← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 93

Sashe 25

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hibba na dariya ta ce"Nan gaba kaÉ—an zai ce saboda ke ce rayuwata. Sunan Inna tuni zai manta da shi."
Dariya suka saka har suna tafawa, Mu'azzam ya san waye yayan shi fiye da kowa amman ya na tausaya masa Saboda ga duk alamu wannan karon Mimi sai ta Jijiiga yan maza. Daran shi da Hibba kusan raba dare suka yi suna ta tattauna batun Hibba na goyon bayan Mimi shi kuma Yana goyon bayan Yayan shi yana tausayin shi ita kuma Hibba ta ce ai gwara dai a jijjiga shi saboda duk abin a ya faru shi ya ja. Daman ance ai dama É—aya take zuwa a rayuwa shi ya bar daman na shi tun a farko ga shi yanzu ya fara nadama dukda dai bai fito ya furta ba amman kowa ya san ya yi nadaman maganganun da ya faÉ—a Mimi a wannan daran.

******

Mansoor bai ƙara tsinkewa da lamarin ba sai daran ranar jumma'a da ya zo gidan, shima ɗin ya zo duba Baba ne da baya jin daɗi mura ta kwantar da shi.Shima sanin shi Yaya Amina ce ta kira shi take gayamasa Mu'azzam ma ya kira shi baya kusa da kuma ya zo ya gani bai kira ba.
Baban ya ji sauƙi amman ranar bai fita ko'ina ba yana gida. Zuwan Mansoor ne ya Dauke sa zuwa wani ƙaramin cinic suka amso mganguna ya biya ya siya masa tsire da fura sannan ya dawo da shi gida ya kuma kaisa har ɗakinsa ya tsaya a kansa ya ci naman ya sha furan kaɗan ya balla masa magunguna ya sha ya kwanta.
Inna Meri ta yi ta shigowa duba shi. Anan ne na yake ce mata ta ɗauki tuwon ta ya yi kwantai. Tsire Baban inna ya siya masa ya ci ya ƙoshi, ba musu Inna ta ɗauke kwanukanta Mansoor yana shirin ya ci ne ya ga Tuwo ne miyar Kuɓewa ɗanya amnan tunda Inna ta kwashe kayanta ya san sai dai ya haɗiye yunwarsa.

Shigowar Magajiya ya sa ya bar ɗakin zuwa bangaren Inna ba wutar nepa amman akwai hasken farin wata sannan garin an fara zafi. Da ya sawo kanshi shashen ya ga mutun kwance gabda ƙofar ɗakin Inna Meri, ya ɗauka Walida ce bai kawo ma kansa matar Saddiqu ba ce shi ya sa yana karisowa ya fara faɗin" Ke Walida ƙofar ɗaki ne wajen kwanciya? Ba na son wawanci kwashe wannan shinfiɗar a wajen"
Shuru ba magana sai ranshi ya ɓaci ya Daka mata tsawa ya na mai kiran sunanta amman Maeesha ko gizau daman tun fara zafi ta samu wannan iskancin sai ta zo ta simfiɗa abin shimfida ƙofar ɗakin Inna, ko innar ne sai da ta raɓa ta gefe ta wuce Walida ta yi mata magana ta ce ɗan cikinta ba ya son zafi ko za ta hana ta kwanciya ne Inna ta ce ta ƙyaleta kada ta kara mgana.

"Yayanmu gani nan fa."

Walida ta katse shi daga Kiran sunanta da yake yi, ya ɗaga kai yana kallonta cikin mamaki kafin  Ya yi mgana da sauri ta ce"Matar Yaya Saddiqu ce."
BuÉ—e ido ya yi kafin ya ce"Oh iskancin nata nan kuma ya dawo? In iskar take son sha ta je Kofar É—akin magajiya mana sai anan duk ta tare ma mutane hanya"
Bai tsaya ba kawai ya nufeta gadan gadan kamar zai takata da sauri ta matsa baya da sauri da kwanciyar sarakai ta yi tana hararan shi tana ko matsawa ya saka takalminshi ya ture shimfiÉ—ar yana faÉ—in"In ta sake kwanciya kada wanda ya kauce mata, ku taka ta ku wuce"

"A taka ni fa ka ce? Saboda ba ka da asara.?

Maeesha ta faɗa cikin hargowa shi ko kamar bai ji ta ba ya shige ɗakin Inna wacce ke salla ta kosa ta Idar kada Baban inna ya ƙara jawo mata wata masifar, Maeesha bakin ciki ya rufe ta sai kawai ta saka kuka tana faɗin an takura mata ita da gidan Mijinta ba ta da halin sararawa Walida na gefe tana yar eariya daman matar nan ta gama cika mata ciki da iskancin ta a cikin gidan nan saboda ita Bintu ta daina zuwa gidan in ta ga abun magana sai ta yi mgana Kuma tana mgana sai a fara hayaniya Ita kuma Inna yar zaman Lafiya ce ita ta ce in fitina ke kawo ta itama ta zauni gidanta.
Maeesha ta yi ta kumfar baki tana tunanin Magajiya za ta fito amman shuru ita kuma Walida sai ta tafa hannu kafin ta ce"Sorry fa, ko shi Yaya Saddiqun ba zai iya da Yayanmu ba ballantana ke karamar alhaki."
Da haka itama ta nufeta gadan gadan kamar za ta murje mata hannu ya sa da sauri ta mike tsaye Walida ta shige É—akin Inna tana faÉ—in" Ashe karyan tsiya kike yi."
Fuu Maeesha ta koma É—aki tana kuka ta kira Saddiqu tana gaya masa karya da gaskiya har ta na faÉ—in Aji ya saka yakalmi ya taka ta kuma da gangan.
Shi kuma cikin Kumfar baki ya ce mata ai ya Kusa dawowa zai yi sharia da wanda ya taɓa masa mata daman ai ya na jin hauahin warning ɗin da ya saka Auwalu ya kira shi ya yi masa to wai shi da me ya ke takama ne?

A ɗakin Inna ko ta na sallame sallah cikin ɓacin rai ta kalli Mansoor kafin ta ce"Ba na son fitina. Ba na so ina zaune lafiya ba za ka jawomin wata fitinar ba, in kai ba ka san darajan matar ka ba, wasu sun sani kuma da gaskiyanta gidan mijinta ne a barta ta yi abin da ta ga dama mana."
Lokacin ya na wasa da Junoir ne wanda tun shogiwarsa a she bai yi barci ba ya naÉ—e masa. Sai ya kasa mgana domin kamar gori ne Inna ta yi masa.
Walida ce ta tura baki kafin ta ce"Shikenan Inna sai a barta ta rika mana abin da ta ga dama."
A fusace Inna ta ce"Sai me? Ai wuri ta samu É—an da ka haifa ma bai ji mganarka ba sai wani can ne za ka damu kanka domin ka yi masa mgana bai ji ba."
Yadda Inna Meri ke mgana ne ya sa ya san ranta ya ɓaci kai tsaye ya ce"Ki yi hakuri inna." Sai kawai ya miƙe ya na faɗin"Inna ki ba ni Junior na tafi da shi wajena ya kwana."
Wani kallo mai kama da harara Inna ta sakar masa kafin ta kalli Walida lokaci ɗaya tana faɗin"Ke karɓe shi, "
Walida ta yi shuru kafin ta karisa za ta karɓeshi shi kuma ya makale masa sai ta Juya tana faɗin" Inna ko za ki bari ya tafi da shi ne, duba fa ki gani baya son zuwa."
Inna ba ta sake mgana ba ta miƙe ta warce Junoir a hannun Babban Inna yaron ko ya fashe da kuka Inna ta mikama Walida shi tana faɗin ta kai shi ciki ya kwanta.
Ta kalli Manaoor da ya yi kasaƙe kawai yana na kallon Inna komawa ta yi ta zauna lokaci ɗaya tana faɗin" Mu kwana lafiya."

Takaici ya kume shi cikin É—an jin haushi ya ce"Inna É—an ÆŠan uwane fa?
Inna kai tsaye ta ce"E fa! Amman ai ba É—anka ba ne ko ? In ka ji haushi ka haifi naka sai ka rika kwana da su."
Har ya dawo gidansa in ya tuna kalaman Inna sai ya ji kamar ya yi kuka wai shi Inna ke yi ma gorin Mata da haihuwa, takaici ya sa a daran ya Kira Mu'azzam y na gayamasa shi kuma ya nuna bai ji daÉ—i ba.
Sai kawai Aji ya ce" Amman ba komai, ta kwantar da hankalinta sai ta gaji da ɗaukan Ƴaƴa na"
Mu'azzan sai ya ji ya ba shi tausayi ya kuma san Inna ta yi masa hakane Saboda ya ji haushi ya gyara abin da ya ɓata kuma kamar hakan ya yi tasiri daga baya shima ya zauna yana tunanin shekaru sun tura ya kamata ace shima yanzu ya wuce wannan matsayin tunda har Inna ta fara masa gorin mata da haihuwa to nan gaba bai kuma san wa zai masa gori ba, ya fi su fa bukatar matarsa akwai abubuwan da suka faru ne suke danne wannan bukatar ta shi amman cikin ikon Allah da shawarwarin Nasir tun kwanaki ya fara yaƙi da abin d ke ransa kuma Alhandulillah yana jin abun na raguwa.

Duk iya yadda ya so ya share Mimi sai ta neme shi amman ba ta neme shi ba Sai ya ji ya kasa hakuri ana neman cin wajen wata ɗaya sai ya fara jin tsoro kada fa ya yi sakacin da zai ƙara jefa rayuwarsa cikin yarari a karo na biyu.
Ba shi da wani abokin shawara sai Mu'azzam Shi ya kira ya na ce masa" Mu'azzam kana ganin na bi Mimi Abuja ba matsala.?
Mu'azzam na mirmishi ya ce"Me zai hana? Ba wata matsala, ka kirata in ba ta É—auka ba ka tura mata sakon za ka zo sai ku zauna ku yi mgana." Kamar wani yaro sai ya ce ma Mu'azzam Toh, Sai yayan na shi ya ba shi tausayi yasan yadda ya tsani garin nan amman ga shi yau zai koma kuma a kan dalilan nan guda É—aya wanda saboda shi ya je a karon farko a wannan karon ma saboda shi zai koma.

"Don Allah Yaya Mansoor kada ka ce za ka mata yi faɗa,  ka lallasheta tunda dai kai ne mai laifi."

"Uhm!

Kawai ya ce daga nan bai ƙara mgana ba Saboda a lokacin yana tunanin ya je ko kuma kar ya je,  amman ya bi shawaran Mu'azzam ya ƙara Sauke kai ya kira Mimi amman matar nan ba ta ɗauka ba sai ya tura mata sakon ta tura mishi adireshin gidansu zai zo su yi mgana.

Lokacin da ta ga sakon shi matuka ta sha mamaki, wani gidan y ke nufi? gidan da ya ce Allah ya yi masa tsari ya ƙara takawa,  ba ta yi gaggawan tura masa sai da ta kira Rukky ta sanar da ita, ita kuma tana dariya ta ce" Na fahimci ba ma zai yi mana wahalan kamuwa ba, tura masa kada ki sake ki gaya masa wani abu."
Chapter 25 · 0% Book details