← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 40

Sashe 10

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eesha da Fido zaune cikin motar Eesha wata mota Benz bak'a tashigo cikin haraban gidan, Eesha tace
"Anya wannan ba Mahaifiyar S.A baneh"
"Ke ja motar dan Allah banso mu had'u inajin kunya"
Wani dogon tsaki Eesha taja tace
"Kunyan banza kuji yarinya wai kinajin Kunya"
Wayan Fido neh yafara ringing ganin New number ta d'auka tace "Assalamu Alaykum"
Can muryan wata mata ce tace
"Ina cikin gida ku kifito"
"Ohk" Fido tace a hankali tareda katse wayan.
Juyawa tayi ta kalla Eesha tace
"Eesha wannan wace irin matace, mesa S.A yabata number nah?"
"Awww kina nufin ita ta kiraki?"
"Mtswww wai tana waje nafito, dan Allah rakani"
"Ohk muje"

Tare suka fita acikin motan, Fido atampa Holland neh ajikin ta d'inkin dogon riga sai gyale data yafa R$S da dogon high heel dake kafan ta, Eesha kuma Abaya Purple neh tayi rolling kanta da veil nashi. Zuwa wajen motar sukayi suka tsaya dan basu kallon wanda ke cikin motar dan glass d'in Super tint ce, haka suke tsaya kusan minti goma kan wani yafito a motar da sauri har sanda suka firgita ya bud'e ownest corner.
Mahaifiyar S.A ce tafito tasha kwalliya jikin ta yasha gold, wani kallon sama da kasa take musu kan tace
"Wacece Fido a cikin ku?"

Ina meh baku hakuri kwana biyu kun jini shuru wlhy banajin dad'i shiyasa

By

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers(p.m.l)

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{July,2017 }

```Page 17```

S.A yace "Haba Aliyu meh haka? Kai da yakamata ka tsaya kaji meh yafaru before taking any action amma kawai sai ka fara zaneta, gaskia banji d'adin wannan abun ba, idan badan kai yayanta baneh Allah da sai mun b'ata"
Aliyu hararan sa yayi yaja dogon tsaki yace
"Kaga please let me rest bana son wani headache"
"Ohk tunda haka kace, but please karka kuma dukan mun mata"
Aliyu a ransa yaji maganar amma ya dake yayi shigewar sa d'akin, S.A girgiza kai yayi shima yafita a gidan.....

Fido zaune take akan gado tana shafa Robb ajikin ta dan ba karamin jin jiki tayi ba, wani farin ciki takeji koh ba komai tayima Meena duka, gani take daga yau sun raba raini.
Wayar ta neh ya dawo da ita daga dogon tunanin data fad'a, S.A tagani baro baro kan screen. "Yaa Salaaam" ta furta a hankali, zatayi receiving call d'in sai kuma ta fasa
"Mtswww yaga Aliyu yana duka nah ai da kunya, kai wlhy Yaya Aliyu yakawo mini cikas, ai wannan aji down neh" haka tabari wayan yata ringing bata d'aga ba...

Can bayan ta kwanta taji message yashigo mata waya, ita duk a tunanin ta zataga number S.A, sai dai kuma code na Nigeria da tagani, bud'e wa tayi taga message: _Mesa kike zuwa cikin mafarki nah and my thoughts every blessing day, WHY???????_

Tsaki taja ta kunna data na wayar ta tana ganin trailer wani sabon film Haseena, sai can tak'ara jin message yashigo wayar ta. Bud'ewa tayi taga same number: _Kina saka ni cikin damuwa and dilemma, why HAYAATEE?_
Wani dogon tsaki taja tace koma waye saidai ka cinye kanka tayi blocking number.........

Tun daga lokacin Meena tana mugun shakkan Fido sabida tasan ba meh kwatar ta amma ta rantse da Allah duk ranar da suka koma gida Nigeria she must regret tab'a mata skin da tayi, ta ayyana a ranta har Aliyu bazata barshi ba tunda ya nuna mata a fili ba ita yakeso ba abunda yake cikin ta yakeso.

Fido karatu take ba kama hannun yaro, takan bincike akan Issam wanda taji labari gidan su yanxu yana abuja. S.A kam ya koma Nigeria amma kullum suna cikin waya da Fido, yake ce mata tana dawowa za'ayi maganar auren su.. Itadai saidai tayi murmushi dan har ga Allah S.A yakai namijin dazata So shi!!!!!!!

_Bayan Shekara d'aya_

Nigeria

Umaru Musu 'Yar aduwa Airport

General Aliyu neh rik'e da kyakkyawan baby girl a hannun sa, gefen sa na dama Fido ce tasha bak'in sunshade, da doguwar riga ready made purple da flowers yellow tayi rolling da black veil da takalmi da jakanta shima black, ba karamin kyau tayi ba, sai nace weather UK ya karb'eta sosai, by his left kuma Meena ce tayi jiki sosai, sai wani shan k'amshi take tana hura hanci a dole ita meh miji da baby itama ba laifi ta k'ara haske duk da ma tun da fara ce, sai idon ta k'anana da yak'ara shiga ciki dan jikin da tayi..

Shamcy da gudu tazo ta rungume Fido tace
"Wow sis kinyi kyau, gaskia UK ta karb'e ki sai kace ba karatu kikaje ba"
Fido taja hancin ta tace
"You can at least say Welcome first!?"
"Sorry Sis! Welcome "
"Thanks"
Shamcy ta gaishe da Meena wanda dakyar da amsa, ta gaishe da Yaya Aliyu ta karb'a babyn hannun sa tace
"Wow Mashaa Allah Yaya kuna kama da Basma amma hasken Anty Meena tabiyo"
"Ke ke ke ban daughter nah bana son jagwalgolo" cewar Meena. Shamcy jiki a sanyaye ta mik'a mata Basmah ta wuce wajen Fido da Yaya Khaleal.
Fido tayi dariya tace
"Maganin ki nan gaba ki k'ara kinji, da maitan ki na son yara d'in". Shamcy dai shuru tayi batace k'ala ba sai wani tura bakin da take.

Fido da Shamcy shiga motan Yaya Khaleal sukayi, su Aliyu kuma suka shiga motan Teema.

Fido tana shiga parlour taga Inna da remote a hannu tana kallon B4U Movies, da gudu taje ta rungume ta tace
"Inna keda India sai kace kina jin yaren"
"Ja'iran yarinya ai kin tsorata ni ya kasar waje ya karatu?"
"Alhamdulillah Inna"
"Kai Mashaa Allah kin ganki kuwa, kin k'ara kyau lalle Aliyu yana kula dake sosai, tunda Allah yasa kin dawo sai maganar auren ku"
"Aure nah da waye kuma?"
"Kuji 'yar iskar yarinya, tambayata ma kike?"
"Kinga Inna I don't have time for this, let me freshen up"
Barin ta tayi tashiga d'aki tayi wanka, bayan ta fito tayi sallah. Shamcy ta zauna kusa da ita tace
"Adda Fido ina tsarabar mu?"
"Mtswww ke kyale ni ba yau ba, ina SIM card da nace kimun register?"

Tashiwa Shamcy tayi ta d'auko mata, bayan ta saka a wayar ta takira number Eesha, Eesha tana d'agawa tace
" 'Yar duniya ai na d'auka zakiyi missing aure nah"
"Hmm na isa nayi missing auren ki, yanxu saura sati nawa?"
"Three weeks"
"Da sauran lokaci ma ashe, umm Issam zaiyi attending kuwa?"
Dariya Eesha tayi tace
"Ai dolen sa yana best friend na Faruq"
Fido wani sanyi taji a ranta, tunani take wani irin mataki zata d'auka a kansa. Eesha tace
"Ya naji kinyi shuru? Wani abu neh?
"A'a wlhy ba komai"
"Zanzo gobe ki ajiye mini tsaraba ta"
"Mtsww bakida damuwa sai kinzo bye"

Fido shuru tayi tana tunani, hankalin ta gaba d'aya yana kan Issam, tunani take wani irin mataki yakamata ta d'auka akan sa. Wani yace ta shafe shi a doron kasa, take ta girgiza kanta tace "NOOOO" wani zuciyan yace ki masa abunda bazai tab'a mantawa dake ba har karshen rayuwar sa. Ya Allah toh meh kenan zan masa?!!!!

Ringing na wayan tane yasa tayi firgit ta dawo a dogon tunanin data fad'a, receiving na call d'in tayi tana murmushi tace
"My Man Shamcy ce ta tura maka number na koh?". Tayi dariya sai can tace "ohk toh ba matsala idan kayiwa Hajiya magana duk yadda kukayi sai ka fad'a mini". "Ohk bye" tareda katse wayan.

Abuja

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers(p.m.l)

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{July,2017 }

```Page 19```

Duk suka durkusa har kasa suka gaishe ta, d'auke kanta tayi tace
"Ba gaisuwan ku nake buk'ata ba, koh kunji nace ku gaishe ni? I just asked you people a simple question kunje kuna abu daban, na tabbata da exams neh da kunyi failing. For the last time nace wacece Fiddausi a cikin ku?"
Da hankali Fido ta furta
"Nice Mummy"
Dogon tsaki Hajiya Lubabatu taja tace
"Toh kaini wajen Ubanki"
A sanyaye Fido ta tashi tace
"Muje"
B'angaren Abba takai ta, a bakin kofa tace
"Bara na mishi magana idan yabada permission sai ki shigo"
Kallon Uku saura tara ta mata ta bud'e kofan da karfi da shiga, Allah yasa yana parlour yana rubuce rubucen sa Mami da Inna na gefen sa. Gani kawai sukayi an bangaje kofa an shiga ba koh sallama, da mamaki suke kallon ta Abba yace
"Ya ke lafia kike kuwa?"
"Aw so kake kace ni mahaukaciya ce koh?"
"Toh idan ke ba mahaukaciya bace toh tabbas bakida cikekken hankali"
"Mei kake nufi kenan?"

Fido da gudu taje wajen Abba tace
"Abba Mahaifiyar S.A ce fa"
A tsawace Abba yace
"And so bloody what? Who gave her the audacity ta shigo mini parlour na haka?"

Dariya tayi Hajiya Lubabatu tace
"You called this a parlour, mei ma kake da suna? Professor Sanusi Umaru Sodangi kake koh? Ai wannan da kake kira da parlour koh driver nah parlour sa yafi wannan. Nawa kake karb'a a wata salary ka. Dubu d'ari hud'u, dubu d'ari biyar koh dubu d'ari shida?"
Abba shuru yayi ya rasa meh zai ce mata dan yafi karfi ace yana sa'insa da mace, a tsawace Hajiya Lubabatu tace
"Answer me mana"
Fido ranta idan yayi dubu ya b'aci, tazo gaban Hajiya Lubabatu tace
"Hajiya Lubabatu ke d'in da kanki salary ki nawa yake? Ai bai wuce irin na mahaifina ba, saidai shi d'in halak malak nasa yake ci, ke kuma hakkin talakoki kuke sata kuke ci"
"Ni kike fad'a wa haka?"
"Ke d'in, highest abunda zakice shine bazan aura d'anki ba koh? Toh ai nima haukan da kika zo kikayi shi kad'ai ya isa yasa bazan aure shi"

"Better da kika furta da kanki baza ki aure shiba, dan Wlhy d'ana yafi karfin gidan nan" ta fice a parlor.
Inna tayi salati tace
"Yau naga tsinanniyar uwa. Kai Allah shirye mu, Ameen"

Abba yace "Fiddausi zo nan"
Gaban sa taje ta durkusa, yace
Chapter 10 · 0% Book details