← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 93

Sashe 90

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ta kira wayar Hibba bayan ta cire ta a blaklist ta ba ta hakuri itama ta ba ta hakuri shike nan sai mgana ta wuce. Amman fa Madiha sako ta turama Mimin da cewa ta gode tunda ta ba da damar da Mijinta ya zage ta har Dr ta kira ta gaya mawa shi kuma ya ce abunda Mansoor ɗin ya yi daidai nw in ita ba ta da hankali sai ta yi ta yi,Khadi ma ta kira Mimin ta mata surutun ta zaɓi namiji a kan su ƴan'uwanta tunda a gabanta ya zagi Madiha ta kasa mgana ita dai sai hakuri ta ba su, tunda ko ita ba ta tsira da faɗan ba kuma suna nan a kan bakansu na ba su som auren. Sai ga shi wata ɗaya da wani abu da auran mommy Khadi ta samu matsala da dangin mijinta sai ga ta gaban Mommy tana kuka, Mommy ita ta kira mijin khadi ya zo har gida suka yi mgan matsalace ta gida yayyensa ne suke son ya kara aure, karshen dai Alkalin da suka raina suke jin haushi ya tsaya mata tare da Mommy dashi suka maida ta kaduna suka kuma nuna ma mijinta ba ruwan Khadi da auransa amman ya kare mutumcin matarsa tunda yayyen nasa har gida suke zuwa su ci zarafinta, tun daga nan Khadi ta saduda itama Madihan ganin ba ta da abokin adawa yavsa ta fara saki amman ba duka ba. To ta na da wacce tafi Mommyn ne? itama Madihan kuɗi ya hado su da Mijinta tunda Kuɗin na su a waje ɗaya ne suna kasuwanci ti shekara ta yi kuma an zauna ana ta lissafi an gano dai shima yana karkatar da wasu kuɗi rigima har Abuja wajen Mommy. Sai ga shi Alkali Mustapha shi ya warware matsalan a ka samu sulhu, itama daga nan ta fahimci aure ga mace sutura ne komai tsufanta kuwa, ta saki suka rumgume alƙali a matsayin uba sannan akwai yarsa Batula dake aure a lagos Lakcara ce a Legal ya haɗa su suna zumumci itama Khadi akwai namiji a kaduna yana aiki da NNPC Shima tare da iyalansa sun zama ƴan'uwa tare da Khadija
akwai wacce ke kano, sunanta Badiyya likitan yara ce ashe ma asibiti ɗaya suke aiki da Sulaiman ya san ta ta san shi sai wannan dalilin ne zumuncin su ya ƙara zama na sosai Iyalanta na zuwa gidansa shima iyalansa na zuwa, ɗayan namijin Soja ne yana Abiya tare da iyalansa amman suna mgana a waya dukkansu.

Bayan wannan ya wuce an samu daidaito zukata kuma sun samu natsuwa sai Mimi ta kara bijiro da mganar ta na son siya wata sabuwar Motar, Aji dai da ta nemi shawaransa cewa ya yi" Ni tun a baya na baki shawara,sannan na yi miki alƙwarin in na samu kuɗi da gumina zan siya miki mota amman na ga kamar kina sauri ne bazan hana ki siya ba tunda kuɗin ki ne amman da kin hakura da siyan wata motan ki cigaba da lallaba taki, ga tawa ma duk ki haɗa ki riƙa amfani da ita, in har Allah ya hore mana ko Jirgi ki ke so zan iya siya miki Mimi ba ma mota, gwara ki fara ko wani kasuwanci ne da kudin kamar zai fi,amman in ba ki ji shawarata ba shike nan ba zan hanaki yin yadda kike so da kuɗin ki ba."
Da ta yi mgana da Mommy da Hajiya suma dai shawaran da suka bata kenan sai ta amince da shawaran ta fara kasuwanci amman ta rasa ina zata fara tunda ba ta da Ra'ayi ko ido a kan kasuwanci da ta yi mgana da Aji sai ya ba ta shawaran ta yi mgana da Yayarta Madiha ai yar kasuwa ce za ta ba ta shawarwari amman shi da ita sun tsaida shawaran ta fara kasuwancin saida Abayoyo da jaka da takalmi in ta karɓu har shago za ta iya buɗewa.

Ta yi mgana da Madiha kuma ta yi na'am da shawaran Mimi ta ce za'a riƙa mata Oder jakunkuna wasu daga Lagos wasu kuma daga China ko India ko Italia,dogayen rigunan kuma daga daga Dubai, tunda ita tana harka da yan kasuwa daga kasashen waje tuni ta haɗa Mimi da su har ta tura kuɗi za'a fara kawo mata kaya kaɗan ta jaraba ta gani. Tunda tana aiki tallatawa ba zai mata wahala ba In ji mijinta Mansoor Ibrahim Aji.

******

"Maryama(Ummi) na da wattani goma sha ɗaya a duniya Mimi ta samu wani cikin, kuma har ya yi wajen wattani biyu da kwanaki a jikinta ba ta sani ba, kamar na Ummi ne, shima bai zo da laulayi ba in da ma ta fahimta ta na yawan ganin jiri da tashin zuciya sannan aiki kaɗan sai ta ji ta gaji kasala duk ya rufeta sannan sai ta fara,kwana da zazzabi mai zafi lokacin Mansoor Aji ba sa nan ya fita wasan shi na farko a kasar Ghana, amman ya bubbuga wasu anan Nageria ƙaananun wasanni wannan ne dai suka tafi wata kasa buga wasan.

Ba ta gaya mai ba ta da lafiya ba ta shirya ta je asibiti domin tafara zargin ciki gare ta sai ga shi gwajin farko a ka gani ciki ɗan wattani biyu da kwanaki a cikin jininta. Hankalinta ya yi bala'in ta shi Ummi ba ta shekara ba amman ta yi yawo tana tafiyanta da kafarta ko'ina amman ita ba ta shirya kara haihuwa ba shirye shiryen komawa makaranta ma take domin yin Phd ɗinta tunda yanzu alhandulillah komai na duniyan ta samu, miji nagari sannan ta samu kuɗi tunda Allah ya saka ma kasuwancinta albarka Odar kusan na goma kenan kuma tana samun ciniki da sun iso da sun ƙare. Sannan Hibba na sara acan kano kuma ta na aikawa da shi Abuja Asma'u na tallata mata ta Online anan ma Gombe sai gqmdala tunda gidan Talabijin ɗinsu ta ba ta dama ta tallata kayanta Shike nan da ta kawo oder suke ƙarewa musamman ma abayoyin. Sannan Rukkya ma ta na saran Abayoyin ta na siyarwa tunda zaman ko me ka taka ba zai yuyu ba ita mace da sana'a a ka santa domin cigabanta. Duk da ta koma can lagos ɗin tana aikinta a wani gidan Talabijin amman duk da haka ta ce itama za ta fara kasuwancinta amman sai ta samu jari mai ƙarfi.

Duk da ba ta yi mgana da gogan nata kan maganar cigaban karatun nata ba amman ta saka a ranta za ta matsa masa sai ya barta tunda dai ba mazauni ba ne,sai ya yi wata biyu ba shi a Gombe ballantana yanzu da aka fara haskashi a duniya ba ma ƙasa ba, shiyasa ta yi tunanin ijiye aiki ta koma makaranta duk da tana da tabbacin mijinta ba shi da ra'ayin ya maida ta Abuja da zama a kusa da shi ya sha faɗa mata a Gombe za ta cigaba da zama ba wai don baya bukatar ta acan ba a'a sai saboda Inna in ya koma Abuja da zama zai zama sai bayan wasu wattani za ta ganshi kamar Mu'azzan kenan. Shi kuma baya son haka ba ta da kowa sai su ba zai yuyu in har Mu'azzam na kano shi kuma ya bar Gombe ba, saboda Iyalansa ya san a kai a kai zai riƙa zuwa Gombe ba kuma ita saboda aikinta ba sai saboda wannan dalilin na shi, da kuma dalilin ba ya son barin garin Gombe saboda yana son garin kamar yadda itama Gombe ta zame mata wani jigo a rayuwarta ba tun yanzu ba tun tana ƙarama take ƙaunar garin.

Bta dawo gida cikin tashin hankali, ko wasan su Aji da aka haska a tashar Rt Tv ta dai kallah ne amman hankalinta baya wajen sai daga baya ta fahimci Nageria ita taci ghana da ci biyu da É—aya. A Daran Khadi ta kira ta tana mata murna ta ce suna ma kallo ne sannan Rukky ma sun yi mgana ta ce sun kallah jar da Daddy shima da Mommy sun kalli wasan na shi,a gida kuma Inna ma ta kalla tunda Walida na gari ta zo gida hutu, ita duk ba wannan ne damuwanta ba ya za ta yi da cikin jikinta? Sun kuma kasa samun lokacin su yi mgana ta waya sai dole ta yi hakuri suka dawo daga Ghana ya zo Gombe sannan ta gaya masa ga halin da take ciki ya fara murna kamar zai goyata cikin taruwan hawaye ta ce" Ummi fa ko shekara ba ta yi ba Baban Maryam? Sai ya kalleta kafin ya ce"Shi ne me? Ummi ai ta girma ta na tafiyanta ko'ina ina waÉ—anda ke samun ciki bayan sun yi arba'in ma? Amman ke nan da kafin ki sauka Ummi ta kusa shekara biyu ba na son wannan koke koken naki, daga Allah ya baki kyauta sai kuma ki fara min kuka?

Cikin hawaye ta ce"Ni ina tsoron haihuwan ne kai da kai ne sai ka ga ba lokacin ma da za ka iya ma yaranka tarbiya."
Kai tsaye yvace"Ba ruwanki da wannan tarbiya ta Allah ce duk da ke ma da naki kokarin amman ni nasan tarbiyan Æ´ayan da zamu haifa ba za su gagaremu ba, Sannan in mganar halin rayuwa ce daman ita kan saka a guji haihuwa ma gabaÉ—aya Fatima Allah ya rufamin asiri ba ma ke da yayan da Allah zai bani ba, ina É—aukan nauyin mahaifiyata da Æ´an'uwana saboda haka duk abin da kike tunanin ma ba zai faru ba ba zai faru ba, in sha Allahu. Abun damuwar kawai lafiyan ki da ta Ummi za mu je asibiti mu yi mgana da likita sai ya bamu shawara ko? Mimi dai ta kasa mgana sai kuka, shi ya share mata hawaye ya rumgumeta yana lallashinta ga shi ta na so ta ce so take ta koma makaranta amman ba ta samu wannan damar ba.
Chapter 90 · 0% Book details