi tsit, kowa na kallon kowa ciki mamakin ganinsa ba su Bintu ba hatta su Yaya Amina sun kasa mgana domin suna ganin yanayinsa a fusace yake.
 Kawai sai ya fita har yana bangaje Nasir ɗakinta yana buɗe ne sai dai an sakaya ne shiga cikin ɗakin ya yi yana kiran sunanta amman shuru shi ne har bedroom ɗinta har toilet ya leƙa ba kowa ya duba kayanta na cikin wardrope ya ga ba'a taɓa komai ba.
Sai hankalinsa ya É—an kwanta da sauri ya fito daga É—akin ya sake dawowa É—akin Inna sai ya iske Nasir na durkushe suna gaisawa da Inna.
"Inna me ya sa kika bari Mimi ta tafi?
 Ji wata tambayar renin wayau haka Hibba da Bintu suka ce acikin ransu, Inna kuma baƙin ciki ya sa ta kasa mgana kawai miƙewa ta yi ta shige ciki ta bar shi nan tsaye jiki a sanyaye, Yaya Amina ce ta yi gyaran murya kafin ta ce"Tun jiya Mimi ta tafi gida nima ina faɗan me ya sa suka barta ta tafi? Shi ne suka ce min Inna ta ce tafi,sannan sun yi sun yi su hana ta tafiya ta ce sai ta tafi."
"Is ok! duk in da ta je ma ai za ta dawo, Nasir ta shi mu je."
 Haka kawai ya faɗa cikin bacin rai sannan ya bar ɗakin sai ma ya fice daga gidan gabaɗaya. Nasir mamaki ya kama shi Aji yaushe zai yi laushi ne ya gane Annabi ya faƙu? A mota ya same shi yana cika yana batsewa sai da ya shiga motar ya rufe kawai sai ya ga Aji ya ja motarsa sun bar kofar gidan.
Cikin mamaki ya juya yana kallonsa kafin ya ce" Ya haka? mu da muka zo ban haƙuri?
Kamar ba zai yi magana ba, hankalinsa na wajen tuki sai can ya ce"Inna ta yi fushi ba za ta sauraremu ba yanzu. Sai bayan kwana Biyu in ta huce."
"Ita Mimin fa? Ba za mu je can gidan Hajiyar mu ba ta hakuri ba?
Kallonsa Aji ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Itama ka ƙyaleta, duk in da ta je ai za ta dawo tunda da aurena a kanta."
Nasir ya ce"Ina mganar da ka ce ta ce tana jiran takardanta in kaƙi, za ta kai ka Kotu.".
Cikin mirmishi Aji ya ce"Kai ka yarda za ta iya kai ni kotun? To ta kaini kotun sai a ga ni shege ka fasa."
 Nasir mamaki ne ma ya hana shi magana har Aji ya maida shi gida. Shi dai har cewa ya yi ya kira ta a waya.Aji ya ce ko ya kirata ta hau dokin zuciya ba za ta ɗauka ba shi kuma ba ya son ya kira ba'a ɗauka ba in ransa ya ɓaci abun ba zai yi mata daɗi ba.
Yana ijiye Nasir a gidansa ya juya kan mota ya koma gidansa. Sai da ya yi wanka ya sauya kaya sannan ya kunna wayarsa ya kira Mu'azzam. Shima dai duk mgana É—aya ne bai kyauta ba Inna ta ce ta cire hannunta a kan shi, shi na Innar ya fi damun shi sai kawai ya ce"Mu'azzam kar ka damu kanka, ba sai ka taho ba komai zai dai dai ta in sha Allahu."
Mu'azzam ya ce"Ta ya ya? Inna ta rantse da Allah ta baza ta saka baki ba. Na yi ta kuma Kiran wayar Mimi ba ta É—auka ba, mun yi mgana da Baba zan shigo jibi sai mu dumguma mu je mu same ta mu ba ta hakuri."
 Kai Tsaye ya ce"Ni ban aike ku ba, kowa ya cire bakinsa a mgana ta da Mimi, ba kuma wanda zai je ba ta haƙuri."
Daga can bangaren haka Mu'azzam ya saki baki ya kasa mgana.
"Ka da ka ce za ka bar aikinka ka taho, na gaya maka ka yi zaman ka, matar ka kuma za'a turo maka ita gobe, Inna na cikin damuwa ku yi min alfarman barin mata Junoir awajenta tunda an yaye shi."
Mu'azzam kasa mgana ya yi sai da ya ji ya ƙara faɗin" Is an oder Mu'azzam."
Shike nan kawai ya ce ya kashe wayarsa.
Baba da ya kira shi daga baya abin da ya faɗamai kenan kar ma wanda ya yi yunanin zuwa wajen Mimi su bar shi da ita, shi a tunanin shi Mimi ba za ta iya dogon Fushi da shi ba za ta dawo Saboda tana son shi sannan yana tunanin in aka bita kanta zai yi girman da za ta fahimci Aji na dai dai da ita zai tsaya ya ga iya gudun ruwan ta amman da gaske ne ya yi nadama sannan yana ta tunanin shawarwarin Nasir a gare shi yana kuma tunanin gaskya ya faɗa masa Kamar lokaci ya yi da zai daina ganin laifi wani a kan wasu. Saboda yadda ma bai saurari Mu'azzam ba, bai samu sanar dashi rigiman ɗaki ba.
********
*MIMI*
Mimi yadda ta kwanta da Kuka haka ta tashi da wannan kukan, Hajiya ce ke ta faman lallashinta dakyar ta yi shuru har ta samu ta yi wanka amman ta saka wani abu a cikin ta ta kasa, ji ta ke yi kamar ba ta da ɗandano a harshenta sai da Hajiya ta nuna ɓacin ranta sannan ta iya shan Tea shima kaɗan, ba ta da aiki sai kwanciya tana hawaye domin in ta tuna irin cin zarafin da Aji ya yi mata sai ta kasa tsaida kukanta.
Hajiya duk ta damu ita da Baaba Uwani, ta kasa kiran kowa sai daga baya ta bi shawaran zuciyarta ta kira Alhaji Hamza ta ce ya zo gida in ya samu sarari yau tana neman shi ya ce sai zuwa dare domin baya gari ya shiga Bauchi.
 Mimi ta riga ta fitar da auran Aji acikin ranta a yadda ta ke jin kanta ba ta tunanin za ta iya kara zaman aure da shi, Shi ya sa ta na gani su Bintu da Hibba na kira ba ta ɗauka ba ta ga har kiran Mu'azzam ba adadi ba ma su kaɗai bakwata kwata ba ta ɗauki wayar kowa ba. Daga karshe ma sai ta kashe wayar gabaɗaya tunda tana da tabbacin Shi uban gayyar ba zai kira ba, to wanda ya ce in ta tafin ma zai fi, kuma a mganganunsa babu so ko tausayi da gaske yake baya sonta kenan tuni ya daina sonta a tunanita yana sonta har yanzu ashe ashe bata sani ba shi baya wannan tunanin kanta ya aureta ne domin ya ɗauki fansa abin da ya faru a baya shi ya sa ya riƙa kuntata mata amman duk dai ta daure, Shi ya sa jauswaa suka ce IDAN AN CIZA a hura saboda kar a gaba a yi nadama ita dai ga ta cikin nadaman saurin amincewa da auran Aji da ta yi cikin gaggawa.
 Yini ta yi kwance a ɗaki sallah kawai ke ta da ita. Bayan Tea ɗin da ta sha da safe ba abin da ya ƙara shiga cikin ta. Baba Uwani Saboda ita ta yi alalan manja da rana amman Mimi ba ta iya ci ba, Hajiya ta ce a dama mata kunin gyaɗa shi ne ma ta samu ya shiga cikinta a cikin kwana ɗaya ta rame Idanuwa sun Kumbura kamar ba Mimi yar gayu ba, Hajiya kuma har waya sun yi da Mommy amman ba ta iya gaya mata wani abu ba. Sannan da yamma Yaddiko ta zo duba ta amman har ta tafi ba ta gaya mata Mimi na gidan ba, ta bari dai Alhaji Hamza ya zo shine matsayin uba a wajenta in ya Kirata suka yi mgana ƙila ta iya gaya masa abin da ya faru.
Ta yi niyar kiran Meri amman sai ta fasa,a tunanin ita kanta Merin ya kamata ta nemeta amman shuru, ita kuma Inna Meri kunya da nauyi suka saka ba ta yi tunanin kira ba har tunanin zuwa gidan ta yi amman Kunya take ji ya sa ta rasa mafita a lokacin.