Sashe 12
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yaya Mansoor, kan maganar abin da ya faru ne, kasan dai ba ka kyauta ba ko? Inna na fushi da kai, sannan ka ɓata ma su Nasir rai ya kamata ka kira su ka ba su hakuri."
 Aji ya yi shuru kafin ya ce"Zan dai iya zuwa na duƙa na ba ma Inna haƙuri tunda Ita ta haifeni, amman naganar na ba su Nasir haƙuri bai ta so ba, domin ba ni na aike su ba."
 Mu'azzam bai yi mamaki ba sanin halin yayan na shi sai kawai ya ce"Ni na ba su hakuri tunda ni na gayyace su a lokacin.'
Aji ya yamutsa fuska kafin ya ce"Allah ya ƙara, kai ma rashin jin mgana ta ne, me na gaya maka?
Sai kawai Mu'azzam ya ce" Maganar ita Anty Mami fa? Ya kamata ka je Yaya bai kamata wannan abin da da kake yi ba."
Aji ya yi jim kafin ya ce" Itama za ta dawo in sha Allahu."
"Yaushe? Ba fa za ta dawo ba sai ka je ya kamata ka darajata, sannan iyayenta su gane ka daraja Æ´ar su"
Aji ya yi gajeren mirmishi kafin ya ce" Daman ai ta tafin ne saboda na je gidansu ina roƙo? To ku kyaleta ta yi ta zama mana waya damu?
Mu'azzam na shirin ƙara mgana. Kawai ya ji Yayan na shi ya ce"Kai ni fa barci nake ji, Kai ba ka gaji ba ne? Maza ka je wajen matarka sai da safe."
Bai ba shi zarafin mgana ba kawai ya katse wayarsa ya bar shi nan sake da baki, Daman Hibba ta shiga ciki ne ta ba shi waje su yi mgana sai ga shi ta dawo yanayin da ta ganshi yasan ta san abin da ya faru.
"Ba'a dace ba ko?
 Mu'azzam ya yi shuru kafin ya ja numfashi ya ce" Ya ce zai je ya ba ma Inna hakuri, amman ba zai ba ma su Nasir ba. Maganar Anty Mami kuma ya ce za ta dawo da kanta amman shi ba zai je gidansu yana roƙo ba."
Hibba ta kaɗa kai kafin ta ce" Ina mamakin yadda yake da ƙwarin gwiwan a kan wai Mimi za ta dawo da kanta? Ina tsoron wannan jin kan na yayanka ya tashi a banza Mimi ta ja shi kasa warwas. Sannan in da ta na ɗaukan wayana sai na gayamata kada ta sake ta koma sai ya raina kansa."
Wani kallo ya yi mata, kamar zai yi mgana sai kawai kuma ya fasa, ya ta shi ya shige ciki jikinsa a sanyaye Hibba ta bi shi da kallo gaskiya magana ce fa sai an faɗa Yaya Mansoor ɗin nan ya cika jinkai da Isa, shi wai ya na takama da cewa Mimi na son shi wato ba za ta iya rabuwa da shi ba. Daman illah ne babba mace ta nuna ma Namiji soyayya mai tsananin da za ta ya iya yin komai saboda shi kuskure ne babba ga Maza ma irin su Mansoor da ba su san darajan da ƙimar da Ubangiji ya ba ma mace ba. Tana tattara kwanukan da suka ɓata ne take wannan tunanin, haba ka yi laifi amman taurin kai da jinkai su saka mutum tunanin kai ne ma za'a ba ma hakuri haka ake yi tsakani ga Allah, gwara Mimin ta sha zamanta sai ta ga karyan tsiya ita dai tasan wlh shima yana sonta in ya ga zai iya rasa ta dole dai ƙanwar na ƙi.
********
*Bayan kwana uku.*
Kimanin Mimi na da kwanaki takwas kenan a gidan Hajiya, Rukky ba ta sani ba saboda Bibi ba ta sani ba domin haushi ya sa Makama bai gaya mata ba, Sannan Mimi na cikin hutun ta ne, ba ta zuwa wajen aiki kuma ita ba ta dame ta a waya ba tunaninta yanzu ba da ba ne, Mimi na da aure ita ba ta san ta na yawan kiranta saboda wannan mara mutumcin mijin nata.
 Ranar tana wajen aiki Na Misau na zencen Mimin sai ta ɗaga waya ta kirata amman Sai ba ta same ta a waya ba sai ta yi tunanin in ta tashi daga wajen aiki za ta biya ta dubata, la'asar ta baro ma'aikantarsu ta hau adaidaita zuwa Gidan Wanzamai a kofar gida ta haɗu da Baba Danjuma a lokacin su ka gaisa, shi kuma bai yi mata wani bayani ba sai da ta shiga gidan, abin da ya bata tsoro shi ne ganin wata a ɗakin Mimi, Saboda lokacin da ta shigo Inna na ɗakinta, Walida kuma ta tafi makarantar Islamiya.
Shi ya sa ta shiga É—akin Mimin kai tsaye sai kawai ta ga komai ya sauya har da mai É—akin ma gabaÉ—aya.
 Cikin mamaki ta ke kallon Maaesha kafin ta kara komawa baya a tunaninta ko ta yi makuwan shashen ne. Sai dai ta ƙara ganin tabbas nan ne.
Cikin mamaki ta ce"Ko na yi makuwa ne? Ba nan ne É—akin Mimi matar Mansoor ba?
Maeesha na zaune ta na cin Aya ta yi waata yar dariya kafin ta ce" A da ba, amman yanzu ya zama É—akin Maeesha matar Saddiqu."
Rukky ta yi shuru tana kallon Maeesha cikin tarin mamaki, amman ba ta sake mgana ba gabanta na faɗuwa ta fita daga ɗakin rike da wayarta tana ƙara kiran layin Mimi sai kuma ta shiga dalilin da ya sa ko ɓarayin dakin Inna Meri bata kallah ba.
Allah ya taimake tana fita sai ta ga mai adaidaitan da ya kawo ta bai tafi ba ya tsaya mgana ta waya sai kawai ta faÉ—a ciki dai dai lokacin da Mimi ta É—aga kiran Rukky.
"Baby Ruƙayya.."
 Mimi ta faɗa cikin sanyin murya, Ita kuma Rukky Kamar zuciyar ta za ta fito waje ta ce"Fatima kina ina ne? Na zo gidan mijin ki a ɗakin ki na ga wata, ko kin ta shi ne ban sani ba?
Mimi ta yi dariya daga bangarenta kafin ta ce"Eh! Ina gidan Hajiya ki zo ki same ni."
Cikin faÉ—uwan Gaba Rukky ta ce"Mimi me ya faru ne? gaba na faÉ—uwa."
"ke dai ki zo, ba komai sai alheri."
Daga haka ta katse wayar, Rukky gabaɗaya sai da jikinta ya yi sanyi, mai adaidatan na mganar Hajiya komawa za mu yi? Tace Eh amman yanzu anguwan Hashidu Estate za su je, nan da nan ya juya kan adaidata suka nufi gidan su Hajiya.
 A Gaggauce Rukky ta shigo, gidan Hajiya na falo Baaba Uwani na kitse mata kanta da ya cika da farin ga shi. Tsabar ma ruɗewa da gaisuwan da tambayan Mimi duk a lokaci ɗaya ta yi su, Hajiya ta ce tana ciki ta shiga ta same ta ai ko har da gudunta ta wuce Hajiya da Baaba Uwani suka bi ta da Kallo Hajiya ta girgiza kanta kafin ta ce"Ina ga ta ji labarin Binta na gida"
Baaba Uwani ta ce"Hajiya yanzu ba za'a gyara lamarin nan ba?
Hajiya ta ce" To Hamza ne kan batun ya ce na cire bakina, sai in har Mijin Binta ya tako da kansa sannan za'a yi maganar gyara."
Baaba Uwani ta yi shuru kafin ta ce" kuma bai zo ba ko? Ni fa kamar sau ɗaya ma na taɓa ganinsa tun bayan auran nan."
Hajiya ta jinjina kai kafin ta ce"Zuwan na shi bai wuce É—ayan ai zuwa biyun."
Baaba Uwani na son cigaba da Magana amman Hajiya ta kauda mganar ta fara mata zencen mutanen can garin su na Akko sai su saki hiran Binta suka kama ta mutanen gida.
 Mimi na kwance ta na latsa wayarta Rukky ta faɗo ɗakin cikin damuwa. Kamar ta faɗa kanta haka ta faɗa saman gado tana faɗin" Kar dai ki faɗa min kun rabu ne?
Mimi ta miƙe da sauri ta na faɗin" Rukky me ye haka? Kin bani tsoro wlh."
Ba ta damu ba sai ma gyara zama da ta yi ta na faÉ—in" Don Allah ki gayamin abin da ke faruwa ko zan samu natsuwa."
Mimi ta yi shuru kafin ta ce" Eh mun rabu amman ba mu rabu ba."
"Ban gane ba?
Rukky ta tambaya cikin zullumi.
Sai Mimi ta gyara zama tana faÉ—in"Rukky labarin na da tsawo amman takaice shi ne na dawo gida ne.
"Saboda mene?
 Ta tambaya tana mai tsare Mimi da ido, ita kuma ta kauda kanta saboda Idanuwanta sun fara tallah kwalla, babban baƙin cikinta yadda ta fahimci ba ta da wata faraja a wajen Aji kwananta takwas da dawowa Gida amman ko kiran ta bai yi ba, ba Saƙo ba zuwa kenan ya nuna ma kowa cewa bai Damu ba da zamanta da tafiyarta duk ɗaya ne a wajensa.
Kawai sai ta saka ma Rukky kuka, ita kuma baki buÉ—e take kallonta kafin ta ce"Mimi me ya faru ne? Ki bar kukan nan ki yi min bayani domin Allah."
Miƙewa Mimi ta yi zuwa gaban window ɗin da ke ɗakin lokaci ɗaya tana faɗin" Ruƙayya ban taɓa tunanin hukuncin da na yanke ma rayuwata na auran Aji kuskure ba ne sai yanzu, na yi gaggawa me ya sa bayan na ciza ban tsaya na hura ba? Rukky Aji ba ya sona iya wancan Soyayya na yarinta ta gushe a zuciyarsa ya aure ne kamar zai rama abin da Abi ya yi masa a shekarun baya, Rukky Aji baya sona tunda na aure shi bai taɓa kama hannuna da gangan ba sai dai bisa Kuskure."
Ta yi shuru ta na sauke numfashi Saboda kuka ne ke cin zuciyarta.