← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 93

Sashe 47

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aji so yake yi in an gama gidan can gabaÉ—aya sai ya kwashe kayan shi ya koma can gabadaya. Bayan ya yi wanka ya sauya kaya an kira sallar isha'i sai ya fita sallah da zai dawo ya biya ya siya ma su Inna tsire tana ta saka albarka, gabaÉ—aya ya gaji shi ya sa ya ce bari ya shiga ya kwanta.
Ya na kuma kwanciyar sai barci sai cikin dare ya farka ya ga Mimi ta kira shi ma, bai samu kiranta ba sai da asuba. Ranar lahadi me yana gida ko da ma ba lahadi ba ne an ba da hutu matasan yan Gombe United É—in duk sun tafi gida hutu sai yan nesa ne da kuma waÉ—anda ba sa son tafiya su suka rage kawai a camp É—in suna sake bitan traning É—in su.

Da wuri ya je ya ɗauki Mimi suka biya ma'aikatarsu suka ɗauki Rukky tunda ita ta shiga duba wani abu, suna kasuwan nan har bayan la'asar bayan sun gama da bangaren Atamfa, leshi, abayoyo, material sai bangaren jakunkuna da takalma sai bangarem kayan kwalliya da bangaren Undies, su dai kam bai bi su ba ya ce su shiga su kaɗai, sai da aka je shagon mayafai y aga Mimi ta na jidan mayafi kala kala sai da ta gama zaɓa sannan ya kalleta yana daga gefe ya harɗe hannuwansa a saman ƙirjinsa sannan ya ce" Duk waɗanan mayafan na waye?
Ta kannne ido É—aya kafin ta ce" Ana mana."
Sai kawai ya karkace kai kafin ya ce"Amman kinsan ba na son wannan abun ko?
Kai tsaye ta marairace kafin ta ce"Naka ne fa, in za mu fita tare zan riƙa yi maka kwalliya." Ya kasa mgana yana ta kallonta kawai Rukky ma ta saka baki tana faɗin"Yallabai a yi hakuri duk saboda a yi maka kwalliya ne."
Mai shago ma dake son ciniki sai da ya tanka kafin ya ce"Ango a yi hakuri, ka ji dai ta ce wannan na fita auting É—in Amarya da ango ne."

Kai tsaye Aji ya ce"Wani Ango? Ba fa Amarya ba ce, Yaji ta yi duk wannan abin daka gani domin za ta yi kome ne."
Mimi ta ji kunya ba ta san lokacin ta É—auki mayafi É—aya ta sarke wuyan Aji da shi ba, shi kuma sai ya rike mata gefen hijabi yana faÉ—in" Yi hakuri na manta to kin daka barkonu a ke cewa ba Yaji ba ko?.
Ya faÉ—a yana kallon Rukky da mai shago da suke ta musu dariya.
Saboda haushi ledan mayafan gabaÉ—aya ta hana yaran shago É—auka tac e shi zai É—auka zuwa mota hakan ban ya rumguma yana faÉ—in" Allah dai na gani."
Mimi ta taso masa da faÉ—in" Yana ganin mene?
Da sauri ya ce"Irin son da nake yi miki mana."

Sai aka bar Mimi da mirmishin jin daɗi, Mai shago da suka gama burgeshi ya ce"Allah ya sa ke da ƙara yin wani yajin har abada Hajiya."
Sai aka bar Mimi da jin kunya Rukky na dariya ta amsa da Amin Aji ya amsa da cewa"Ai ba za ta ƙara ba saboda tana tsananin sona, na bayaa da ta yi duk burga ce na sani."
Mimi ta É—auki Jakarta ta maka masa a baya yana dariya ya ce", Shi fa illah ka yi yaji kenan har Æ´aÆ´a da jikoki sai ya bika"
Mai shagom mayafai ya sha nishaÉ—i, Rukky kuma haka take ta dariya tana ma Mimi raÉ—an daman haka Aji yake? Mimi na dariya ta ce Ya fi haka ma in ya yi niyar yin raha.
Mimi ƙiri ƙiri ta ce ba zai kai mayafan nan Mlmota ba sai sun je shagon hijabai sannan haka nan da ledoji niƙi niƙi a hannu suka je shagon hijabi ta zaɓa amman anan suka bar masa sai an ɗinka yau ɗin ma sai mangariba suka fito daga kasuwa booth da bayan mota ciki da kaya Dakyar Rukky ta samu wajen zama.

Suna hanyar maida Rukky gida, Mimi take gaya masa abin da Rukky ta ce sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Ba haka nake ba fa, duk ita ta maida ni haka." Mimi ta daki kafaÉ—ansa tana faÉ—in" Wallahi ka daina gaya ma nutane na yi yaji ba na so"
Ta faÉ—a ta na shan mur.
Kai ya jinjina kafin ya ce"To ai shike nan na yi shuru da bakina."
Rukky dai ta na shan kallo suka sauketa gida suna ta mata godiya yau bai tsaya shan ruwa ba. Sun rabu dai akan gobe ba zai zo ba sai jibi ta yi masa abin shan ruwa kuma ta ci kwalliya saboda zai mori kallon matarsa sa son ran shi.

A gidan Inna Meri ya sha ruwa ranar. Washegari kuma gidan Nasir ne tunda shi ya gayyacesa tare da Makama, kamar ba zai je ba ba sai kuma ya tuna yanzu fa ya ce ya gyara sai ya shirya ya je,.Sai a ranar ma ya iya ganin Nafisa da Æ´aÆ´an Nasir, Nasir na ta yi masa tsiyan ya ji kunya bai san Æ´aÆ´an sa ba, shi kuma ya ce kada ya damu tunda dai shi ubansu ne ko da sun girma ne za su iya gane shi. Nafisa kuma sai da ta tambayi Mimi kai tsaye Aji ya ce" Nasir bai gaya miki ba? Ai ta yi yaji ne amman za ta dawo bayan sallah.'
Me su Nasir za su yi in ba dariya ba, ita kanta Nafisan sai da ta yi dariya, da zai tafi 10k ya ba ma Nafisa da yaran da ya koma gida ya kira Mimi sai ya gaya mata Nafisa ta tambayesa shi kuma ya gaya mata ta yi yaji, Mimi ta riƙa dariya tana fadin ita kam ta shiga uku da wannan yajin.
Shi kuma ya ce wlh kada ta ƙara. Domin yaji a aure yana da tambari, kawai miji bai sake ka ba sai ka dawo gida ka ce ka gaji da auran saboda samun waje, ta ce eh ta ji ai ta tauna tsakuwa aya kuma taji tsoro, ya ce kuma da wannan don wannan.

Ranar labara tunda sun yi anan zai sha ruwa a masallacin kusa da gidan Hajiya ya yi sallar mangariba dabino kawai ya ci ya karisa gidan. Da yake ya zama ɗan gida yanzu ya na zuwa kai tsaye falon yake shiga, Tabbas ya ga baƙuwar mota a haraban gidan amman tunaninsa bai kawo masa wani abu ba. Ƙananun kaya ne a jikinsa rigar mai ruwan kasa ce wandon kuma baki ne kafarsa takalmi ne mai buɗewa. Sai Kuma yau bai saka hula ba sumar kansa ta sha gyara tana ƙyalli, sallamar da ya yi ƙokarin yi ta makale ne a fatar bakinsa lokacin da ya yi mugun gani, to mugun gani mana, Mimi ce cikin kayatticiyar kwalliya na wani leshi fiteed gown, ta yi ɗaurin gashinta a waje daga baya, kuma ba mayafi ga kayan sun kamata tsam tana tsaye gaban wani namiji tana yi masa dariya.

Wani irin Kolulin abu ne ya ji ya taso masa ya tokare masa kirji saboda Kishi har duhu duhu ya koma gani. Daga anan sai ya ga kamar Mimi rumgume da wannan mutumin tuni idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir, jijiyon kansa suka ɗaga. Ya ma kasa yin wani motsi, Mimi ce ke facing kofar ita ta fara ganin shi daman roƙon Jaheed take yi ya tafi kafin Aji ya zo ya gan shi ya ja za mata wani bala'in ashe aikin gama ya riga ya gama. Ba ta san Jaheed ya zo garin ba sai kwatsam tana wanka ya zo gidan bayan ta gama yi ma Aji abincin shan ruwa ita ba ta ma san ya zo ba ta shirya ta fito ne Hajiya ke gaya maya Jaheed na falo yana jiranta.

Da sauri ta bar gaban Jaheed ta fara takawa zuwa wajen Aji amman wani kallo da ya yi mata ya sa ta tsaya cak. Da ya sa Jaheed ya juya shima sai ya ga abin da ya sa Mimi rawan jiki ya gane shi saboda yadda Mimi ta so shi ya sa har hotonsa yana da shi a wayarsa sannan yana da duk wani labarinsa

Ya yunkura domin ya bi bayan Mimi sai kawai Aji ya juya da sauri ya bar falon, Mimi ta mara mishi baya da sauri tana kiran sunan shi.

"Aji.."

"Mansoor"

Amman ina ko juyowa bai yi ba, yana zuwa da sauri ya shiga motarsa ya kunna ta zo tana ƙwankwansa masa gillas ya yi banza da ita. Ribas zai taka yana ƙokarin taka ta sai ta yi tsalle ta koma gefe dai dai lokacin Jaheed ya kariso sai ya riƙe mata kugu yana tambayanta ko Lafiya take, wannan rikon a Idon Aji da sai da ya ji kamar ya mutu hon ɗin ma da karfi yake saki Megadi ya buɗe masa get ya fice da gudu kamar zai tashi sama.

*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB30011*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Chapter 47 · 0% Book details