Sashe 23
Idan An Ciza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai Kawai Mu'azzam ya ce"Ina da shawara me zai hana in ka koma ka nemi Babanta Alhaji Hamza? Tsohon Sanata tunda shine Waliyinta?
Aji ya yi shuru kafin ya ce"Da na ce ba zan je ba, amman yanzu ai ba ni da zaɓi. Zan je in sha Allahu da zaran na koma."
Sun É—an tattauna Mu'azzam na kara gaya masa in ya je ya kwantar da kai tunda sulhu ya ke so, Bayan nan suka gangaro kan mganar gida Mu'azzam na faÉ—in Bintu ta gaya mai Inna wulakanci take kwasa tun bayan dawowar Matar Saddiqu bangarenta.
Aji ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce"Ka san Allah na kusa ɗauke Inna daga gidan, kawai dai ba na so Baba ya ga na nuna masa shi ya gaza ne."
Mu'azzam ya yi saurin cewa" Ni ma na yi wannan tunanin. Tunda Dai Magajiya ta fi ƙarfin Baba ba ya iya tsawarta mata, Inna kuma kasan halinta ko dukanta za su yi ba za ta taɓa mgana ba."
Mansoor ya koma ya jingina da Kujeren da ya ke zaune kafin ya ce" Kar dai a yi wani abin da zai ɓata min rai, zan ɗauke Inna gaskiya a wannan gidan."
Mu'azzam ya ce"Ko Yaya Amina abin da ta ce kenan gidan duk ba daÉ—i."
Sun cigaba da tattaunawa har kan batun su Walida Mu'azzam ya ce hakan ya yi dai dai, Aji yac e da zaran ya koma zai nemi Auwalu kan mganar ita Mariya.
Nan su ka shantake sai bayan oa'asar sannan suka ɗumguma zuwa gidan Mu'azzam d ke BUK old site. Sai dai Hibba ta ga Yaya Mansoor kamar daga sama itama bakinta kamar zai yage, faɗi take yi" Lalle muna da babba baƙo, sannu da zuwa Yaya Mansoor"
Ya amsa mata cikin sakewa abincin da ta yi sun fi kala huÉ— nan suka baje suka ci suka sha suna ta hira kamar kada su rabu, Mu'azzam ya kira Inna ya sanar da ita ga shi ga Baban Inna itama kanta ta yi mamaki ta ce ya kyauta.
Sun É—auka ma ko kwana zai yi ya ce ba zai kwana ba. Sanin halin shi ya sa Mu'azzam bai matsa masa ba wajen shidda da rabi ya kai shi tasha ya hau mota sai da suka tashi ya dawo gida tafiyar dare suka yi sai wajen sha biyu ya iso Gombe, bai je gidansa ba a Camp ya kwana kuma evening Traning suke dashi shi ya sa tun bayan sallar asuba ya kwanta barci ya kwashe shi. Bai ta shi ba sai da ya ji ana ta kiran wayar sa yana tashi ya Duba sai ga inna ta kira shi Bintu ma haka.
Sai ya bi bayan kiran yana duba Lokaci goma saura na safe,
Wayar Inna ta na ƙara ba'a ɗauka ba, yana cikin neman Bintu sai ga kiranta sai ya ɗauƙa da sauti gabansa na faɗuwa yana tunanin ba lafiya.
Kuka ya ji ta na yi masa, da sauri ya miƙe ya na laluban rigarsa.
Cikin fargaba ya ce"Bintu me ya faru ne?
"FaÉ—a ake yi a gida saboda Matar Saddiqu ta dagi junior har sai da ta ture shi ya fasa goshi, shi ne shi ne Walida ta yi magana Meesha ta ja ta da faÉ—a suka kama Kokuwa sai ta faÉ—i, Saddiqu na zuwa kawai ya rufe Walida da duka Inna ta zo ta hana ya tureta har sai da hannunta ya goce."
Bintu ta faɗa ta na shesshekan kuka, Aji ya ji wani abu ya taso masa a ƙasan zuciyarsa. cikin maimaitawa ya ce"Ta goce? Ita Inna ce ya gotar don uban shi? Lalle ne ma."
Haka kawai ya ce ya kashe wayar daman ya saka riga kawai sai ya zura takalmi ya É—auki key É—in mota tabbas yau Saddiqu zai fahimci yana cin darajan mai daraja ne amman tunda har tura ta kai bango yau za'a buga final É—in.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3005*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Cikin girmamawa suka gaisa da Hajiya, Ita kuma ta amsa masa cikin sakewa kamar wani abu ma bai faru ba. Har ta na masa irin zolayan da ta saba yi masa, tunda har ga Allah ba ta san da zuwan sa ba tunda Binta ba ta kira ta ba.
Kallon sa ta yi kansa na duke lokaci É—aya tana faÉ—in" Ka makara da zuwa biko, Binta ba ta na nan shekaran jiya can ta tafi can Abuja wajen Murja. Hala ba ku yi waya ba ne?
Kansa na kass a cikin zuciyarsa ya maimaita" Abuja?
Lalle ne ma Mimi ta maida shi wani sakarai ya ga alama akwai kasawa ma ya ce ma Hajiya sun yi magana a waya shi ya sa kawai sai ya ce mata ya kira wayar ta bai same ta ba.
Hajiya ta muskuta kafin ta ce"Ai ko ba ta nan, amman tunda biko ka zo kuma ta karfe ta gudu, me zai hana ni mu daidaita? Ta fada cikin Sigar zolaya yar dariya ya yi yana shafa kansa kafin ya ce" Haka za'a yi Hajiya."
Shuru na wani lokaci, Hajiya ce ma take É—an Jansa da hira tana tambayan shi aiki da mutanen gida.
Ya amsa mata da duk suna lafiya kai tsaye ta ce" Ka gaida min da Meri dakyau dakyau."
Ya amsa da In sha Allahu, ko ruwan da aka kawo masa bai sha ba ya yi ma Hajiya Sallama da cewa zai koma.
"To ko za ka ƙarisa gidan Babanta Hamza ne. Daman yana neman ka."
Hajiya ta ce tana kallonsa lokacin da ya miƙe shi kuma ba ya son wata doguwar mgana sai kawai yace mata Toh, amman shi ya san ba zai je ba wato ya kai kansa kenan tunda daman ana jiran shi.
Kuɗi ya ijiye ma Hajiya a nan ƙasa ta saka hannu ta ɗauka tana faɗin" Ai shike nan kana bikon dani tunda ka fara toshi, Na gode kwarai Allah ya ƙara ma rayuwa albarka."
Ya amsa mata da Amin Amin sannan ya yi mata sallama ya bar falon ta bi shi da kallo, Binta ta cika taurin kai sai da ta hana ta tafiyar nan amman ta haɗa ta da ubanta ya ce a ƙyaleta ta je ta gaida mahaifyarta ga shi megidanta ya zo ba ta nan, Baaba Uwani Hajiya ta kira ta Umarce ta da ta Dauko mata Wayarta a cikin ɗakinta.
Bayan ta kawo mata sai ta ce ta kira mata Binta tunda Baaba Uwani ta iya karatun Hausa ita ta nemo lambar Mimi ta kira ta sqnnan ta miƙa ma Hajiya tana ɗauka ta fara faɗin" Hajiya ta, kin yi kewata ne?
Hajiya ta ce" Kin san cewa yanzu mijin ki ya bar gidan nan yana neman ki?
Sai Mimi ta gyara kwanciyarta kafin ta ce" Wa? Aji? Ban sani ba saboda bai kirani ba."
Ta yi ma Hajiya ƙarya. Sai ita kuma Hajiyar ta ce"To ya zo, na sanar da shi bakya nan amman na ce ya karisa wajen babanki ke kuma sai ki yi kokari ki dawo a daidaita ki koma gidan Mijin ki."
Ba gaddama ta amsa ma Hajiya saboda ko ta ce za ta yi gaddama Hajiya ba za ta gane in da ta dosa ba ne.
Bayan sun gama waya da Hajiya ita kaɗai take ta Mirmishi, Kaɗan ya gani yanzu ma aka fara wasan ba ɗaɗewa ko sai ga kiran shi ya sake shigo mata wannan karon ba ta kashe ba barin shi ta yi har sai da ta katse, wani kiran ya ƙara shigowa ya katse har sau uku bayan mintina kaɗan sai ga saƙon sa.
"Kin raina ni ko Mimi? Kina jin daÉ—in kin yi wasa da hankalina ko? to ya yi miki kyau amman ina so ki sani ki sauke wannan abin da da ki ka É—auka na tunanin za ki wahalar da Aji ko ki yi ramako a kaina, Never zuwan ma da kika na yi saboda inna da Baba sun matsa sai na zo na dawo dake gida, in kin ga dama daga nan Abujan ki ci gaba kin ji ko."
Daga ganin yanayin saƙon ta san ranshi ne ya ɓaci, tana yar dariya bayan ta karanta wato zai fake da Baba da Inna shi a dole kada a hango ya gaza, a lokacin ba ta yi tunanin maida masa da martani ba sai bayan kamar awa ɗaya tun da barin ɗakin ta yi zuwa falo in da Asma'u ke kallo Mommy kuma tana ɗakin ta tana faman duba takardu sai wajen goma saura ta Daawo ɗakinta ta yi wanka ta kuma yi shirin kwanciya sai da ta kwanta sannan ta jawo wayarta ta tura masa saƙo.
"To shike nan zan ci gaba kamar yadda ka ce."