← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 93

Sashe 40

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan tafiyarsu Khadi ta kalli Mimi lokaci É—aya tana faÉ—in"Ke da aka ce kin buga yaji da kukan sai kin kashe aure, sai kuma a ganki kina bin gidajen dangin Miji?
Mimi ta kalleta kawai amman ba ta yi mgana ba Sai Khadi ta fara dariya tana faÉ—in" Wai ni ki gaya min me ya yi miki ne da zafi haka? Aji ne fa Ajin nan da kike matukar so? Shege namiji É—an Babansa ya kunsa miki kenan?
Tashi kawai Mimi ta yi ta ba ta waje saboda ta san tana dukan ruwan cikinta ne ta ji labari nan ta barta da Jawahir tana ta mganganu ita kuma sai dai ta yi mata mirmishi.
Har Dr. da ya dawo sai da Khadi ta ce masa" ƙanwarka an ce ta yi yaji amman kuma sai ga ta ta na bin gidan ƙanin mijinta.*
Dariya ya yi kafin ya ce"Bacin rai ne amman yanzu mun huce za mu koma."
Haka Khadi ta rika tsuntsura dariya tana Faɗin" To daman ita an gayamata soyayya ta na dauwamana, ku gaya mata kowa ma hakuri yake yi a gidan auran shi. Duk da ban so auran su ba amman daga baya na saki, duk lalacewar aure gwara auran da rabuwar wani lokacin, kawai ta cigaba da hakuri daman an ce baƙin mutum akwai faɗin rai sai kin ninka haƙurin ki."
Ƙala Mimi ba ta ce mata ba. Sai Dr ne ke kare ma Mimi yana faɗin har nan Aji ya zo biko kuma dai shi kam ya ba shi bikon Mimi.

Madiha ba ta zo ba sai ranar suna, Asma'u ma Mommy ta turo ta dag anan za ta tsaya gida ta yi hutu, Madiha ba ta san an daidaita har Mimi ta sauko ba sai da ta ga zuwan Hibba ana cewa matar ƙanin Mijin Mimi sai kuma da ta ganta sai ta tuna ta taɓa ganinta a wannan gidan da aka kai Mimi, Tun anan ta nuna ba ta ji daɗi ba Mimi ba ta ma san tana yi ba ta riƙa ina ta saka da bakuwarta Hibba ta na nan har dare har riga ta kawo ma Bby Girl da ta ci sunan Mahaifiyar Jawahir mai suna Hadiza, Sai bayan da Mu'azzam ya zo ya ɗauketa ne da daddare suna ɗakin Dr su huɗun gabaɗaya Madiha ta tada zencen da cewa"Ke Mimi me ya haɗa ki da dangi wancan matsiyacin?
Ba Mimi kaɗai ba harta Khadi sai ta ji wani iri, Dr ya kalleta cikin ɓacin rai kafin ya ce" Haba Madiha, ko an rabu ai bai kamata ki kira shi da wannan sunan ba, Ballantana har gobe a matsayin mijin Mimi yake."

Madiha cikin halin ko in kula, ta ce"To sai me? Ai sai ya sake ta wlh in ya yi taurin kai a maka shi a kotu,"
Khadi ta yi Saurin cewa"Ke, to tana son mijinta, yanzu hakama ya je ya samu Daddy kuma ya ce ya ba shi bikon ta, tana komawa Gombe sai shirin tarewa daman Yajin barazana ta yi ko Mimin Abi?
Mimi ta kasa mgana Idanuwanta har sun kawo kwallah, Dr ne ya tsawarta ma Madiha da cewa" Ki daina shiga hurumin da ba na ki ba don Allah, Mimi ba za ta ji daÉ—i ba."
Madiha ta kalle su cikin mamaki kafin ta ce" Mi ye illar mgana ta? Na ga ita da kanta ta ce ba ta son auran domin na taimaka mata komai ya kare laifi ne?
Sai kawai Mmi ta miƙe tana kallon Dr kafin tace" Dr gobe ko jibi zam koma Gombe."
Ta na gama faÉ—in haka ta bar musu É—akin.
Khadi ta kai duban ta kan Madiha kafin ta ce"Gaskiya Sisto ba ki kyauta ba, kamar ni ne fa ki zagi Muhammad"
Madiha ta taɓe baki kafin ta ce"Muhammad dabam wannan talakan dabam, ki daina ma haɗa su."
Khadi na dariya shi kuma Dr ya haÉ—e rai yana mata faÉ—an abin da ta yi na ta kyauta ba sai kawai ta ce"Au don nace matsiya ci? Karya na yi? To shike nan na cire bakina."
Ba za ta daina ba halin su ɗaya da Abi shigen kafiya aiko har washegari Mimi ba ta ƙara yi ma Madiha mgana ba sai ta nemi ma jirgin Komawa Gombe ta samu na yamma.

Dr bai hana ta tafiya ba, an kulla mata Naman suna da yaji na ta da na Hajiya, Jirgin karfe biyar ta bi zuwa Gombe Dr. da Khadi su ka kaita filin Jirgi sai da za ta tafi sannan ta yi ma Madiha sallama ta amsa a daƙune ita gani take yi ina laifi domin ta faɗi gaskiya.
Sai dai Hajiya ta ga Mimi sarkin Ya ji kamar daga sama kuma ba domin mganar Daddy ba, hutun ta ya ƙare ya zama dole ta dawo.
Hajiya ta yi murna Baaba Uwani ta ce daman gidan shuru da ba ta nan, ta kira Daddy ta ce masa ta dawo kila anan Mama taji ta gayama Jaheed daman tun da ya ji ta Dawo gida ya addabeta da waya yana gaya mata yana kan bakan shi ta ce ba shi ma da hankali da auranta ai ba ya mutu ba ne.
Sai da ya ji ta dawo wai zai biyo jirgi gobe su yi mgana. Daman a gidan Madiha zuwan sa uku wajenta yana mata magiya ta faɗa masa Mijinta bai saketa ba amman ya na ce wai zai taya ta karɓan sakin daman ai ba su da ce da juna ba, shi a tunanin shi Madiha na goyon bayan shi, shike nan ya same ta ya gama. Tun da ya ce mata zai zo washegari ta ce masa ka da ya zo, domin ita ta san abin da take yi da auranta ba za ta zo tana haɗuwa da shi ba.

Washegari hutawa ta yi a gida, shi kuma Jaheed bai samu dama a wajen aiki ba Shi ya sa bai zo ba, Aji kuma Daddy da kansa ya kira shi ya faɗa masa Mimi ta dawo daman ranar sun karɓi lambar wayar juna sai ya ce zai shigo gidan ko a ranar da daddare ko washegari da yammah.
Bai samu zuwa a daran ba sai washegari bayan la'sar daga gida yake ya je ya gaida Inna sai da ta kara masa mganan Mimi ya ce daga nan wajen ta zai nufa.
A motarsa ya je yana sanye da ƙananun kaya, megadi na buɗe masa get ya shiga motarsa Mimi na fitowa tare da Rukky da ta zo ta rakota sun tsaya suna mgana sai ganin Aji suka yi ya fito daga motarsa duk da ya saka hula P. cap ta rufe rabin fuskar shi ba zai hana taƙi gane shi ba.

*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3009*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

Mimi na sanye da wata doguwar riga amman rigar mai roba ce ta ɗan kama mata jiki kaɗan. Sai ta saka mayafin rigar a saman kanta Rukky ma baƙar Abaya ne a jikinta amman ita sai ta saka ƙaramin hijabi a sama sannan har da Igiyan ID card ɗin ta dake maƙale a saman wuyanta, Saboda daga wajen aiki ta biyo wajen Mimi.

  Dukkansu yana fitowa daga mota suka zuba masa ido. Shi kuma ya fito kenan sai aka kira wayarsa sai ya tsaya yana amsa wayar, Mimi ta ƙura masa ido kamar yadda shima ya ƙe kare mata kallo daga kasan hulaarsa wato ita wani ja ma ta ƙara da haske da kiba shi kuma ya na nan ta barshi yana faman wahala, ita kuma sai ta ga ya ƙara mata tsawo saboda ta daɗe ba ta gan shi ba, har wani sanyi sanyi take ji a ƙasan ranta, ta shagala da kallonsa ba ta san Rukky na kiran sunanta ba sai da ta ji ta dafa kafaɗanta.

"Mimi.."

  Sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta maida kallonta kan Rukky lokaci ɗaya tana faɗin" Sorry me kika ce?
Rukky ta balla mata harara kafin ta juya ta na kallon Aji ya gama wayar yana tahowa wajensu da sauri ta matsa kusa da Mimi lokaci ɗaya tana faɗin" Dilla behave you self." Duk da bai ji abin da ta faɗa ba amman ai ya ga bakinta na motsi, yana jin sau ɗaya ya taɓa ganin Rukky amman yana ganinta sai ya ganeta ita ce wannan kawar ta Mimi wacce ba ta masa ba munafuka ce, illau ga shi yau ya ga shaida sai wani kyfta ido ta ke yi alamun ba ta da gaskiya.
Shi kuma cikin yanayin takunsa na masu karfi da Kuzari ya ƙarisa gabansu duka hannayensa zube a cikin aljihun wandonsa.

  Sai da ya zo gaban Mimi Sannan ya tsaya ya kuma saka hannu ya ɗan daga gularsa sama yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa ya juya yana kallon megadi na zaune a mazauninsa da radion sa ya na ji. Sannan ya juya ya na kallon Mimi Sai dai ba fara'a ko kaɗan a fuskarsa sannan Rukky dake wajen ko kallonta ma bai yi ba, sai ma ya yi kamar bai san da wanzuwar a wajen ba.

"Haka kike fitowa waje ba hijabi ba mayafi Mimi.?
Chapter 40 · 0% Book details