← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 40

Sashe 7

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Aliyu zaune a parlor yana kallon Tv yaji kamshi ya buge hancin sa, a hankali ya d'aga idonsa yaga Fido tana gyara agogon hannun ta.
"Kee ina zakije yau ba Saturday baneh"
"Wlhy wajen Eesha kuma inada lecture kamar karfe uku". Kallon ta yayi sama da kasa shi kansa yasan ba karamin kyau tayi ba, ji yayi zuciyan sa yana bugawa kamar zai fita, a hankali yace
"Kije ki cire kayan nan kuma karki fesa perfumes haka"
"Haba Yaya wlh nayi......" Bata k'arasa ba ya daka mata tsawa yace
"zaki canza koh sai na tattakaki"

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers(p.m.l)

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{July,2017 }

```Page 14```

Turo bakin ta tayi tace
"Zan canza but i don't see any thing wrong with what I'm wearing" Mugun kallo ya watsa ma take ta juya ta koma d'akin ta. Zama tayi akan gado tana meh mugun jin haushin Aliyu, can koma sai ta tashi taje gaban mirror tana kallo kanta. Tsoki taja tace " Wlhy Allah bazan canza kayan nan ba"
Jakarta ta d'auko ta lek'a parlour taga wayam ya tashi a wajen, da hankali tafita a gidan ba tareda wani ya sani ba. Tana fita taxi ta tsaida bai gama tsayawaba ta bud'e tashiga ciki tana sauke numfashi tana dariya kamar wata zararriya.

Kofan gidan su Eesha aka sauke ta tashiga ciki. Da sallama tashiga parlour ta tarar da Antyn Halima wacce take yayar Eesha, Faruq kuma Cousin na Eesha neh so dukkan su a gida d'aya suke da zama. Murmushi Anty Halima tayi tace
"Su Fido manya yakike" zama tayi tareda cewa
"Washhh!!! Wlh agaje nake. Lafia kalau Anty Halima" bayan sun gama gaisawa Fido tace
"Inaa yar air nan tashiga neh"
"Suna can garden" take ta tashi tace
"Anty Halima ga jakata idan na tashi tafiya zan shigo na d'auka"
"Ohk toh" fita tayi a parlour ta wuce bayan gidan wajen garden. Da sallama ta iso wajen su duk suka amsa mata da fara'ar su. Tace
"Kudai kullum kuna tare dan Allah kuyi aure kowa ya huta" dariya Faruq yayi yace
"Karki damu Matar abokinah zamuyi Soon amma maybe ku rigamu" Fido kallon sa take dan bata ganeh meh yake nufi ba tace
"I dnt just get you, what do you mean by matar abokin ka?"
Eesha ta kashe mata Ido tace
"Issam mana. You know people flocked around him, it wasn't just his perfect looks; it was his charisma and genuineness that made you wanted to be around him" Fido kallon ta take da mamaki, she can't believe abunda kawar ta Eesha take fad'a wai tana son Issam. Eesha taciga
"And you know what my friend? Inaji ajikinah Issam na kaunar ki fiyeda yadda kike tunani"
Kan ta bud'e baki tayi magana sai Faruq yace
"Gashi nan ma yana zuwa" d'aga kai Fido tayi tana kallon sa, tafiya yake kamar zaki, idan ba fad'a makaba sai ka rantse ba d'an Nigeria baneh. A farko data gansa taji tana masifan sonsa, amma yanxu kam tsantsan tsana take masa,she can't even explain how much she hate him. Take ta tashi a kujerar ta tace
"Inada lecture sai mun had'u next time" tareda barin wajen. Eesha tabi bayanta tace
"Yake haba karki bani kunya mana" had'a rai Fido tayi tace
"Dan Allah kibarni bana son magana" sunzo dai dai da Issam Eesha ta gaishe shi, da kyar ya iya bud'e baki ya amsa. Fido tace
"baga irinta ba, kina gaishe shi yana wani jin kanshi Wlhy kin bani haushi" Eesha tace
"Haka nature shi yake miskili neh na gaske" tsoki taja tace
"Nature buru uba, naga Yaya Aliyu uban miskilanci". Dariya Eesha tayi tace
"Toh Issam ya ninka sa a miskilanci"
"I don't have time for this" tayi shigewar ta wajen Anty Halima ta d'au jakarta tayi mata sallama ta tafi
Har a ranshi Issam baiji dad'in barin wajen da tayiba data gansa, baya kaunar yarinyan koh kad'an amma each time da sukayi fad'a yana samun nishad'i koh ba komai ya b'ata mata rai......

Fido bata dawo gida ba sai da yamma likis kusan karfe shida, Aliyu tagani a waje tareda wani saurayi wanda shekarun sa bazasu haura talatin ba. Taji dad'i data gansa da abokin sa koh ba komai bazai mata fad'a agaban sa ba.
Gaishe su tayi zata wuce ba tareda jiran amsan su ba dan bata bukata, Aliyu yace
"Yau Saturday ma sai yanxu"
"Eh" kawai tace a takaice, wanda suke taren neh yace
"Wow wannan itace sister ka d'in"
"Eh" Aliyu kawai yace dashi, abokinsa zai kara magana Aliyu yace
"Maza kishiga ciki" tawani b'ata rai tashiga abun ta... Ji tayi abokin sa yana cewa "gaskia zaka bani wannan kanwar ka d'in ta mun" Aliyu yabasa amsa yace
"Ba yanxu zatayi aure ba" Fido tace gwara daka fad'a masa haka a zuciyar ta bata k'arajin zancen su bakuma.

Fido shiga tayi d'akin ta tayi wankan sallah, tana cikin shafa mai ajikin ta taji Aliyu yana kwala mata kira, da sauri ta saka kaya zuciyan name bugawa tana cewa "wayyo Allah yau na banu"
"Kifito koh idan nashiga cikin d'akin nan zan karkaryaki" jikin ta yana shaking ta bud'e kofan, janta yayi kamar tsumma zuwa parlour yace
"Dan Ubanki banace ki canza kaya kan ki fita ba" Tura bakin ta tayi tace
"Haba Yaya kana treating d'ina kamar wata 'yar 18 years na girme matar ka fa". Cire belt na jikin sa yafara yana cewa
" maimaita abunda kikace" tana ganin zai cire belt nasa ta haura a goje yabita amma inaa yakasa kamota tashiga d'akin ta tasa lock. Yayi bugun duniya amma inaa taki ta bud'e. Duk da yunwan dake addabar ta Corn Flakes kawai tasha tabi lafiar gado..Tace "wai Allah ya d'au beli nah"

_Bayan Wata D'aya......_

Tun ranar da Fido ta had'uda Issam gidan su Eesha bata k'ara kallon sa ba. Tanason tambayar Eesha amma kar Eesha ta d'auka dagasken sonsa take, tsoki taja tace "basai ta d'auka inason sa ba d'in" D'aukar wayan ta tayi ta latsa number Eesha, bayan Eesha ta d'auka sun gaisa tarasa ta yadda zata tambaye ta, sai can tace
"Kina gida neh?"
"A'a ina cikin school yanxu muka fita cin abinci"
"Ohk nima ina School lemme come and meet you guys but hope baku tareda da yaron nan"
"Wani yaro kuma?"
"Ummm mei ma sunan sa, kinsan ba kowa nake rik'e sunan saba, abokin Yaya Faruq dai"
Eesha taganeh tsaf amma sai ta muge tace
"Wa kenan? Kinsan abokan sa suna nan dayawa"
"Ummm koh Issam neh koh meh yakeda suna"
"Are you freaking serious Fido, kefa kika kirani time da kike Nigeria akan kina neman details na yaron akan akwai wani unfinished business tsakanin ki da yaron yanxu kuma kice bakisan sunan sa ba?" Ajiyan zuciya Fido tayi tace
"Yanxu yana ina? It been long ban gansa ba"
"Ya koma gida" atake Fido tace
"Wani gida?" Dogon tsoki Eesha taja tace
"Yanada gida da yawuce Nigeria neh?"
"NIGERIA?" ta fad'a da karfi
"Eh Fido, wani abu neh?" Take tace
"No ba komai thank you bye" ta katse wayan. Salati tafara a hankali, yanxu ya zatayi, danshi tazo UK gashi baza barta ta koma Nigeria ba sai bayan ta gama d'an iskan Masters d'in nan...

Toh fa masu karatu, shin zatabar Issam???? Wa zata aura??????? Aliyu, Issam koh abokin Aliyu...

Nima dai dunno

*HAYATEEY*

Pure Moment Of Writers(p.m.l)

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{July,2017 }

GAISUWA NA MUSAMMAN MUNAYSHA, words can't explain how much I missed yhu..

```Page 15```
Chapter 7 · 0% Book details