← Book details Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 93

Sashe 33

Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Inna Meri na tsaye ta kasa zama idanuwanta sun ciko da hqwaye, Mansoor ya zo ya riƙe ta yana faɗin"Inna ki zauna mana, an juma za'a kawo sabbin kujeru da sauram kayan amfani in sha Allahu."
Inna kamar ta yi kuka ta ce"Baban Inna wamnan gidan ya yi mana girma da haya ka kama min"
Cikin Mamaki ya ce"Haya kuma Inna? Wani irin haya kuma?  Ina da gida kuma sai ace mahaifiyata sai na ne man mata haya?
Inna na rike hannunsa ta ce" Kai fa? Ina Binta za ta zauna in  ta dawo?.
Mirmishi ya yi mata sannan ya kamata ta zauna saman Cafet shi kuma ya zauna a gabanta yana faÉ—in" Inna ina da kuÉ—in da zan iya siyama Mimi wani gidan ta zauna ko na gina mata wani, amman daga yau wannan gidan ya zama naki halas malak Inna."
Inna Meri ta fashe da kuka tana faɗin" Allah Sarki haihuwa mai rana Na gode kwarai Allah ya yi maka albarka, don Allah Baban Inna zan roƙe ka wata alfarma."
Ta faɗa tana riko Hannuwansa duka biyun da sauri ya ce"Faɗi koma menene ni kuma Zan yi miki  shi in har bai gagareni ba."
Inna na hawaye ta ce"Kukan farimciki nake yi Baban Inma ba na baƙin ciki ba. domin haihuwa ta min rana Ubangiji ya gama min komai. Ni kamin komai wlh na gode amman ina so kaima  na ga ka samu Farinciki Don allah ka manta komai ka je ku daidaita da matarka ka dawo da ita ku zauna domin kaima ka samu farinciki ka tara zuru'an da za ka yi alfahari da su sannan ka samu rayuwa mai inganci Baban Inna"

  Inna ta gama faɗa tana hawaye  Sai Mansoor ya share mata hawaye kafin ya ce"Ina sha Allahu Inna, ba saboda mganarki ba ni da kaina nake son na dawo da Mimi in sha Allahu."
Haka Inna ta ji daÉ—i ta rika saka masa albarka tana hawaye.
Su Bintu ya kira yac e ta bishi su je gida su kwaso kayan sawan su, Inna na zaune ta ce" Har da ma sauran kayan amfanin ai ba sai an siya wasu ba."
Shi kuma ya ce a'a ta bar musu gidan da abib da ke ciki kayan sawan su kawai sai abin da suke so za su É—auko Inna ba ta da abin cewa sai fatan alheri kawai.

  Daman kuma tuni Bintu ta kira su Yaya Amina ta gaya musu abin da ya faru mamaki ya kama su suka ce ga su nan zuwa, Da Bintu kaɗai a ka koma can gidan ita ta haɗo duka kayan sawan su Inna da duk abib da za su bukata har da kayan amfanin gida su mopper da botikai da sauran su sannan ta saka key ta kulle ɗakin, daidai sai ga Yaya Halima daman sun yi waya ta ce tana gidan ta zo ɗaukan kaya gidan shuru ba motsin kowa kamar ba nutane. Bayan mota sai da ya cika da kaya da booth, sai Yaya Halima ta bi Mansoor ita kuma Bintu ta hau adaidata suka isa can gidan Yaya Halima ta samu Inna na ta sharan kwallah ta fara mgana sai ta ce ke ni kukan daɗi nake yi Halima sai dariya kuma gabadayan su nan da nan suka mike suka fara gyaran gidan ba daɗewa sai ga Yaya Amina ma ta ƙariso.
Mansoor kuma ya ce bari ya je ya dawo Junior na ta murna ya ga irin gidansu na Kano.

  Tun da mansoor ya tafi sai bayan la'asar ya dawo ya je ya yi wanka ne ya sauya kaya ko da ya dawo ma sun yi dubaran yin girki Tunda Bintu ta taho da kayan abinci da gas tunda daman Inna na da shi ita ce ba ta cika amfani da shi ba. Sai ya ji daɗi daman yana can ya na tunaninsu sun yi waya da Mu'azzam ne wanda ya ce Auwalu ya kira shi ya faɗa masa ga abib da ke faruwa sun yi mgana sabbin kayan gidan da za'a saka ma Inna suna gama waya Mu'azzam ya tura ma masa 100k yace a kara da shi ai ko ya sha faɗaa domin Mansoor ya ce shi bai ce ya kawo wani abu ba, shi kuma ya ce ai Inna mamansu ce gaɓadaya shima ya na neman albarka sai bakin Mansoor ɗin ya mutu.

  Nan ya ce su Yaya Halima su zauna su rubuta duk abib da za su bukata na kayan amfani gida oabulai kayan gadaje da Kujeru kuma ya ce har da su duk su je su zaɓo Atm dinsa na babban bankin sa First  Bank ya damka musu su kuma su ka ce tunda yamma ta yi sai da safe za su yi sammakon fita  Gabda mangariba ya bar gidan shi kanshi ya samu natsuwa tunda nan yaci abincin rana Jallop ɗin shinkafar da suka dafa da daddare ma Bintu na dafa shinkafa da miya ya ce su ijiye masa zai dawo tuni sun gyara gidan gabaɗaya sun tsabtace komai kayan Inna sun samu matsugunni cikin wardrope Walida kuma tuni ta manta da duka ta ware tana murna ita abin daɗinta wannan kayattacen tiolet na cikin ɗakin da aka ce nan za ta zauna ga Wardrpoe ɗin bango daman tun lokacin ginin aka gina da shi sai dai aka saka masa Kofifi kawai.

  Bintu a nan ta kwana tunda ta kira Bashher ta gaya masa Inna ta sauya gida za ta tsaya ta taya su gyare gyare. Da kan shi ma ta yi masa kwatance ya zo ya kawo ma ta su Hussaini tunda abokiyar zamanta ba ta nan ta na gidansu ana suna, ya zo ya ga gida shima ya yi mamaki, amman jin gidan Babban Yaya ne sai bai yi mamaki ba.
Yaya Halima da Yaya Amima gidajen su suka koma su ka kwana sai washegari suka dawo da sassafe suka tafi kasuwa su uku tare da Bintu tun safe sai yamma a kamfanin da suka siya kayan su suka basu motar da ta É—auko musu kayan da kuma ma'aikatan su Kafin dare duka an haÉ—a gadajen, falom ma tuni an zagaye shi da sabbin kujeru masu kyau da yarari, har da labulayan suka siya da karafan su ma'aikatan suka haÉ—a musu komai tunda an riga daman an É—inka su a kirchen ma sun yi ma Inna É—aki domin har kololi sabbi suka siya mata da sauran kayan amfani kitchen da na tiolet gida dai ya fito kamar gidan wata amarya yana kuma tashn shin kamshi tun da daman sun siyo turarukan tsinke da na rushi.

  Gadon Inna shine 6by7,Na Walida kuma karami ne 6,by 6 ne. Gida ya fito ras da shi sai son barka, Inna Meri duk ta damu wai shi Baban Inna ina zai riƙa kwana? Ya
na dariya ya ce"Inna ina da wajen kwana ga Camp É—in mu, sannan ga É—aki na nan in ina son kwana tare daku zan zo na yi kwanciyata sannan daga yau mun zama family daya ko da Mu'azzam ya zo da iyalansa waje É—aya za mu rika kwana a matsayin Ahali É—aya in sha Allahu."
Sai Inna ta jinjina kai domin itama ta ji matukar É—adi ganin iyalanta a waje É—aya.

  Maƙota na ta zuwa ganin gida suna murna Mariya kwananta biyu sannan ta koma gida ta labartama Magajiya gidan Inna da yadda aka saka komai sabo, Bintu ce da gayya ta ke yi ma jama'a kwatance ana zuwa ana ta yabo da cewa Inna Meri ta samu muhalli mai kyau in aka ce waya siya mata gidan? sai ace babban ɗanta mana sai dai ki ji ana tambayan shi ko aikin me ya ke yi haka? sai ace  ai Babba ne a ƙwallon kafa, Jummai ta zo itama ta ga waje ita da su Gaje Magajiya dai da zuwaira bakin ciki bai bar su ba hatta su Baba Sani sun zo gidan nan da Auwalu sai ga su zaune a falon Inna suna hira sun ci sun sha wai yau sune ke yi ma Inna hira suna dariya, hasken wuta ko'ina da yake ana barin wuta sannan kuma Mansoor ya kira an duba za'a saka ma Inna Sola a gidan, Baba Ɗanjuma kuma ya zo ya yi kwanaki biyun sa kamar kada ya koma gidan wajen Magajiya da aka barta daga ita sai halinta ba mai lekowa gidan daga nan ta gane duk jama'ar na Meri ne ita kuma Maeesha gida iyayenta suka ce a maidata ta haihu acan gida daga magajiya sai halinta Mariya ma guduwa take yi gidan Yaya Zuwaira ko gidan su Walida.

  Kayan ɗakin Inna na da kuwa su Bintu suka raba a tsakaninau Kujerun da gadon Yaya Amina ta ɗauka tunda jinyar mijinta a lokacin ya sa duk ta saida kayan ɗakin ta Cafet kuma da sauran kayan amfani Yaya Halima ta ɗauka ta kuma ɗauki kula da sauran filet filet da yake komai na Inna sabbi ne Mansoor ya sauya mata sannan Mu'azzam haka, kamar kayan ɗakin wata Amarya sakin wawa Fridge ne kaɗai suka kaima Inna can gidan tunda daman ba su siya ba suka ce nata bai yi komai ba. Kaf suka kwashe koma ko roba ba su bari ba Sai ma datti da suka bari Bintu ce daman ta je ta rufe ɗakin ta leka ɗakin Magajiya ta ba ta key ɗin ta ce ta ba ma Baba in ya dawo ga shashen nan gabaɗaya Inna ta bar musu in ta ga dama ta koma ɗakin Innar gabaɗaya wannan dai ya rage nata. Sai ga Magajiya shuru ta kasa maida mgana da Baba Ɗanjuma ya dawo ya ba shi makullin shima cewa ya yi ta riƙe ta ba ma Saddiqu ya haɗa ma Matarsa duka ta zauna a ciki Meri ce kuma ta samu wani sauyim alheri, Ita dai ba ta je ba amman har Vadeo gidan Mariya ta ɗauko a waya ta numa mata tabbas Meri ta samu kyakyawan sauyi.
Chapter 33 · 0% Book details