← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 40

Sashe 8

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'aukan jakarta tayi hankalin ta duk a tashe, batasan ina zata k'ara had'uwa da Issam ba, batasan ina neh asalin gidan su yake ba. Jin k'aran horn yadawo da ita daga dogon tunanin data fad'a. Abokin Aliyu neh ya fito a motar yana mata murmushi yace
"Sister nah ina zuwa haka"
"Hmm gida"
"Shigo toh na kaiki" shiga kawai tayi dan ita hankalin ta sam ma baya jikin ta, surutu yake mata a hanya wanda batasan ma yanayi ba. Ya tambaye number wayar ta ta mik'a masa wayar kawai ya latsa number shi yakira wayan shi yayi saving. Ya kaita har kofan gidan su ta sauka ba tareda tace masa tagode ba. Lokacin daidai Aliyu shima ya dawo gida kenan. Wani mugun kallo Aliyu ya watsa mata take tashiga cikin gida. D'akin ta direct tashiga tayi wanka tayi alwala tayi sallah. Fashewa da kuka tayi tana meh tuna mahaifin ta, mahaifin su yana sonsu kamar ransa. Baya barin Mum tamusu fad'a koh kad'an. Duk da sangantar dasu da yakeyi haka baisa sun lalace ba. Bazata tab'a mantawa da last maganan da sukayi da mahaifinta ba a daren dasu Issam suka shigo gidan _idan kin samu namiji meh hankali wanda kike sonsa yake sonki toh ki gabatardashi koh da bashi da koh sisi, bazan miki auren dole ba tunda bakison yaron marigayi abokinah duk da nayi alkawarin zan had'a ku aure nayi watsi da alkawarin nan sabida farin cikin ki shineh nawa_
Kuka ta fashe dashi tana dana sanin kin auren yaron abokin mahaifinta wanda batasanshi ba bai santa ba. Ringing na wayan tane ya dawo da ita dogon thinking data fad'a, rejecting tayi dan a halin yanxu she ain't in the mood of receiving any call. Same number neh yake sake kiranta, dogon tsaki taja ta d'auka wayar ta danna loudspeaker ba tareda tace komai ba sabida new number ce
"Assalamu Alaykum Beauty" muryan namiji but it seems familiar to her.
"Wa'alaykum Salaam" ta amsa k'asa k'asa
"Queen of beauty har kin fara bacci neh"
"Who is on the line?"
"General Suleiman Abubakar" sai yanxu ta ganeh abokin Yaya Aliyu neh
"Ohh sorry ina yini"
"Lafia kalau Beauty, daman I just call to say hi"
"Thank you"
"Ba komai, kiyi saving number nah"
"In Shaa Allah"
"Bye" ya katse wayan. Tashiwa tayi akan gado dan yunwa sosai takeji, zata wuce kitchen Aliyu yakira ta yana zaune a parlour kuma sai ta wuce parlor kan tashiga kitchen. Yace
"Ke zonan" kallon sa take ba tareda tayi motsi daga inda take ba, tsawa ya daka mata yace
"Ba dake nake magana baneh"
Tafiyan ta ahankali take har ta iso cikin parlour ta nema kujera ta zauna tayi crossing leg. Duk kallon ta suke daga Aliyun har Meena. Yace
"Sauke kafan nan" sanda tayi kusan secs goma kan ta sauke kafan. Aliyu yace
"Uban mei yahad'aki da S.A? Ina kuka had'u?"
"S.A kuma ni ban sanshi ba" dunkule ya mata yace
"Kinci gidan ku, aboki nah da yayi dropping naki d'azu"
"Ohhh you mean Suleiman?"
"Shi"
"Nima dai ganin shi a school namu nayi, yana tamun magana naki na kulashi, shineh ya durkusa har kasa wai nayi hakuri koh bazan kulasa ba nashiga motar sa yakaini gida, shineh ni kuma na tausaya masa nashiga" Meena ce tayi magana tace
"Kut!!!!!!!!! S.A d'in ya durkusa miki har kasa, ahhh lalle ke muguwar mak'aryaciya ce, kinsan S.A kuwa, kinsan mahaifin sa waye neh a Nigeria?"
"Ban sani ba kuma ban damu na saniba, kuma yanxu yakirani a waya yana rok'o nah akan na so shi idan baniba bazai iya ruyuwa ba, yana cewa nice HAYAAT nasa"
Aliyu dai kallon ta kawai yakeyi dan yasan Fido terrible liar ce, wata zuciyar kuma na gaya masa S.A zai iya aikata haka akan abunda yakeso
Gyaran murya yayi yace
"Don't even dare fall him, sabida an miki miji"
"Yaya Aliyu kasan mutum bai sanin lokacin da zai fad'a cikin so, we don't get to choose who to love, love just happen"
"Sannu Mrs Love kinji maza ki tashi kibani waje kuma karki kuskura ki sake masa fuska"
"Dan S.A yafi karfin ki wlhy kije can ki nema class naki" cewar Meena
Fido tashiwa tayi tana mamakin abunda Meena tace wai S.A yafi karfin ta, ita bataga wani abun fin karfin ta dayayi ba. Duk da yahad'u sosai amma wollah baifi karfinah ba. Juyawa tayi ta watsa wa Meena kallo tace
"Wlhy Allah watarana sai mu bibbiyu zan miki dukan gaske naga meh kwatar ki, sai kin raina kanki yarinya"
Bud'e baki duk sukayi suna kallon ta, Aliyu mamaki yake irin karfin halin Fido, yace
"Ki mata duka kema jikin ki ya fad'a miki, wato kin raina matata koh? Ita ba aunty ki bace ehhhh? Very stupid girl kawai b'ace mini anan bana kaunar ganin wannan fuskan meh kama dana mayu"

Ficewa Fido tayi tana cewa a hankali "wlhy koh kai baka isa ka tab'a lafia ta ba"

Meena tayi hugging Aliyu tace
"Moon of my life Fido ta manta da MATAR SOJA take zance, zan karkarya tane idan tamun iskanci"
Aliyu kallon ta kawai yayi yasan dai Fido zata iya aikata abunda ta fad'a. Girgiza kansa yayi yana wani shu'umin murmushi....

Nigeria

Abuja

Issam neh awani mansion parlour, Mahaifyar sa ce take sauka akan stairs har tazo dab inda yake amma baima san tazo ba hankalin sa yana wani wajen. Tab'a sa tayi tace "lafiya Son". Take yayi firgit, saka hannun sa yayi cikin dogon bak'in gashin sa yayi ajiyan zuciya yace
" I didn't know what to think of or maybe I did and I just refused to think about it. Mum all I know is that I liked this gurl" rik'e Mum nasa yayi gam yace
"Ina tsoro Mummy, nafara jin ajikinah idan ban samei taba rayuwata tana cikin hatsari, inajin wani abu gamei da ita, Mummy karshen tama inajin kamar SHE'S MY HAYAAT, kamar ITACE RAYUWATA!!!!!!!!"

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers(p.m.l)

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{July,2017 }

Na sadaukar da wannan page ma Shamcy, I heart you dear....

```Page 16```

Mummy shafa gashin d'anta tayi tace
"Karka damu Son, idan har Allah yayi matar kace toh tabbas sai ka aure ta, kasani mutum baya auran matar wani, matar mutum kabarinsa kaidai kata addu'a nima kullum ina cikin maka" Murmushi yayi yace
"Mother you won't just understand, inaji ajiki kamar ta tsane ni, I see nothing in her eyes but hatred, she hated me Mother, ta tsane ni"
"Shhh karna k'arajin ka fad'a haka, mesa zata tsane ka, bata tsane kaba Son kaji"
Murmushi yayi yace
"Yanxu naji relief"
"Yanxu yaushe zata dawo Nigeria?"
"In next 10 months In Shaa Allah"
"Wow Allah kaimu"
"Ameen" yace tareda rik'e hannun mahaifiyar sa gam kamar wanda idan yasake zata b'ace.....

UK

Washegari Fido tun da sassafe ta shirya zuwa school, bayan Aliyu yayi dropping nata yace
"Wlhy Allah kar kishiga motan kowa idan kin tashi zuwa"
"Koh da Motar Suleiman"
"Shi d'in kanin Ubanki neh koh na Uwarki" fita tayi kawai a motar ba tareda da ta kara cewa komai ba, tace "Gosh!!!! Ban kaunar maza masu ashar wlhy, basu san aji down baneh"

Bayan ta gama lecture da practical nata taje wajen Eesha, acikin hiran neh Eesha take fad'an Issam dole yabar Abuja yazo KT auran su, anan tasan Issam yanxu yana Abj. Tunani tafara idan Allah yasa ta koma gida wani irin k'arya zatayi da za'abarta taje Abuja. Eesha ce ta tab'o ta tace
"Lafia kuwa Fido?"
Firgit Fido tayi ta kwakulo murmushi tace
"Lafia"

Wayar tane yafara ringing d'aukawan da zatayi taga Gen. Suleiman, bata d'auka ba a first call sanda ya k'ara kira na biyu, Eesha tace
"Ki d'aga mana ba kiranki ake yi ba?"
"Mtswww kedai bari wlhy wani abokin Yaya Aliyu neh shima an turo shi wani assignment but shi tun last year yana nan, next month ma zai koma gida"
"Wow kice kin samu Soja"
"Kinsan duk rashin kunya nah ina shakkan su ai, tun lokacin da wani tsinannen Soja yamini rashin mutunci a Maiduguri, tun lokacin nake shakkan su"
Dariya Eesha tayi tace
"Ba ke kince you are very stubborn ba, ai kin had'u da daidan ki"
"Kinsan wani abun takaici, Sojan fa recruit neh, kurkutun banza, a yau idan na had'u dashi sai na saka Yaya Aliyu da S.A sun masa rashin mutunci, zance su zaneh sa a gaba nah kuma su sakashi frog jump" dariya Eesha tayi tace
"Ahh lalle bakida dama, please kiyi receiving call d'in mana"
"Ohk bara na saka a loudspeaker kiji"
Picking call d'in tayi ta danna loudspeaker
"Haba Queen of beauty inata kiran ki bakya d'auka wa"
"So sorry wlhy wayar ce a silent ina lab"
"Ohh ayyah, yanxu kina ina?"
"Na fita shan coffee"
"Wani coffeehouse?"
"Rio"
"Ohk yanxu zaki ganni In Shaa Allah" ya katse wayan
Eesha tace "wow kice kinyi sabo, toh ina zakikai Issam namu"
Murmushi Fido tayi tace
"The truth is that I feel nothing for Issam, believe it or not Eesha. Idan ma ina feeling wani abu akanshi bai wuce hatred ba"
"Sub'hanallah!!!! Tsana kuma Fido, meya miki da kika tsaneh shi"
"Forget it"
"Hmm Allah shi kyauta, but kinsan tsana yana iya komawa SO"
"Never!!!! Allah sawwaka"

Sallama S.A ya musu tareda neman waje ya zauna
"Good afternoon" cewar Eesha. S.A yayi murmushi yace
"Afternoon durlin" dariya duk sukayi Fido tace
"Kar Faruq yakama ka kana kiran ta durlin"
S.A yace "Wait are you jealous"
Dariya Eesha tayi tace
"Inaga she's jealous, Mrs J!!! Bari natafi ana jirana bye" tareda d'aukan jakarta ta. S.A yace
"Toh baki fad'a mun sunan ki ba?"
"Eesha" tareda musu bye bye tabar wajen..
Chapter 8 · 0% Book details