← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 93

Sashe 14

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har aka shafe wajen sati biyu da komawar Mimi gidan Hajiya, Ba Mansoor ba ƙeyarsa bai ƙara tako kafarsa gidan Inna Meri ba, ita kuma daman ta ce ta cire hannunta a kansa.
Baba ÆŠanjuma ne yaga rashin jankalin Mansoor ya yi yawa sai ya kira shi a waya yace duk abunda ya ke yi yau da daddare ya zo gida ya same shi.
Sai ya amsa masa da toh, shi kuma daman Kunyar Inna meri yake ji, yana so sai ta fara hucewa sannan yana fargaba ya shigo gidan ba Mimi a cikin shi. Har gabansa faduwa yake yi in ya tuna bata nan bayan ganinta a cikin gidan ƙarƙashin Inuwarsa Kuzarinsa har karuwa yake yi in ya shigo gidan ya ganta, yana so ya kirata amnan kuma yana tunanin in ya kirata kenan ta yi nasara shi ya sa yake iya sarrafa damuwarsa amman shi duk a tunaninsa Mimi za ta dawo domin kanta bai taɓa tunanin za ta iya ba shi Wahala ba.

  Wajajen karfe tara ya zo anguwan a mashin ɗin haya saboda motarsa sai an mata juye, mashin kuma duk ya yi kura tunda ya daɗe bai yi amfani da shi ba, Sai kawai ya hayo na haya ya zo a kofar gida ya iske Baban Danjuman na jiran shi, ya san akwai mgana aiko ya sha faɗa kamar zai dake shi yana kuma nuna masa illar abin da ya aikata Mahaifiyarsa na fushi da shi amman ya nuna bai damu ba.
Kansa na ƙasa ya ce"Na damu mana Baba, kawai dai na ga ranta Inna  ya ɓaci sai na bari a ɗan kwana biyu in ta ƙara hucewa sai na zo na bata hakuri."
Baba kamar ya kai masa duka cikin takaicinsa ya ce" Haba Baban inna ina tunaninka yake ne? Ita uwa in ta yi fushi ba ta bukatar a bata lokaci Mansoor, a lokacin za ka yi kokarin kaga ka nemi gafaranta yanzu adadin kwanakin da ka ƙara adadin ɓacin ranta a kanka, Maza mu je cikin gida ka duka ka nemi gafaranta."
Kafa da kafa Baba ÆŠanjuma ya tasa shi har falon Inna Meri ta na zaune tana kallon Tibi tunda akwai wutar nepa. Walida na kwance kan kujera tana game da wayar Inna.
Sautin waƙa kuma na tashi daga ɗakin Matar Saddiqu haka take duk dare ta hana mutane sukuni.
Bayan sun shigo Walida ta mike tana gaishe su Baba kaÉ—ai ya amsa ban da uban gayyar, Inna Meri ko mijinta kaÉ—ai ta yi ma sannu da zuwa Mansoor ko kallo bai isheta ba.
Sun zauna kenan Shi Baba a saman kujera shi kuma Aji a ƙassn cafet.

  "Daga ina wannan sautin ke fitowa?

  Baba ya faɗa lokaci ɗaya yana kallon Inna Meri wacce ta yi kamar ba ta ji ba,Junoir ne kan jikinta ya yi barci shi kawai ta gyara masa kwanciya ta cigaba da kallon shirin gata nan gatan nan ku da ake haskawa a Karamchi tibi. Walida ce da ta kawo musu ruwa ta ce"Baba ɗakin Matar Yaya Saddiqu ce wlh tunda ta dawo wannan bangaren ba ta barin mu yi barci da saka kide kiɗe. Da Inna ta yi mgana sai cewa ta yi nan gidan Mijinta ne ba wanda ya isa ya takura mata."
Mansoor ya ji ransa ya baçi sai dai bai yi mgana ba ganin Baba ya yi shuru kawai bai ce komai ba Domin magajiya ta fi karfinsa har barazana ya yi mata na saki amman ta nuna bata damu ba sannan Inna Meri ta ce kada ya hana natar Saddiqu tarewa domin Allah kar ya sake mgana shi kuma yana ganin darajan Inna shi ya sa ya yi shuru.

"Je ki faÉ—a mata ta in ji ni na ce ta kashe sautin nan, ko ba ta san dare ya yi ba ne?

  Baba ya faɗa cikin nuna ɓacin ransa, sai Walida ta amsa da toh,  har za ta fita Inna Meri ta dago tana faɗin" Walida dawo abun ki, kyaleta Mallam ai gaskiya ta faɗa nan din gidan mijinta ne, ni ban isa na takura mata ba."

"To Inna ke sa'arta ne da za ta gaya miki haka? Ko ba ki isa ki ce ta daina abin da take yi ba ne?

  Mansoor ya faɗa ransa bace, Inna Meri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce" ta isa ne shi ya sa ta faɗi haka, me ya sa zan damu?  duk wa ya ja min? Ɗan da na haifa ne da cikina ya sa na koma abun cin mutumcin acikin gidan nan tunda ko shima bai ɗauke ni wata aba mai daraja ba, to tunda ɗan da na haifa bai ganni  da daraja ba wa zai kake tunanin zai kalleni da daraja?
Ta faɗa cikin jin ƙuna a cikin ranta.

"Ki yi haƙuri Inna.."

  Ta yi masa shuru kamar ba ta jisa ba. Sai da ya ƙara faɗin" Ki yi haƙuri inna don Allah ki yafe min."
Sai a lokacin ta juyo tana kallon shi kafin ta ce" Haƙurin me kake ba ni? Ka min wani laifi ne? Ba ka min komai ba ta shi ka yi tafiyarka sabogiginka Allah ya yi albarka."
Ta faÉ—a lokaci É—aya tana kokarin É—aukan Junoir da ke kwance saman jikinta,
Da sauri Baba Danjuma ya ce"Ki yi haƙuri Meri ki tsaya ki saurare shi, tunda har ya gane kuskuren shi ya baki haƙuri domin Allah ki daina fushi da shi"
Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba, Baban Inna na ta ban hakuri Baba Ɗanjuma na tayasa sai kawai ta ce"Ni fa ban riƙe shi ba. Har ga Allah na yafe masa Saboda ɓacin raina zai iya jefasa cikin bala'i, hannuna ne na ce na cire a kan rayuwarsa ya je ya yi duk rayuwar da ta yi masa dai dai."
Baba ÆŠanjuma ya ce"To baki hakuran ba kenan?
" Wlh na yafe masa tuntuni a cikin raina."
"To in har kin yafe masa ina nema masa alfarman ki shirya ki je gidan Hajiya ki yi masa bikon matarsa."

  Dariyar nishaɗi inna ta saka kafin ta ce"Au an zo wajen kenan? Tana gama faɗin haka ta mike ta sunkunci Junior lokaci ɗaya tana faɗin" Ai ya ce ba ya sonta shi ya sa ya ce ta tafi gidansu, in ya ga dama ya sake ta duk ban damu ba ni abu ɗaya ya dame ni yadda ya ɓatamin suna ya sakani jin Kunyar yarinyar nan da Iyayenta, Amman ni ban damu da duk abin da ya aikata ba wannan rayuwarsa ce abin da ya fi masa daidai shi zai yi."
"Ki yi hakuri Inna."
Abunda Kawai Mansoor ya ce kenan, Baba Danjuma a ka bar shi da cewa" ba ki dai yafen ba kenan?
Inna Meri ta ce"Na yafe masa, amman wallahi tallahi kafata ba za ta taka gidan su Binta da sunan yi masa biko ba. Shi ne ke auran nan in har ya na son natarsa yana da Kafa kuma ya san in da zai sameta amman in ni yake Jira to ya daina jirana na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba, ba in da zan je"
Tana gama faÉ—in haka ta shige cikin uwar É—aka in da Walida ke kwance ta kasa kunne tana ganin Inna ta shigo sai ta yi barcin karya.
A ranta ko daÉ—i ta ji wlh kada Inna ta je, shi da ya aikata barnansa ya je ya gyara da kansa.

  Ganin Inna ta shige ya sa Baba ɗanjuma ya kallesa kafin ya ce"Tunda ta na ce to ba za ta je ba, ka shirya ka je ka yi bikon matarka ka ji ko?
Cikin jinjina kai ya ce"In sha Allahu Baba., daman ai tsakanina da Mimi ba saki, amman za ta iya yin yaji wani lokacin in bukatar hakan ya ta so."
Kai tsayen shi ya faÉ—i haka, kuma har acikin zuciyansa haka yake nufi.
Sai Baba Danjuma ya ƙara faɗin" Ko kuma in za ka je ka min mgana sai mu tafi tare"
Da sauri yac e"A'a Baba kada ka damu ba sai ka je ba."
"Ka tabbata?
Sai ya gyaÉ—a masa kai, shi kuma sai ya dafa kaffaÉ—ansa kafin ya ce"Sannan ka yi hakuri akan abubuwan da suka faru, kasan halin magajiya ita ta saka rigimar dawowar Matar Saddiqu É—akin Fatima, yanzu in za ta dawo a ina za ka ijiye ta?
Mirmishi ya yi kafin ya ce"Wajen zaman ta ba matsala ba ne Baba, bakomai na gode ƙwarai Allah ya ƙara girma."
Baba Danjuma ya amsa da Amin bai daÉ—e ba ya ce zai tafi 30k ya ba ma Baba ya ce Auwalu zai kawo kayan abinci na wannan Watan Baba Danjuma nata godiya har ya tafi Inna Meri ba ta fito ba, ga shi ya na jin yunwa amman kuma yasan yau Inna ba za ta basa abincin ta ba.
Da ya fito ya tsaya jim ya na kallon ƙofar ɗakin Mimi, na wani lokaci sannan ya kaɗa kai ya fice, dole zai ɗauko mataki daga Saddiqun har matarsa ba su isa su raina masa uwa ba.

  Bayan fitan sa ma Baba Ɗanjuma da kansa ya tsaya kofar ɗakin ya yi ma Maaeesha mganar ta kashe wannan Sautin ba ta da yadda za ta yi dole ta kashe, Saddiqun baya nan ya koma Lagos daga nan ya shiga ɗakin Magajiya ya ja mata kunne ya ce ta yi mata Surukarsa mgana wlh baya son diɓan albarka ta daina takura ma Meri da daddare da sautin banza in ba haka ba wlh za ta bar masa gida.
Magajiya ta buga shewa ta ce saboda Meri zai kori matar É—ansa? To lalle kuwa sai dai itama Merin ta bar gidan. Shi dai bai biye mata ba ya fice zuwa É—akin sa ya barta tana Kumfar baki ko kunyar Mariya dake É—akin ba ta ji.
Chapter 14 · 0% Book details